DUBAI PART 1

“Mom kada ki soma yin wannan gangancin babu inda Habeey zataje in kuwa kin matsa to nima zan barmiki gdan sai ku zauna a ciki ni na kama hotel nida matat….” Sake buge bakinsa tayi tace “idan ka qara cewa wannan munafukar yarinyar matarka wlh sainayi maka baki ka lalace Koda yake dama ai ka lalace din tunda har ka fasa gardin mace ajiyeta ma kake a gdanka, to bari kaji ma Taheer yau qafata qafarka in kaga nabar qasar nan to tare muka tafi dakai tunda abin naka iskanci ne aure ma zanyi maka dan ubanka”
Fincikewa Habeey tayi daga jikinsa ta dauki hanyar fita da gudu shima yabita yana kiranta itama Hajiya binsa tayi ta riqo rigarsa yasan halin Habeey sarai zuciyace da ita kamar masifa bata daukar wulaqanci in ba nasa ba shiyasa hankalinsa ya tashi.
Baisan sanda ya durqushe ya cafki qafarta ba yace “Don girman Allah ki tsaya Habeey kada ki tafi a wannan daren bakisan inda zaki ba…” Cikin kuka ta warce qafarta tace “Indai kanasona kuma kanaso nima nasoka to kayiwa mahaifanka biyayya don Allah Taheer dama nice kai….”
Tana fadin haka kukan da ta hadiye ya qwace mata tace “kai dan gatane mahaifiyarka tanada iko akanka ba kamar tawa ba” Kama hannunsa tayi tace “don Allah kada ka bata kunya kaji ta isa dakai ne shiyasa take qoqarin saitaka a hanya, Taheer kada ka damu dani ka damu da kanka kawai ni tawa qaddarar kenan”
Miqewa tayi ta fice da gudu daga gdan shima ya fincike daga ruqon da Mom tayi masa yabita amma harta tsare mota ta hau.
Bin gurin yayi da kallo tare da zamewa ya zauna a qasa ya buga hannunsa akansa ya kalli Mom da ta qaraso yace “shikenan ranki yayi fari kin koreta Mom batada kowa fah a garin nan buri nake na aureta Mom kema fah kin haifa kuma wlh Habeey batada matsala har tafi yayanki tarbiyya kawai qaddararmu ce hakan…”
Tsaki Mom tayi tace “ai nima tafini tarbiyya shiyasa ta baro iyayenta ta taho take karuwanci a qasar daba tataba shashasha soko bandama tsabar iskanci ubanme zakaci a jikin wannan yarinyar mazan titi sun gama debe albarkar jikinta, zaka tashi mu shiga ciki kosai naci qaniyarka”
Miqewa yayi suka koma ciki ya zube a kujera Mom nata sababinta shikam baimasan tanayi ba wayar Habeey kawai yake Kira amma taqi dagawa takaici yasashi jifa da wayar yace “yanzu ya kikeso nayi kin bata Mata rai nima kinjamin ko wayats taqi dagawa don Allah kibarni naje naganta”
Ko kallon tsiya bai samu ba balle na arziqi saima miqewa da tayi ta zare key din parlourn ta shige wani dakin a cikin dakunan tayi wanka ta dawo ta tayar da sallah, Bushirah ce ta dubesa tace “amma Ya Taheer meye yasa bazaka auri Habeeba ba kalamanta sun kashemin jiki sai naji inason sanin wacece ita, don Allah ka bani lbrnta koda wani taimako da zan iyayi Mata wannan rayuwar bata dace da kyakkyawar mace kamarta ba”
Iska ya furzar ya miqe yace “ni kaina bansan komai game da Habeey ba kawai dai nasan nine na fara lalata Mata rayuwa amma bazan iya cewa dake ga abinda ya kawota Dubai ba nasan dai sometimes zanji tana kuka tana cewa Pappa ka cucemu Allah ya saka mana, Amma bansan waye Pappa ba bansan me yayi Mata ba”
____________Tana fita cikin saa ta samu taxi ta hau har sukace unguwar tasu kuka takeyi ga wani mahaukacin sanyi da takeji, hakanan dai cikin dauriya ta fito ta shiga cikin gdan Aysher na ganinta ta miqe da sauri tace.
“Habeey kece a daren nan?” Kada Mata kai kawai tayi ta bude dakinta ta fada saman katifarta taja bargo ta qudundune jikinta tana kukanta me taba zuciya.
Juyawa Aysher tayi ta fice saboda inda sabo ta saba da kukan Habeey me taba zuciya gashi bajin rarrashi takeyi ba balle tace zata rarrasheta.
Haka tayita makyarkyata har tasamu bacci ya dauketa, sai asuba ta farka ta samu jikinta ya dan ware ta shiga tayi wanka tayi sallah ta koma ta kwanta har yanzu qirjinta ciwo yakeyi.
Tananan kwance ta kasa ko tashi taji an bude qofar dakinta an shigo ta bude idonta a hankali ta saukeshi akansa gabanta na faduwa shikam Taheer wanne irin mutum ne da asubar nan har ya samu ta fito?
Zama yayi kilusa da ita ya kamo hannunta yace “kinsha maganinki kuwa?” Daga masa kai tayi ya fitar da huci yace “bazan barki anan ba inada wani gdan Dad dina dake hannuna ki tashi muje na kaiki can kafin Mom ta tafi”
Kada masa kai tayi ta sake Jan bargo ta rufa ya yaye yace “banaso halinki na gardama Habeey inayi ne don mutuncinki zama a irin gurin nan bai dace da nutsattsiyar mace ba komai zai iya faruwa”
Daga masa hannu tayi tace “nikam nace banaso ko dolene” kada Mata kai yayi yace “eh dolene kibi umarnin mijinki kuwa Habeey Koda bakyaso, ki tashi muje yau zan wucce 9ja idan komai ya lafa zan dawo gareki Ina fatan faruwar abubuwa da yawa kafin lkcn”
Juyawa tayi tace “Allah ya tsare hanya” daga haka bata qara cewa dashi komai ba har ya gaji dayi mata mgn ya dagota yace “kinyimin alqawarin duk tsanani duk wahala bazaki juyamin baya ba, meye yasa tun kan aje ko Ina kikeson ki fara butulcemin Habeey Mom mahaifiyata ce amma batada ikon canza abinda ya riga ya ginu a zuciyata inasonki a duk yanda kike kuma zan tsaya tsayin daka wajen kare qimarki a ko inane a duniya”
Itadai batace masa komai ba saida taji yana shafa bayanta a hankali tasan sarai inda zancen zaije wannan dalilin yasata miqewa ta fada bathroom ta kulle.
Bugun duniya taqi budewa magiyar duniya taqi ta bude har saida yaji Mom ta fara kiransa ya daga yace “inazuwa Mom” kashe wayar yayi ya dauki biro da takarda yayi wani dan short note ya ajiye Mata tare da check na kudi masu yawa ya fice.
Saida ya nemi magajiyar gdan yayi Mata ihsani tare da roqonta ta kula masa da Habeey kada take barinta zuwa ko Ina har zuwa lkcn da zai dawo, sannan ya tafi zuciyarsa babu dadi yana tuqi yana hawaye tare da jin haushin Mom dinsa yasan itace duk taja masa wannan matsalar da yake ciki.
UMMUH HAIRAN CE…✍️
[7/23, 9:22 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI✈️
PAID BOOK
HAƘƘIN MALLAKAR
????????
FAUZIYYA TASI’U UMAR
(UMMUH HAIRAN)
21/7/2020
Kamar yanda duk Wanda yaga status dina na yau ya sani cewa, littafin DUBAI ya koma na kudi da sabon farashi VIP 1k 30 people’s kawai nakeso single 300
Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin
Account number
????????
0255526235
Fauziyya Tasi’u Umar
GTB
Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp
????????
09013718241
Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number
????????
09013718241
LAST FREE PAGE
Episode 12
Yana Isa gdan Mom ta rufeshi da fada tana sababin ya saci jiki daka zuwa masallaci ya tafi gurin karuwa, zubewa yayi a gabanta ya kasa boye abinda yakeji a zuciyarsa, tsoro ya kama Mom ganin yanda dan nata yake kuka kashirban yana girgiza kai yace.
“Mom wlh idan kikaja na rasa Habeey kema Zaki rasani don na tabbatar mutuwa kawai zanyi Mom yarinyar nan tafi kowa buqatata a rayuwarta batada kowa a garin nan saini idan kika matsa na tafi nabarta bansan halinda rayuwata da tata zata kasance ba…”
Wata tsawa data daka masa tasashi hadiye guntuwar mgnrsa tace “ashe kuwa zaka mutu don wlh nama rantse maka idan kaga ka auri yarinyar nan to ka qaddara babu numfashin Hajiya Saratu ne kai ko bana raye ka auri yarinyar nan bazan taba yafe mak…”