DUBAI PART 1

Miqewa yayi yace “wannan kuma ke ta shafa nidai nasan dana dake cikinki kuma dole ki haifemin abuna saboda inasonsa” ficewa yayi yaja qofar da qarfi ya datse ta zube a qasa ta rushe da kuka tana fadin “innanillahi wa innah ilaihirraji’un”
Kuka takeyi sosai tana dukan cikinta duka bana wasa ba aikuwa kafin wani lkc ta galabaita jini ya balle mata, bude qofar yayi ya shigo ya hangeta a kwance riqe da cikinta da sauri ya nufota kawai yaji ya cambala qafarsa cikin wani abu me dumi yakai dubansa qasan farin tiles din yaga jinine yaketa malala.
Zubewa yayi a gurin yana fadin “garin yaya jini kuma meye ya kawoshi?” Yana mgnr yana jijjigata amma batako motsaba ya dauki wayarsa da sauri ya kira health care din hotel din sukazo suka kinkimeta suka fice da ita.
Agajin gaggawa suka bata suka dubata sosai duk inda sukayi yana biye dasu ya kashe kudi sosai kafin cikin ya tsaya, aka kafa musu manyan dokoki ciki harda qauracewa juna shikam wannan labari baiyi masa dadi ba amma babu yanda zaiyi haka ya karba ya rungumi qaddara suka koma gda aikuwa tasha ruwan masifa da bala’i harda rantsewa idan ta zubar masa da ciki sai sunyi shari’a.
Zama sukeyi na gabar gaske ko gaisawa basayi saidai idan jarabarsa ta ciyoshi yazo ya qwaquleta ya koma dakinsa jaraba kam tana shanta.
Shine ya dauki nauyin turawa Pappa kudi duk watan duniya.
A cikin wata hudunnan abubuwa sun faru marasa dadi itadai Habeey kullum cikin damuwa take duk ta rame ta fita hayyacinta abu sai girma yakeyi gashi babu wata mu’amalar arziqi tunda ta nuna batason cikin shima yake tata mata rashin mutunci.
Da tayi masa mgn sai yace shifa siyanta yayi gurin ubanta kudi yake biyan babanta saboda haka dole tayi masa biyayya.
Ranar da suka gama abinda ya kawosu suka fara shirin tafiya, kwana biyu suka qara suka daga zuwa Dubai tafiya ce irinta kurame babu me cewa da wani qala.
Nanma gidansa yakaita ya ajiyeta kashedi na tashin hankali yayiwa masu gadin gdan akan bayason Koda ya tafi abar wani ya shigo gdan, kudi ya ajiye mata sosai ana i gobe zai tafi da dare ta samesa a parlour yana kallo ta nemi guri ta zauna “bai ko dago ya kalleta ba har tagaji da zamanta ta miqe zatabar gurin ya riqo hannunta.
Fadowa tayi jikinsa ya riqeta tare da dafa cikinta yace “da magana a bakinki maman twins me kikeso?” Kukan da take hadiyewa ne ya kubce mata yayi saurin dora bakinsa akan nata ya rufe mashi ruf yana tsotsarta yana shafa cikinta.
Janyewa tayi a hankali tace “yanzu kuma idan ka tafi yaushe zaka dawo?” Murmushi yayi yace “zanje nayiwa Mom albishir ne takusa daukan jika…”
Da sauri ta zuba masa manyan idanunta tace “na shiga ukuna don Allah kada ka fada musu Taheer me zance da Addata idan taji wannan baqin lbrn bayan karuwancin da nakeyi ma har cikin shege nay….”
Wani gigitaccen mari ya dauketa dashi ya miqe yana huci ya sake dauketa da mari ta zube kanta ya daki glass ya fashe kuwa jini yayi tsartuwa.
A masifar zafafe yace “ke wacce irin jahilar qwaqwalwa ce dake sau nawa zance miki ki daina sheganta min babena Amma kinqi ganewa”………..
UMMUH HAIRAN CE…✍????
[7/23, 9:23 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI✈️
22/7/2020
Page 15 shine last Free Page, ga wadanda suke buqatar jin qarshen wannan labari zasu biya kudinsu ta wadannan hanyoyin dake qasa single section da nake posting sau daya a rana 200 VIP da nake posting sau uku a rana 600
Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin
Account number
????????
0255526235
Fauziyya Tasi’u Umar
GTB
Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp
????????
09013718241
Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number
????????
09013718241
Episode 16
Cikin mugun tashin hankali ya dagota yana jijjigata yana Kiran sunanta ta bude idonta a galabaice ta shafa fuskarsa tace “ad… Adda..na ta mut… Shi…shikenan ba…ni da sauran me fadamin gsk…” Amaine ya turnuqo Mata ta fara tureshi tanajin yanda qirjinta yake wani mugun zafi a fara sheqa amai.
Tsoro ya cika zuciyar Taheer ganin zallan jini takeyi amansa guda guda, ya qanqameta a qirjinsa yana danna Mata qirjinta yana cewa “zaki mutu ki barni kike nufi Habeey aa bazai yuwu ba bazaki mutu ba don Allah kada kice zaki mutu nima mutuwa zanyi, ki bari muyi aure sai mu mutu tare…”
Jikinta yana wani mugun tsuma hakanne yasashi surarta ya fice da ita a guje yasata a mota ya nufi asibitin data taba kwanciya da ita cikin fitar hayyaci sai aman jini takeyi.
Ikon ilahi ne kawai yakaisu asibitin ya sunkuceta suka shiga ciki ya kwantar da ita a saman wani gado yaje ya finciko wani likita ya kawoshi gaban gadon kawai ya zube a gurin.
Suma sosai abin ya firgitasu suka turata suka nufi heart attacks ward da ita suka fara qoqarin ceto rayuwarta, sun raba ranar kafin su samu numfashinta ya daidaita likitar ta fito ta tarar dashi a zaune ya hade kai da gwiwa yanata sharar gumi yana duba agogo tun 3:00 na dare gashi har 1:00pm sannan suka fito.
Tararsu yayi yana tambayarsu “ya take? Ya baben Amma dai babu abinda ya samesu ko?” Share gumi likitar tayi ta miqa masa takardun hannunta tace “akwai abinda yake damun matarka da take boyewa Wanda ya haifar mata da kumburin zuciya, yakamata ka bincika kasan matsalarta ku kawo qarshenta idan ba hakaba rayuwarta tana barazanar yankewa”
Sakin baki yayi yana kallon likitan a sanyaye zuciyarsa ta tafi tunanin matsalar dake danqare a zuciyar sahibar tasa shikam wannan karon duk me yuwuwa zaiyi yaga yaji matsalarta domin ya kawo qarshen koma menene course rashinta rashin tashi rayuwarsa ne”
Duk wani abu da aka rubuta masa Saida yaje ya nemosa ya kawo, sannan ya tafi gida ya zube a parlourn yana tunanin ta inda zai fara tunkarar iyayensa da mgnr haihuwar da zaayi masa.
Bayason dauko dalar sai yaje gabansu zaifijin dadin nada gammon dauka, shima yini yayi bashida lfyr saboda zuciyarsa batada lfy ko abinci ya kasaci sai ruwan tea kawai da yakesha.
Daqyar yayi wanka ya koma asibitin yayi saa ya tarar da ita ta farka ya ajiye kayan hannunsa ya matsa gabanta da sauri ya rungumeta yace “sannu wifey don Allah kada ki mutu ki barni zuciyata nima gaf take da bugawa”
Lumshe idonta tayi wasu hawaye masu dumi suka zubo mata tace cikin kasalalliyar wahalalliyar murya “shikenan Taheer Addana ta mutu shikenan ta tafi ta barmu shikenan tabarwa duniya mu, Taheer Adda ta mutu da baqin cikina ta mutu da baqin cikin wannan qazamar rayuwar da mukeyi”
Sai yanzu ya fahimci abinda ya sabbaba mata ciwon ya sake rungumeta cikin tsananin tausayinta da yakejin yana ratsa duk wata qofa ta shigar iska jikinsa.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo masa suka sauka akan dokin wuyanta ya dora habarsa cikin gashinta a hankali yace “ Innanillahi wa innah ilaihirraji’un Allah ya jiqan Adda Habeey” kukane ya sake kwace Mata ta rungumeshi sosai tace “shikenan fah na rasata har abada ko Taheer” shafa kanta yayi yace “dukkanmu a haka mukazo da daidai kuma a haka zamu koma mudaiyi fatan kyakkyawan qarshe”
Kukanta takeyi me quntata zuciyar me sauraro yayi rarrashin duniya taqi tayi shiru, a hankali ta dago tace masa “Adda tabar wasiyyar na koma 9ja nayi aure Taheer ya zanyi da Pappa da kullum yake cewa idan na dawo 9ja saiya tsinemin?”