DUBAI PART 1

Dagota yayi yace “meye asalin abinda ya kawo rikicin jumurdar dake faruwa tsakaninki da mahaifinki? Na roqeki badon kaina don Allah da Kuma darajar mahaifiyarki dake kwance cikin qasa tana sauraronki ki fadamin wani abu game dake”
Kwantar da kanta tayi a qirjinsa taci gaba da rera kukanta tace “banason tuna komai game dani Taheer lbrna bashi da dadin sauraro baudadden lamari ne me wuyar warwara Taheer nifa dama zaka sanya suyimin allurar da zan mutu da nafi farin ciki fiye da rayuwar da zanyi a gaba ta quncin da bansan adadinsa ba”
Rufe mata baki yayi yace “babu abinda bazai wucce ba Babe don Allah ki sanar dani inason taimakonki na mayar dake gda, hakan kuma bazai taba faruwa ba harsai kin sanar dani wacece ke”
Ajiyar zuciya tayi ta dago manyan idanunta da suka kada sukayi jawur tace “nayi maka alqawarin zan sanar dakai abinda ka dade kana tambayata.
Sake mayar da kanta tayi qirjinsa tace
_____________Hajara Liman Ɓillire shine cikakken sunan mahaifiyata amma muna kiranta da Adda, mahaifinta shine limamin masallacin jumma’a na ƙauyen ɓillire yaransa shidda hudu maza biyu mata, mahaifiyarmu macece kyakkyawar gaske me cikar zati hakan yaja Mata masoya daga lungu da saqo na garuruwan gombe.
Abinka da yayan malamai Hajara bata kulasu sai sun nemi izini gurin mahaifinta, ana haka wani mutumin Ganjuwa wanda ya kasance qabilar tangale shima ya shigo cikin maneman aurenta.
Cikin qudura ta ubangiji da Kuma rabo sai Allah ya cusawa Hajar qaunar Dalson Damuna Iro, zuwansa na farko gidan Liman da zummar neman aurenta sai Liman ya kirashi ya sanar dashi yayi hqr babu aure tsakaninsa da Hajar.
Aikuwa Hajar ta shiga tashin hankali ita da masoyinta kullum cikin kuka take shikuma ya rinqa zugeta yana qara cusa Mata qaunarsa a zuciyarta ita kuwa ta saki jiki wutar qaunarsa sai ruruwa takeyi a zuciyarta.
A dabi’ar qauyukan da suke da cakudin addinai ba wani abu bane don auratayya ta shiga tsakanin ahlil kitab maza da mata musulmi duk da abin ya kasance haramtacce a jadawalin dokokin addininmu.
Wannan dalilin yasa Liman ya kafe yace bazaayi wannan abin kunyar dashi ba, qarshe ma da yaga Hajar tana qoqarin bijire masa sai ya zaba Mata miji cikin almajiransa hakanan Liman ya hada auren nan aka ganganda akayisa.
Amma Kuma sai zama yaqi dadi duk wani haqqoqi na aure hajar ta hana Salihu mijin da Liman mahaifinta ya zaba mata sai cin mutunci da tujara kullum cikin sulhu suke amma idan ta koma gdan jiya zaa koma.
Daqyar Hajar ta iya yin wata biyar a gdan Salihu suka hada baki da Dalson sukayi masa kurciyya yabar garin lkcn tana dauke da ciki watanni biyu, ya akayi ya akayi baa sani ba wasu dai sunce kwantar dashi sukayi.
Tsayin sati uku da batan Salihu sai gashi ya aiko da takardar sakinta, murna kamar Hajar ta zuba ruwa a qasa tasha hakanan tayi idda a daddafe Dalson ya dawo sahun maneman aurenta.
Lkcn daya dawo yazowa Hajar da albishir din ya karbi kalmar shahada tayi murna sosai hakanan yazo ya shiga cikin almajiran Liman yana daukar darasi,a gefe guda kuma yana gyara kansa gurin Liman.
Shidai Liman har lkcn zuciyarsa bata kwanta da Dalson daya koma Haroon ba, amma Kuma yaga Hajar ta mutu akansa, har takai lkcn daya kirata yanayi Mata nasiha akan aurenta da Haroon ta fito tace masa itafa yanzu ya qyaleta ta auri abinda takeso.
Hakanan da yaga abin zai zama matsala ya kira Haroon ya fada masa ya kawo sadaki a daura musu aure da Hajar” cikin sati daya akayi biki aka gama amarya ta tare a gdanta.
Farkon zaman Hajar da masoyinta Haroon abin gwanin gwasama amma da zama ya fara nisa sai hali ya fara bambamta Haroon baya sallah azumi ma sai yaga dama yakeyi Haroon bai damu da bawa Hajar abinci ba.
Ana cikin wannan murdadden zaman ne cikin da suka kwantar ya tashi, nan fa sabuwar rigima ta tashi yace shifa saidai a zubar da wannan ciki saboda baya qaunar duk abinda ya shafi Salihu, itakuma tace bai isaba ai shine yace su kwantar dashi tun farko.
Shikuwa ya hanata abinci saidai tayi surfau da dakau da wankau ta samu abinda zataci har cikinta ya isa haihuwa cikin dare naquda ta kamata daqyar ya taso mata wata Mata da suke haya tare Cristian ce sunanta Alheri itace ta karbi haihuwar cikin hikima ta ubangiji Hajar ta haifo sunkuceciyar yarta mace kyakkyawar gaske.
Alheri ce tayiwa Haroon albishir na kyakkyawar yarinyar da suka haifa da farko qin zuwa yayi amma da yaji anata zuzuta kyawun yarinyar sai yazo yaganta kamarta daya da Salihu amma saboda idanunta da hancinta na Hajar ne sai kamar ta buya amma har kalar fatar yarinyar irinta Salihu ce wato chocolate colour.
Yana ganin yarinyar nandanan Allah ya dasa masa qaunarta a zuciyarsa ya daukita yayi Mata huduba da Anitah Nan fah Hajar tayi tsalle ta dire tace aa ita Habibatullah sunan yarta nan ma an samu rikici me yawa kafin kowa ya zabi sunan da zaike kiran yarinyar dashi shi yana kirana da Anitah Addana tana kirana da Habibatullah………
UMMUH HAIRAN CE…✍????
[7/23, 9:24 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI✈️
22/7/2020
Page 15 shine last Free Page, ga wadanda suke buqatar jin qarshen wannan labari zasu biya kudinsu ta wadannan hanyoyin dake qasa single section da nake posting sau daya a rana 200 VIP da nake posting sau uku a rana 600
Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin
Account number
????????
0255526235
Fauziyya Tasi’u Umar
GTB
Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp
????????
09013718241
Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number
????????
09013718241
Episode 17
Haka Addah take rainona ta dauki son duniya ta doramin tun Ina shan nono Addah takeda tarin buruka a kaina, babban burinta shine nayi karatun addinin muslumci me zurfi sannan nayi na boko.
Watanni na goma sha bakwai Addah ta haifi Ibrahim wato Sunday sunan da Pappa yake kiransa dashi kenan, tsakaninmu da Pappa kullum naira biyu da ficika ce nida Ibrahim itace abincin rananmu itace ta darenmu gashi kamar ya kafe Hajar bata iya fadawa kowa matsalarta saidai tayi surfau dakau wankau ta sama mana abinda zamuci.
Taheer tunda nake a rayuwata idan ka dauke kayan jarirantaka zan iya rantse maka baa tabayi mana sabon dinki ba saidai abamu saqabu musaka wasu ma sunyimin yawa haka zanta bunjim bunjim a ciki gani Masha Allah ta ko Ina Allah ya qerani baiyimin qirar wasa ba amma babu kulawa.
Duk da mahaifiyarmu tana iyakar bakin qoqarinta abinne yafi qarfinta ci sha sutura omon wanki sabulun wanka man shafawa duk Addah keyi mana, a haka ta haifi Aishatu wato Hellin.
Nan fa dangantaka ta fara tsami tsakanin Addah da Pappa takai ta kawo Pappa sai yayi wata biyu yana cikin garin gombe amma baizo inda muke ba Amma hakan bazaisa idan yazo Addah ta canza masa kallo ba.
Gashi Allah yayiwa addanmu baiwar aihuwa data tashi sake haihuwa sai tayi biyu Fatima da Idris Wato Ritah da Jumson lkcn inada shekara hudu yar kyakkyawa dani, sanda na fara tasawa ne al’amura suka qara quntata.
Wani dare da bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata daren dana fara fahimtar me rayuwar gidanmu take cewa, Taheer na fito tsakar gida fitsari ya kamani na shiga bandaki na fito kawai sai na tarar da Addah zaune kan kujera yar tsugunno tanata rera kukanta.
Nan na matsa gabanta na zauna na riqo hannunta kawai sai naji jikinta da zafi, Ina Shirin yi Mata mgn naga Pappa ya fito rungume da wata mace a jikinsa yana shafata yana cewa “madam yau kinyi sugar dubu uku zan baki”