DUBAI PART 1

Mamaki ya kamani da naga ya sanya qafa ya hankade addana yace “shashasha da kin dauka ni dan iskane da zan tsaya Ina wahalar sallah azumi sannan insha wahala na tara dukiya ace nayi zakkah to bari kiji Hajar wannan addinin naku na wahalallu yayimin tsauri bazan iyaba Kuma giya da neman Mata yanzu na fara, Hajar bakida wani dadi ni’imarki Habeey ta kwashe da ganin wannan dundubusar yarinyar ruwazata tara bana wasa ba.
Amma dake abin naki son kaine baki bawa yayana ba sai kika bawa yar tsohon mijinki da mota ta niqeshi, to ko ruwana da aka diva aka wanke wannan yarinyar idan ta girma saita biyani da hannunta saboda ni ba bawan wani shege ko shigiya bane”
Nidai sakin baki nayi bata da ina gane ko kalma dayaba Ina kallonsu suka fice Addah ta dago ta kalleni tace “kije ki kwanta Habbatullah kada ki makara zuwa makaranta kinga gobe akwai tahfiz”
Banyi Mata musuba na miqe naje na kwanta amma zuciyata cunkushe da tunanin abubuwa da yawa, abin mamaki Dana tashi da safe banga alamun wata damuwa a fuskar Addah ba tanata aikinta na dauki tsintsiya nayi Mata shara nayi wanke wanke na taso Fatima da Idris nayi musu wanka naja hannunsu zamu tafi Tahfiz amma sai naji Pappa ya kirani da sunan dana tsana wato Anitah.
Babu yanda zanyi haka na juya na kalleshi yace “sakesu dan ubanki kedai da kika gaji wahala kije kiyi amma yayana bazasuyi wannan wahalar ba”
Tatar qullin kunun da Addah takeyi ta bari tace “wai da gaske kakeyi maigida kayi riddah?” Batare da tunanin komai ba yace “Ni dama ban musulumta ba balle nayi riddah sani nayi wannan daqiqin uban naki meci da buguzun bazai bani aurenki ba sai nayi masa basaja bakisan wani abuba yanzu haka church gudace a hannuna saboda haka Hellin Sunday Ritah da Jumson Yaya nane bana buqatar ki qara dangantasu da addininki”
Duk da ba komai nake fahimta ba amma kalaman na qarshe sunfi komai girgizani ina tsaye kamar dashe yazo ya janye qannen nawa ya mayar dasu ciki nikuma addah ta kalleni tace “jeki makarantarki kinji Habbatullah” hakanan natafi tahfiz din ni kadai.
Tundaga wannan ranar su Aisha suka daina zuwa makarantar islamiyya saida Adda ta koya musu, ana haka sai Dalson ya tsiro da wata tsiya wai lallai sai Addah ta rinq binsa church, itakuma tace Allah kasheta bazata ba nanfa dangataka ta qara tsami kullum sai Dalson yayiwa Addah dukan mutuwa sannan yaje ya shawo giyarsa yazo yayita sheqa Mata amai hakanan zata wanke kuma ya jibgeta.
Nikam dukan yana damuna amma ban isa na fadaba sai Addah tacemin Ina ruwana ai laifi takeyi masa shiyasa yake jibgarta, ana haka labari ya ishe liman na cewa Haroon yayi riddah ya koma kafircinsa.
Nan fa kakanmu yayo tattaki har zuwa garin Ganjuwa yazo domin qwatarwa Addah yancinta amma fir tace itafa a qyaleta da mijinta zata zauna dashi a haka saboda idan ta tafi bazai bar mata yayanta ba kuma tasan canza musu addini zaiyi.
Taheer duk yanda Liman zaiyi yayi amma Hajar taqi basa hadin kai har cewa yayi zai bata gidan zama anan cikin birnin gombe da jari me tsoka sannan zai shigo da hukuma ta qwatar mata yayanta amma taqi yarda wai ita idan ta rabu da Dalson mutuwa zatayi.
Wannan bacin ranne ya sanya Liman tattara kan zuri’arsa yace ya sallamawa Dalson Hajar ko mutuwa yayi bayason tazo kan gawarsa.
Tun daga wannan ranar komai ya qara lalace mana duk cikin yaran gidanmu mu biyar ni kadai nakeyin karatu shima wani Alh ne ya dauki nauyi na saboda nidin qawar yarsa ce Zainurah amma sauran qannena duk basa arabi basa boko sai tallan burkutu da Pappa yake dora musu sukai church.
Haka rayuwar tayita tafiya cikin qunci talauci da qangin rayuwa, a zahirance Pappa bayada mahaukacin talauci amma ya rantse daidai da ransa indai Addah batayi riddah ba to bazata qara samun tallafi daga gareshi ba itakuma tace ya riqe tallafinsa bata buqata.
Daqyar Addah tasamu ta dorani akan tarbiyyar islama saboda tanayi ne Pappa na warwarewa duk cikin yayan Addah ni da Aisha ne kawai mukebin addinin muslumci sai Ibrahim da naji lbrn shima ya musulumta yanzu.
Girma nakeyi sosai bana wasaba shekaruna goma sha uku duk wasu halittuna suka gama bayyana komai nawa na musamman ne, tun a lkcn samarin maza yayan masu halin garinmu suka rinqa kawomin caffa amma naqi domin zaman gidanmu ya dasamin tsoro da tsanar da namiji cikin zuciyata gani nakeyi duk wani namiji irin halin Pappa ne dashi sai gashi a hankali Taheer ka tabbatar min da zatona gsky ne ko babu bambamcin addini akwai zalumci tsakanin namiji da mace.
Komai ya fara lalacewa Pappa takai ta kawo an qwace church din dake hannunsa saboda neman matansa da Kuma lbrn da yajewa pastor din cewa baya kula da iyalinsa.
Itama burkutun aka daina siya ko mun fita da ita haka muke dawowa da ita nicema saboda kyawuna nake danyin ciniki, kawai sai ya yanke shawarar komawa facin motoci.
Bakin titi ya karbi hayar guri ya kama sanaarsa kullum zankai masa abinci zamu zauna muyita Hira dashi nikam Pappa baya nunamin wani abu na qyama komai zaice yata Anitah hakan yasa na saki jiki dashi, inda ya dauki buri ya dorawa kyauwuna har cewa yakeyi bazaiyimin aure ba saina tara masa dukiya.
Wata ranar juma’a an tashemu daga makaranta muna tafe nida Zainurah duk wata halitta ta jikina tana rangaji, munzo wuccewa ta wata majalissar matasa sai wani natashi da ake Kira Nafi’u Mai saa ya taso ya biyoni nikuma tsoronsa ma nakeyi saboda kisa ba wuya yakeyi masa ba a gabana wataran ya dabawa wani yaro wuqa.
Aikuwa na kwasa da gudu na shige rumfar Pappa lkcn wata Hajiya tana zaune yanayi mata facin mota yana ganina ya taso yace “ya akayi kike gudu” fadawa nayi jikinsa Ina haki ya rungume ni yana shafa bayana.
Saida yaga na nutsu sannan ya tambayeni menene, nan nake zayyane masa abinda ya faru, nanfah Pappa ya ringa fada itadai Hajiyan nan sai kallona takeyi har na juya zan fita ta kirani naje tace “ya sunanki?” A gajiye nace “Habbatullah” murmushi tayi ta dauko yan dari biyar guda biyu tabani tace nasai kayan kwalliya.
Nayi gdy na tafi inata murna yau Addata zatayi mana girki da nama saboda ni Allah yayini dason naci dadi a rayuwata banason qazamin abinci, ban dade da shiga gidaba Ina mayarwa da Addah abinda ya faru Pappa ya shigo afujajan yana qwalamin kira…….
UMMUH HAIRAN CE…????
[7/23, 4:44 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: DUBAI
22/7/2020
Page 15 shine last Free Page, ga wadanda suke buqatar jin qarshen wannan labari zasu biya kudinsu ta wadannan hanyoyin dake qasa single section da nake posting sau daya a rana 200 VIP da nake posting sau uku a rana 600
Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin
Account number
????????
0255526235
Fauziyya Tasi’u Umar
GTB
Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp
????????
09013718241
Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number
????????
09013718241
Episode 18
A firgice na tashi na fito daga dakin kaina ko dankwali babu, Pappa ya figi hannuna yayi waje dani Allah bai bawa Addah ikon yin mgn ba muna fita naga Hajiyan nan ta dazu gabana ya fadi amma ban iya cewa komai ba.
Inaji sukayi yarensu na tangale tayi masa godiya ya dawo kusa dani nace “Pappa Ina zatakaini naji kana cewa sai kunyi waya?” Ranqwashi ya sakemin yace “kajini da shegiyar yarinya da idonta kamar dinya nunanna to unguwa zaki rakata maza shiga mota kuje ku dawo”
Zuciyata bata nutsu ba amma nasan inayin gardama akan Addah ta zai hucce hakanan na shiga ta kalleni tayi murmushi tace “talaucinku ya yanke Habeey daga yau kedai ki saki jiki duk abinda aka sanya ki kiyi”