DUBAI PART 1

DUBAI PART 1

Nidai bansan ya wasan ya qare ba sai farkawa nayi na ganni a asibiti Aysher na jinyata, lkcn dana farka nayi nadamar abubuwa da dama ciki harda saninka da nayi har qaddara tursasawar mijin mahaifiyata danake dauka matsayin mahaifi tunda duniya batasan wani ubana bayanshi ba ta haifarmin.
Nayi kuka mara iyaka ina tambayar kaina yanzu shikenan na rasa Heimen din budurcina ka rabani dashi saboda kudi? Idan na tuna hakan nakanyi kuka kamar rayuwata zata qare tun daga wannan ranar na ciwa kaina buri da alwashin bazan taba son wani da namiji ba balle naji Ina burin aurensa ya jefani da yayana a irin halin da Pappa ya jefamu nida yan uwana.

Taheer kasha ganina Ina kuka duk lkcn da ka nemeni bawai kukan rashin sabo bane aa cikin sati biyun da mukayi tare dakai dole da wahala tasa na saba saboda jarabarka abar bugawa a mujallah a siyarce ko a tarihi inajin labarin jarababbun maza amma bantaba tunanin akwai irinka ba wanda idan ka kama mace kakeyi Mata cin qoshi ba kamar kai.
Inayin kukane saboda baqin cikin Pappa ashe badon mahaifiyata yasani sallama maka abinda na dade Ina tattali ba aa kawai saboda karuwarsa ne Grease itace taje tayi sata aka kamata yakeson yayo belinta yasani fansar da budurcina saboda a ceceta.

A lkcn inata gwada wayar Addah bata shiga ashe yayi tunanin zan Kira shine ya dauke wayar, kwana biyu bayan tura kudinnan mukayi waya dashi nayi tunanin zai tambayeni ya akayi na samu kudin aa shikam ba damuwarsa bace damuwarsa kawai.
“Anitah ki rinqa dafa ruwan zafi da gishiri kina shiga ciki saboda rashin sabo a hankali zaki Saba ai dama mace saida namiji kedai ke kula da kanki ki nemi magunguna masu kyau kina amfani dasu”
Wadannan kalamai suna girgiza duniyata da tunani na har cemin yakeyi na saki jikina naji dadina shine yake bani shawarar kada na yarda namiji ya kusanceni ba comdom, Taheer in taqaice maka zance bayan ni ya baza Aisha da Fatima qannena qasashen duniya yawon karuwanci don nasan qarshan dai alewa qasa ce sannan a qarshen qarshe baqin cikin halin da muke ciki da labarin wannan liqaqqen cikin daka liqamin yasa zuciyar Addata bugawa ta mutu tabarmu cikin ha’ula’i Taheer Addah ta mutu bata hadani da mahaifina ba duk da har yanzu baasan duniyar da take ba amma wasu sunce suna ganinshi a talabijin itama addah tasha fadamin tasha ganinsa a TV yanzu ya zaayi ya yarda niba jinin wannan kafirin bace ya karbeni a matsayin ƴarsa?”………….

UMMUH HAIRAN CE…✍️
[7/27, 10:34 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI✈️

PAID BOOK

HAƘƘIN MALLAKAR
              ????????
FAUZIYYA TASI’U UMAR
(UMMUH HAIRAN)

Masoya wannan littafi mai farin jini wato Dubai dake qasar Niger, ga dama ta samu
Kuma zaku iya kasancewa da wannan littafi na Dubai ta hanyar turo da katin Orange na kudinku Wanda zaiyi daidai da 200.
Idan VIP kikeso zaki turo da katin da zaiyi daidai da 600 kudin Nigeria kada ki manta da lambar da zaki turo katin ta WhatsApp

09013718241

Idan kuma a Nigeria kike zaki turo katin MTN ta WhatsApp a wannan number dake sama ko ta account number

0255526235

Fauziyya Tasi’u Umar

GTB

Don Allah idan kinsan baki biya ba kada ki karanta VIP 600 single 300

Episode 26

Wannan shine abinda na sani game dani Taheer nayi mu’amala da maza da dama amma bantaba haduwa da namijin da yake wahalar dani kamarka ba Taheer don Allah ka mayar dani qasata ka rabani da cikin nan….”
Rufe mata bakinta yayi yana girgiza kai labarinta ya taba masa zuciya tausayinta ya nunku a zuciyarsa ya miqe a hankali yace “kiyi hqr Habeey kome kikeso zan iyayi miki amma banda zubar da cikin nan wlh tallahi inason cikina kiyi hqr ki haifemin abuna muyi aure mu raini danmu”

Sauka yayi ya hado mata abinci ya kawo mata yana zuwa ya tararta ta hade kai da gwiwa tana kukanta me dafa zuciya, ajiye kayan yayi ya matsa gabanta ya tallafota yana shafa cikinta yanajin yanda babyn cikinta me wata shidda yaketa motsi yayi murmushi yace.
“Babe na yanada lfy kamarni” itadai bata iyace masa komai ba sai zamewa da tayi a jikinta ta koma ta kwanta tana ajiyar zuciya, dagota yayi yace “bazaki barmin babe da yunwa ba jiya bakici abinci ba yauma ki zauna da yunwa, aa bazai yuwu ba kiyi har kibarmin komai insha Allahu komai yakusan zuwa qarshe nidai burina kada ki juyamin baya ki bani hadin kai zamu kai inda mukeso mukai yanzu dai waye ya fadawa Addah kinada ciki?”

Dagowa tayi suka hada ido yayi mata murmushi yace “inason sani saboda musan matakin dauka Koda yake yanzu ma ba wannan ne a gabanmu ba”
Itadai bata qara cewa dashi komai ba ta koma ta kwanta ya sake dagota ya rinqa bata tea din tanasha saida tasha sosai sannan ya barta ta kwanta bacci ya dauketa, saida suka qara kwana sannan suka koma gidansa duk yanda yaso suci gaba da mu’amala amma fir taqi saima kuka da takeyi masa to shima yanzu tausayinta ya danne sha’awarta shiyasa bayayi mata dole kamar yanda ya saba binta yake a hankali har yagama yimata cuku cukun komawarsu.

Ko sallama basuyi da Aysher ba suka dauki hanyar 9ja Koda suka isa baikaita gidansu ba kuma bai barta taje gida ba gdansa ya sauketa Amma sunsha fama kafin ta yarda akan zata kwana a gidan dayake darene washegari zata tafi.
Shima anan ya kwana tare da ita da safe gari na wayewa yasa aka kawo masa mota cikin sirri daga gdansu ya dauketa suka nufi gombe.
Suna tafe duk inda yaga wani abu saiya tsaya ya siya mata, kallonsa kawai takeyi tana hawaye zuciyarta na quna tana tuna yanzu shikenan idan taje gidansu bazata tarar da Addah ta ba.

Mamaki ya cikata da ganin yanda yakebi lungu da saqo har suka iso unguwarsu yayi parking a jikin gdan Pappa, ya juyo ya kalleta itama shi take kallo yayi murmushi yace “kinyi mamaki ko?”
Lumshe idanunta tayi yace “bai kamata kiyi mamaki ba Habibah maso dan tsuntsu shine yake binsa da jifa, fita mu shiga cikin gdan ayi duk wacce zaayi, qasa tayi da kanta tana shafa cikinta ya dora hannunsa akan cikinta yace “bazakiyi danasani ba indai akan ciki nane muje ki huta baby na ya huta”

Bude mata qofar yayi suka fito tana daga mayafinta saboda tsoron kada ya manne a jikinta cikinta ya fito, mamaki ne ya kamata ganin yanda aka gyara gdan kamar ba gdansu na qasa ba.
Shine yayi mata jagora har cikin gdan saiya zamana kamar itace baquwar suna shiga Pappa yana fitowa daga dakin matarsa Graise ya tsaya cak yana kallonsu itama tsayawa tayi tanayi masa kallo biyu na mamakin qibar da yayi da Kuma ganin wata Matar ba Addanta ba ta biyo bayansa sai kuma na tsantsar tsanarsa da takaici hadi da baqin cikin biyayyar da mahaifiyarta ta rinqa tursasata tayi masa a baya yanzu ga abinda baqar biyayyarta taja mata……..

UMMUH HAIRAN CE…✍️
[7/27, 10:35 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI ✈️

PAID BOOK

Idan kinsan baki biya ba kada ki karanta in kin karanta keda Allah, VIP 600 SINGLE 200

Account number

0255526235

Fauziyya Tasi’u Umar

GTB

Ko katin waya MTN ta wannan number

09013718241

Yan Niger zaku turo katin Orange Wanda zaiyi daidai da 600 dinmu idan VIP ne idan SINGLE ne wanda zaiyi daidai da 200 dinmu ta Nigeria.

Episode 27

Kallon kallo sukeyi da Pappa kafin daga bisani taga Taheer ya tsugunna yana gaisheshi bai amsa gaisuwar Taheer din ba sai wani mugun kallo da yakebin Habeey dashi har ya iso gabanta ya damqota yace.
“Ubanme kika dawo kiyi a qasar nan da izinin wa kika dawo ko an fada miki tsinanne ne ni har kin gama biyana kudina da Zaki dawo?” Saurin miqewa Taheer yayi ya finciketa ta qarfin tsiya ya dakawa Pappa tsawa yace “kada ka kuskura ka qara tabamin Mata wannan ai haukane bakaga yanda take bane”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button