DUBAI PART 1

DUBAI PART 1

Ajiye wayar yayi ya fita ya nufi parlourn Dad din qirjinsa yana bugawa Amma sai ya aro juriya ya sanyawa ransa ya shiga da sallama Dad ne kadai ya amsa masa ya zuba masa ido har ya iso gabanshi ya rusuna yayi zama irin na daa yace “Dad na sameku lfy?” Furzar da iska Dad yayi yace “meye yake faruwa ne tsakaninka da Mom dinku?”
Shafa kansa yayi yace “ah wani abu tace maka Dad nidai bansan komai ba ohhhh wai ko maganar jikan da zakuyi ne ta kawo maka, to ai wannan ba tsakanina da ita bane tsakanina da rayuwata ne……” wani mugun mari Dad ya sauke masa yace “kai wanne irin dan iskan yarone ne Taheer anya kuwa kai danane jinina ne nikam ina tantama akanka, komai naka daban tunaninka daban Taheer haihuwa zakayi a titi dan shege kake dangata tsatsona dashi?”

Miqewa yayi a hassale yace “aa fah Dad kads ka qara shegantamin ciki shege a gidan aure akeyinsa tsakanin ma’aurata nikam cikina saidai ka kirashi kafin fatiha” juyawa yayi zai fice Dad ya fincikoshi da qarfi yace “baka isaba Taheer ka zubarmin da qimata da mutuncina a idon duniya dole ka kaini a dauki yarinyar nan a zubar da cikin nan ko kuma a batar da ita da abinda zata Haifa”
Tabe baki yayi ya kallesu sheqeqe yace “wannan ne kuma fah babu wanda ya isa yasani nayi laifi biyu najima da na zinar mana wanda kune kuka sabbabamin shi amma bazanyi kisa ba kisanma na abinda nafi qauna a rayuwata Dad yanda nakejin habeey da cikin jikinta wlh zan iya yafe kowa a duniya please Dad kada kayimin dole kaikam ks tausayamin mana wlh Habeey tafi Kubrah da Bushirah tarbiyya qaddararmu ce wadannan abubuwan da suka faru wanda Allah shi kadai yasan abinda yake nufi damu”

Miqewa Dad yayi ya fara zagaya dakin shikuma ya sace jikinsa zai fice Mom tace “zonan dan ubanka yanzu ba mgnrka mukeyi ba mgnr mafitarmu mukeyi gabadaya wannan abin da kayi abune da zai taba qima martabarmu da kuma daukakarmu Taheer ka fahimcemu mutuncika mukeson karewa” juya yayi ya nufi qofa ya fice da sauri ya koma part dinsa bugun duniya yaqi budewa saboda shidai saidai suyi duk abin da sukayi niyya amma yanason cikinsa kuma yayi alqawarin indai basu yarda ya auri Habeey ba to a haka za tayita haifa masa yayansa qarshe ma ya dauketa subar qasar kowa ya huta shi da ace da wata duniyar ma can zasu tafi suyi rayuwarsu cikin farin ciki ya mantar da ita duk wani damuwa dake damun zuciyarta………..

UMMUH HAIRAN CE…✍????
[7/28, 6:13 PM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ DUBAI ✈️

PAID BOOK

Idan kinsan baki biya ba kada ki karanta in kin karanta keda Allah, VIP 600 SINGLE 200

Account number

0255526235

Fauziyya Tasi’u Umar

GTB

Ko katin waya MTN ta wannan number

09013718241

Yan Niger zaku turo katin Orange Wanda zaiyi daidai da 600 dinmu idan VIP ne idan SINGLE ne wanda zaiyi daidai da 200 dinmu ta Nigeria.

Episode 29

Ita kuwa Habeey tunda ya tafi ya barta take faman yiwa Addah magiya Amma taqi sauraronta hakanan ta koma gefe ta zauna ta dora kanta a saman akwatin kayanta taci gaba da shassheqar kukanta tanajin ninkin nadamar abubuwa da yawa.
Ibrahim ne ya gyara mata wani daki jikin na Addah ya shigar Mata da kayanta yazo ya dauko Mata abinci yakai mata tare da zama kusa da ita yace “nayi mamaki kuma na tsorata lkcn da aka Kira wayar Addah ake fada mata karuwanci kika zaba a Dubai kin ma bi saurayinki kun tafi Malaysia kuma ma cikine dake, bamu zaci haka daga gareki ba Aunty Habbatullah ko kadan ban taba tunanin hakan zata faru ba” itadai kuka kawai takeyi tana girgiza kai.

Matsawa yayi ya tallafo kanta yace “ya akayi haka ta faru Aunty Habbatullah?” Cikin shassheqa tara basa labarin komai shima hawaye yakeyi yace “kinyi ganganci da kika rinqa biyewa hudubar Pappa yanzu gashi ya kaiki ya baroki” miqewa yayi ya fita ya shiga dakin Addah ya zauna kusa da ita tanata matsar ido yace “ya kamata ko kowa zai juyawa Habbatullah baya kekam karki juya Mata domin komai ya faru da itane ta sanadin qaryar da mijinki ya rinqayi Mata da baki da lfy kina asibiti kina karbar magani har tayi sabo da maza Addah hanunka bai taba rubewa ka yankeshi ka jefa…”

Daga masa hannu tayi tace “ka tsame bakinka daga abinda ya shafeni nida Habibah wlh da basan irin yayan dana haifa kenan a duniya gara inyi barinsu….” Rufe bakinta tayi saboda shigowar Habiban ta tsugunna ta riqe qafarta tace “gani gabanki mahaifiyata wlh duk hukuncin da kika yankemin idan har zai zama sauqi da sassauci wa zuciyarki zan karbeshi nasani Addah nayi kuskure amma duk da haka Addah ki tausayamin kiji qaina rahamarki ta kwaranyo cikin rayuwata bani da kowa saike kuma bani da komai saike kw kadai nake tsammanin jinqai da rahma daga gareki…”

Tureta tayi ta miqe zata fice daga dakin tayi saurin kamota tace “na roqeki da girman Allah ki yankemin hukunci Koda na kisane Addah duk duniya babu wanda zaice yafini baqin cikin taskun da rayuwata take a ciki Addah bantabajin kaico da baqin cikin halittata a matsayin ya mace ba kamar yau….”
Hankadeta tayi tace “na tsaneki Habbatullah na tsani ganinki Kin cuceni kin gurbatamin zuri’ata kinyimin tabon da bazan taba mantawa dashi ba kaico Habbatullah kaico da haihuwar asara irinki danasani da mahaifinki ya bata zubar da cikinki nayi da wannan mugun tabon da kikayiwa zuciyata Allah ya is…..”

Saurin rufe mata baki Ibrahim yayi yace “Haba Addah da wanne kikeso taji ne don Allah ki sassauta mata mana kowanne bawa baya wucce qaddararsa kece kike fada mana haka kullum….” Katseshi tayi da cewa “wlh idan Habibatullah bata bacemin daga qwayar idona ba saina tsine Mata ta qara tambadewa ta lalace gabadaya”
Miqewa Habbatullah tayi idanunta na shararar da hawaye tace “indai hakan yayi miki nima yayimin Addah amma ki sani duk halin dana tsinci kaina a ciki nan gaba babu hannun Pappa kece me ruwa da tsaki domin kema uwar da kika haifeni kin gujeni kin qyamaceni Addah bazanji ciwo ba kuma bazanji haushi ba idan mutanen duniya gabadaya zasu qini”

Tana gama fadin haka ta juya ta fice da sauri ta dauki akwatin ta tana kallon gdan tana kuka a ranta tanajin anya kuwa ita ba yar tsuntuwa bace, biyota Ibrahim yayi ya riqe akwatinta yace “wlh babu inda zata Addah saidai ke ki tafi tunda ke kinsan inda zaki ita kuwa fah Ina ta sani hannun wa zata qara fadawa? Haba haba Addah wannan rashin adalci ne kiji tausayinta mana a yanda take dinnan ga dare yariga yayi”
Qwacewa tayi tace “wlh tallahi saina fita daga gdannan Ibrahim gara ta kwana cikin salama koda ni zan kwana a saman juji nasani duk yana cikin qaddarata”
Ficewa tayi da sauri Ibrahim yabita yana roqonta ta dawo ta tsayar da Napep ta sanya kayanta ta juyo ta dafa kansa tace “kada ka damu qanina zan shiga cikin garin Gombe zan nemi gida na kama kafin Addah ta sauko nayiwa kaina dakai da Addah alqawarin bazan qara aikata wani abu na sabo ba insha Allahu ka tayani da addu’a kaji?” Hawayensa ya share yace “amma aunt….” Rufe masa baki tayi tace “nafi buqatar farin cikinta da nawa kaima kayi biyayya da farin cikinta kaji Addah tariga ta rantse idan na samu gda zan fada maka sai kazo ka gani”

Kudi ta zaro masu yawa a Jakarta ta basa tace “ka kula da kanka kafin muyi waya kaji qani na” Napep din ta shiga tana hawaye tana daga masa hannu shima yanayi yana daga mata harta qule, sunyi tafiya me tsayi kafin su fito gari da yake darene qofar wani hotel yakaita ta sauka ta biyasa ta shiga ta kama daki suka bata mukulli ta shige ciki tayi wanka ta fada gadon tana rera kukanta me ban tausayi tanajin wayarta tanata ring amma takasa duba ma wayene saboda ji takeyi kamar ta kashe kanta ta huta da wannan quncin rayuwar, tambayar kanta takeyi ita yaushe zatayi farin ciki ne a rayuwarta?………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button