FITAR RANA 18

FITAR RANA 18
Happy birthday to me,(surayyahms)
“Today 26th may i celebrate myself for being able to take off the mask i wear out and knw who i am underneath,for being vulnerable enough to accept my flaws nd knw dat those are wat makes me human nd real,.for being confident enough to cherish my strenght witout hiding or minimizing them cos they are my beautiful gifts to share with the world.nd For being brave to say i knw wat,and oll of it.”sumtimes i can be messy,full of shits nd mistakes,my undying forgetfullnes,despite that, “im soo proud of me,proud of who i am, nd proud of wat im becoming and dats wat i call selflove!”..happy birthday to impecable me..longlive nd prosperious 365days in health nd wealth for decades SUSU,HBD SURAYYAHMS#.
A sandare taheer ya tsaya yana kallon saheeb da tsananin mamakin sa a yanayinsa,ji yay kamar ana sare masa gangan jikinshi da takobi,wani runtse idanunshi yay game da dunkule hannayensa ayayin da wasu mahaukatan jijiyon dake hannayensa suka harzuka sukayi tauri suka wani murmurdu..
atake jikinshi ya soma kyarma bacin rai da baƙar kishi su suka hadu suka makantar dashi baiya ganin komi agabanshi sai duhu duhu yanajin wani abu mai tsananin ciwo da radadi na tsaga masa kahon zuciya.
A duk inda taher ya kasance wasime takan ji alaman hakan ajinin jikinta sabida ƙarin bugun zuciya da mummunan faduwar gaba,atake atake taji ta ƙara tsorata,kkrin ture saheeb takeyi shikuma yana bijirewa,tana waigowa kuwa saita hade ido da taheer a tsaye akansu kamar wani fatalwa, wani irin ja da baya tayi tanamai kara sautin kukan ta a mugun rude tace”wayyo Allah na”Nifa bana son haka..bana so..bana so.
Tafada tana tutture saheeb din shikuwa bai lura ba,kkri yake yi don ya jawota jikinshi,sam taki tahau matsawa baya baya tana kkrin hankarar dashi cewa taheer ya shigo yana kallonsu
Can baya baya ta matsa har sanda ta jingina bayanta da jikin gadon ta rakuɓe snn ya farga,a dan fizge saheeb Ya juya sai caraf suka hade ido da taheer dake kallonsa cikin wani irin rikitacciyar yanayi mai tsoratarwa.
Baisan sanda ya miƙe tsaye ba,kallon juna suka tsayayi,agaggauce jikinshi yahau rawa with so much guilty consience duk ya daburce ya rasa abunda zai fara cewa.
Dan Lumshe idanunsa
Yay cikin neman wa kansa karfin gwiwa,wani huhhhh ya sauke tukikin numfashi snn ya daure yace “Taheer!
Hannu ya daga masa azafafe alaman baison jin komi.
Bai fasa ba yace “
Taheer im sorry abt this..
“Look,is not what u think okay?bayani yafara masa akan asalin abunda ya kawosa na qudirin basa hakri akan abunda ya faru da wasime jiya.
Gaba daya taheer ya kasa daurewa dan shikadai kawai yasan
Zafin dayakeji a zcyarsa yanzu.
Yi yy kamr baiji saheeb ba,kuma dagsken ne baijinshi,duk wani maganganun daya furta baiji ko daya ba tsabar yadda zcyarsa ta raunana tayi baƙi kirin har gani yake kamar zaiiya hallaka saheeb ya kuma kashe shi har lahira inyace zaiyi fada dashi koya dokeshi.
gabaki daya kishin matarsa da damuwa suka taru suka cunkushe masa zuciyar sa,ransa tay matukar lalacewa,a rayuwarsa sam bai san meye so ba,bare ma yasan zafin kishi. amma ayanzu haka a lokaci guda yakejin wayannan feelings din duka biyu suna azabtar da shi,ya rasa meyasa ma tun farko bai dauki aurensa da muhimmanci ba?whats it bcos she is just a girl?..he deeply regrets his decision right now.
Akan mema yasa zai boye aurensa?who the hell is saheeb,nd who is the whole world to judge him over his personal life?yanzu ne yasan yayi kuskure da wawanci mai girma,at same time he was feeling confused abt his emotions,tun usuli shi bamai tsoro bane,akan harkan rayuwarsa baya shayin uban kowa shikansa yasan da hakan,amma sai yaga akan wasime kominshi ya sauya ya lalace,tsoro da nauyin zuciya su suka danneshi suka hanashi nunawa duniya cewa ita din tashi ce,kawai dai yasan bai shirya ma tarban abun bane.
Maybe He just accepted it wholeheartdly dominya faranta ma iyayen sa rai ne Kuma yasan zaiyi zaman soyayya da wasime ne sabida ya samu rahmar ubangiji da kuma lada.
Aure at his young age to a younger gender ba abu bane wanda xai shirya masa cikin gaggawa,he need this little time to compose himself,hes tryng so hard to be true nd to make sure of what he is about to feel for her..the strees of telling his friends is just waht he neva wanted to confuse him or confuse his decision to accept her.
Yana son inhar zai amshe wasime arayuwan sa toh ya fison ya sake ranshi ne gabaki daya ya amsheta,ya kuma sota da xcyarshi,snn ya kaunace ta,Ya bata dukkan wani kulawa da kariya domin Allah badon kowa ba.
A tunaninshi hakan bazai taɓa yuywa ba inhar ya fallasa alakrsu wa duniya musamman ma wa abokansa,yasani dayawa acikin su zasu saka masa kokonto acikin zucyarshi,wasu zasu mocking dinshi suyi masa dariya sabida ayi nishadi,wasu kuma zasu karkatar dashi ga barna wanda yasan inyay hakan zai iya cutar da ita.
Shima din yarone haryanzu amma yasani sarai cewa da akwai yaranta sosai ajikjn sauran abokansa inda ya bayyana musu yay aure da zasu iya lalata mishi tunaninsa da shawarwarin banza.
Saidai bai taɓa tsammanin yarintar harda saheeb aciki ba
Asalin silar fara abokantar su da saheeb sabida halayyarsu ta kamun kai yadan zo kusa ne,dan shi saheeb baiya nuna cewa shi yarone sabida sunada kudi kuma baiya nuna gazawarsa a fili rayuwan big boys yakeyi kafin nan yazo ya soma shan giya,taheer baiji dadin hakan ba amma ya bar hakan ne akan saken iyaye da kuma tarbiyan banza da aka basu irinna yaran da aka ɗasa musu son rayuwar nasara,da tsara musu shi acikin tsarin rayuwarsu,sai aka jefar da koyarwan addini da al’ada aka nuna musu wanncan rayuwar nasarar itace rayuwar masu ilimi da wayayyu.
Tunda saheeb ya soma shan giya kominsa ya lalace,ya soma sex da yan mata…duk aganin sa hakan ba komi ba is just a way of life kowama inyaga dama zaiyi.
sumtimes Yakan dauke taheer ne a matsayin wanda baisan dadin rayuwa ba,kuma dan talaka wanda baisan dadin duniya ba.
Mai girman kai da jiji da kanshi sabida taheer bai taɓa yunkurin nuna wani abun duniyar da saheeb ya mallaka yana burgeshi ba,.duk shakuwr su da shi da wuya kaga taher acikin tsabgar saheeb musamman in abun ya shafe abun duniya ko matsayi..ther y just cool friends for good snn jininsu ya hadu sabida sukan iya tolerating juna.
Ya tuna tun farko washi ya soma jin shaukin fallasawa alakar sa da wasime kodama xai karfafa masa gwiwan sa akanta, amma ta dalilin yawan shan giyansayasaka shi ya fasa maganan yy shiru.
wani runtse idanunsa yayi cikin tsananin fushi yana huci mai karfi game da jin haushin kansa matuka akan kuskuren da yay na boye masan tun farko.
.,da hannun sa dake bari yay pointing bakin kofa ransa matikar bace, in ransa na bacen, yasani sarai baxai iya aikata wani nagartaccen hukunci ba,ahankli yace wa saheeb…
“Malam kazo ga hanyarka!.
Jikin saheeb duk yay sanyi gwiwarsa ya sace
Ya juya kadan ya kalle wasime data kanannede kanta ta takure waje guda tana kuka sosai.
Wani abu yaji yana tsarga masa na tausayin halinda ya jefa ta aciki,tun daga kansa har xuwa tafin kafarsa yake jin sacewar jiki da karyewan xcya,ji yay kamar baxai taɓa iya hakura da ita ba har abada.