NOVELSRANA DAYA

RANA DAYA BOOOK 2 CHAPTER 8

Mun tsaya

Ya ce, “Ke! Ba wani wayo da zaki yi min. Cire ki ajiye rigar daban sannan ki dauki wannan ki gwada, kuma saura kiftawar ido goma in ce uku.”
Da sauri ta cire rigar sai ta juya baya ta kuma kulle idanunta, sannan tasa hannuwanta ta harde, ta rufe kirjin. Dariyar shi ta kasa rukuwa sakamakon sikyat din da ta sa a jikinta, ta kuma daure da dankwali a kugunta, alamun yayi mata yawa sosai.
Yayi dariya har da hawaye, ita kuma tana ta dan kukanta jikinta kuma yana ta ɓari. Ya ce, “Salma wannan siket din fa da ki ka daure kugu da igiya? Cikin kukan ta ce, “Ya min yawa ne, kuma bani da wani.”

Yanda tayi maganar ya sake ba shi dariya. A ranta kuwa cewa take, “Mugu kawai, dole ka min dariya. ” Ya ce, “To kwance wannan madaurin.” Ta ce, “In na kwance zai fadi fa Yaya.” Ya ce, “Kin juya baya kina min magana bana jin me ki ke fada. Bari in zo in juyo da ke.”
Ta ce, “Yi hakuri Yaya, Allah zan juyo.” Ya ce, “To juyo.” Ta juyo. Fuskarta ya kalla sharkaf da hawaye, idanunta a runtse, hannuwanta a makale a kirjinta.
ya tashi ya tafi a sannu, bata ji zuwanshi ba sai dai taji an ja dankwalin da ta kulle siket din, lokaci daya kuma ya warware. Da sauri tasa hannu ta riko siket din. Ya saki sabuwar dariya tare da fadin, “To ai
kuma kin bude kirjin.” Ta tsugunna da sauri tare da fadin “Na shiga ukuna!” Yayi dariya sosai sannan ya shige bandakinta tare da fadin “Ki zo kiyi alwala muyi sallah irin ta ma’aurata.” Yana wucewa tayi maza ta saki siket din, sannan ta dauki rigarta ta maida.

Ya fito ya ce, “Kije kiyi alwala.” Wuf! Ta
shige bandakin. Taci kuka, a ciki sannan tayo
alwalar. Ta samu ya maida akwatin ya ciro wata
yasa kayanshi, sannan ya cire na jikin shi yana saka na bacci.
Ta juya baya don lokacin da ta fito yana kokarin saka dogon wando a kan gajeren jikinshi, sannan bai kai ga sa riga ba. Ya kalle ta yayi murmushi. Sai da ya shimfida Darduma, sannan ya ce, “Kin juya baya kamar kin ga abin tsoro, ki sa hijabi ki zo muyi sallah.”
Bayan sun idar ya ce ta dauko musu kajin
Amarci su ci. Gabanta ya fadi, ta tuna da suka je
kauyen Innarsu biki wanshekaren da aka kawo
Amaryar suka je dakinta shi ne ta ke ba su labari,
wai in ango ya kawo kaza da daddare amarya ta yarda ta ci, to ango zai ce ta biya shi. Sai Salma ta ce, “To kudi za ka ba shi?” Sai Amarya ta ce, “Tab! Kama ki zai yi yata wahalar da
ke, kuma ko kina ihu ba zai bar ki ba.”
Duk da Amaryar ba ta fayyace ba, Salma ta gane abin da take nufi. Ya katse mata tunani da cewa, “Shima abin tsoro ne cin kazar?” Ta ce, “Na’am!, a’a dama na tuna ne da abincin da ka ce in yi da kai.”
Ya ce, “Kawo in ga irin shi ko kin iya girki.”
Ta dauko har da goran ruwa da kofi, da ya ke yasa
an kawo musu katan-katan na ruwa da lemon roba.
Ya bude shinkafar, yayi dariya. Ya ce, “Ai ni bana cin shinkafa haka tsura, ba wani dan ganye, ba wake, ba komai.
Kuma ina zan kai wannan abincin? Kin dauki kula irin ta can kasan saiti, babbar ciki, kin shake.” Yasa cokali ya dan tona, kamshinta sun hadu da warin lalacewar, ga wani kauri.
Ya ce, “Salma ai wannan ma ya lalace. Sannan kuma gashi yana kauri.” Ya dube ta, “Ba ki iya girki ba ko?” Ta ce, “Ni dai ban san irin naku ba, amma a gida ni nake yi mana.” Ya ce, “Dan kadan za ki ke dafawa, kar kiyi
la’aklari da yawan na gidanku. Fita da wannan ki
aje da safe ki zubar, kin ga kin yi ta’adi. Zubar da
abinci ba shi da kyau.”Ta ce, “Zan bar shi a bude, da safe sai in
dindima în ci, da rana ma in ci.” Ya zaro ido. “Wa
ya fada miki ana barin abin da za a ci ya kwana a bude? Ba’a fada miki ba Manzon Rahma (S.A.W) yayi mana umarni da rufe abincin mu da na sha in dare yayi sannan mu kashe fitilunmu. Ranar fa naji kina cewa ba kya iya bacci, sai a
haske.” Ta ce, “Eh.” Ya ce, “To dama kin daina,
don ba shi da fa’ida. Maida ki zo muci wannan.”
Duk da kamshin ya ishe ta amma bata jin zata ci wannan kaza ta mugunta. Ya ciro cinya ya ce, “Bude baki.” Ta tuno da zancen wannan Amarya, in da a hirar take cewa, “Har fa a baki za ki ga suna baki naman.” Cikin sauri Salma ta girgiza kai, “Na koshi, bari dai in ci dankalin nan da kwan.’
Ya tausasa murya cikin sigar lallashi, “Kin san muhimmancin kazar nan kuwa?” Gaban Salma ya sake faduwa, a ranta ta ce, “Na sani sarai, ta zalinci ce.
Ya sake maimaita tambayar. Ta ce, “A’a.” Ya ce, “Kowace Amarya ana kawo mata a daranta na farko, daran ta na alfahari, kuma dole ta ci.” Ta ce, “To in bata ci ba me zai faru?”
Ya kai bakinshi ya gutsira, sannan ya ce, “In bata ci ba Angonta zai ji haushi, kuma zata hadu da fushin Allah.” Tayi shiru, a ranta ta ce, “Kai! Ana cewa aure hutu ne, gaskiya babu wani hutu a cikinsa…
Ta dube shi. “To in ta roki mijin ya yafe mata fa kuma ta roki Allah?” Ya ce, “Za su yafe amma mijin zai rage sonta.” A ranta ta ce, “Ashe dai ina da mafita. Ya ma daina sona ba rage so ba
Ta dauki kwan ta ce, “Ni ga abin da zanci.” Ya ce, “Ke nan ba za ki ci kazar ba?” Ta ce, “Ka yafe min zan roki Allah Shima ya yafe min.” Yayi dariya, har ya kusa kwarewa.
Ta bude ruwa da sauri ta mika mishi. Sai da ya sha sannan ya ce, “Ke ba Amarya ba ce yau.” Ta ce, “In dai don wannan kazar ne naji.” Ya ce, “To sai ki fada min me yasa ki ke gudun kazar ki ta daran farko?”
Tayi shiru. Ya ce, “Ina jin ki, in ba ki fada ba zan matse bakinki in baki.” Ta ce, “An ce biya ake, ni kuma dai ba zan iya ba.” Ta tsura mishi ido taga yanda zai dauki zancen.
Yayi murmushi mai sauti, “Biya kamar ya ya?” Ta ce, “Nima dai ban sani ba, amma dai haka naji.” Ya ce, “Gurin wa?” Ta ce, “Wata Amarya ce a kauye ta ce haka.”
Ya daure fuska, “Ok! Dama kuna yin irin hirar nan mace take tona sirrin gidan mijinta?” Salma ta ce, “A’a ni ba ruwana.” fuskarshi a daure tam! Ya nunata da yatsa,
“Ko da wasa naji kin ba da labarin abin da ke tsakanina da ke, ko maganar da muka yi, sai na bata miki rai, kina ji na?” Ta ce, “Wallahi ni ina jin kunyar fadi ma.”
Ya ce, “Ci kazarki, ni ba sai kin biya ni yanzun ba, nan gaba dai kin biya ni ko?” Ta daga kai. Ya dauki wani yanki ya ce, “Bude baki to.” Ta amsa. Ya ce, “Ko ke fa! Kina ta wani boye kirji ashe ma babu komai.”
Ta rufe fuska da hannunta daya. Ya ce, “Yanzun me da me kike so a nan dakin? Kin ga sauran suna da TV da Fridge, ke ko hita din nan kina bukata.”
Ta ce”Ni dai in sona ne kawai a bar komai a sani a boko da Islamiyya.” Ya ce, “To shi kenan. Amma zan sai miki kettle na dafa ruwan zafi, don ki ke tashi da wuri kina hada min koda tea ne, kar in yi lattin gurin aiki. Kema in kin soma zuwa Makaranta kin ga za ki ke shiryawa da wuri.”
Ta ce, “To Yaya.” Ya ce, “Ba za ki daina ce min Yaya ba wai?” Ta ce, “Ni ban san to abin da zan kira ka da shi ba.” Yayi murmushi, “Shi kenan, shima na daga miki kafa zuwa nan gaba. Ki gama ci kije ki wanke baki, sai ki kwanta don ki tashi da wuri ki min abin da ya kamata, don kar in yi latti ko?”
Ta ce, “To Yaya.” Sannan hankalinta ya kwanta.
Shi ko falo ya koma yana cewa na biye miki ina da aikin yi. Ya ciro Laptop din shi ya shiga aikinshi. Tabbas Salma ta birge shi, domin tana idar da sallar Asubahi yaga ta nufi kicin ta kunna Risho, domin shi a kan doguwar kujerar yayi kwanciyarshi bayan ya gama aikinsa.
Har zai shiga ciki sai kuma yayi tunanin kada ta tsorata da shi in ta farka, bare yasa ta kashe wuta
Ta ce, da ruwan zafi zai yi wanka? Ya ce, “Ai bayin akwai na’ura mai dumama ruwa.” Ta ce, “Ita bata sani ba.” Ya ce, “Zo ki gani.” Ya nuna mata inda zata kunna ruwan ya dahu, da kuma in
da zata murda ya zo. Tayi ta al’ajabi, har ma tayi masa tambayar da ta bashi dariya, wai ba za a iya diban ruwan ba a hada shayi? Yayi dariya sosai, sannan ya ce,
“Amma ina ki ka taba ganin an sha ruwan bayi?” Itama tayi dariya, ta nuna na’urar da ake tsarki da ita, “Wai wannan to mene ne amfaninta?” Ya ce, “To kin gá dai wannan ruwan zafin shi an yi shi ne saboda in ba ka bukatar ruwan sanyi, ko kuma lokacin sanyi. Shi kuma wannan na tsarki ne, in ka gama
bayan gida ko fitsari, kin ga ba a bukatar buta.” Ta
saki dariya, “Ka san ni wanka nike yi da shi abuna?” Ya ce, “Wanka?” Ta ce, “Na zata wancan na saman na ganshi da fadi na manya ne, wannan kuma na yara, shi ne na ce ni yarinya ce.
Ta nuna jerin sabulun wankanta da ke saman kwamin wankanta, ta ce “Kaga wadancan ko? Anty Badi’atu ta jera min su, sannan ta nuna min amfaninsu.”
Ya ce, “To ban da wannan me ki ke son sani?” Ta ce, “Shi kenan.” Ya ce, “To zo ki taimaka min in yi wanka?” Ta fita da sauri tare da fadin “Sai ka fito.”
Yayi kyau cikin kananan kayan da yasa, ya ce “Ya ki ka ganni?” Lokacin da take aje masa kayan shayi. Ta sake kallonshi. “Kayi kyau Yaya, dama kai me kyau ne.
Ya dauki flaks din ya tsiyaya ruwan zafin a kofi ya ce, “Sai dai sona ne da ba kya yi ko?” Tayi dariya, “Ni ai ba zan iya sani ba.” Ya ce, “Na ce ki nemo yanda ake so da mene ne shi kanshi son amma kin ki.”
Ta ce, “Ban san ina zan nemo ba.” Ya ce, “Shima na daga miki kafa zuwa nan gaba.” Ta bude biredin sannan ta bude robar bluebond “In
shafa maka?” Ya ce, “A’a, ko kina son in yi
kato?” Cikin dariya ta ce, “Eh mana.” Ya ce, “Saboda me?” Ta ce, “Saboda bana son a ce kayi aure kuma ka rame.” hankali?” Ya ce, “Ashe wani lokaci kina da
Ta ce, “Au! Da ni Mahaukaciya ce kenan?” Ya ce, “A’a ban ce ba, sai dai ke yarinya ce, baby ce ke.” Zata yi magana ya ce, “Ke kin dinga cin wannan din ko ke ma kin yi katuwa.”
Bai lura da yana biye ma shirmen Salma, sai kawai yaga karfe bakwai ta gota. Ya ce, “Kai! Nayi latti.” Ya mike ya dauki Jakarsa, bata tashi daga inda take ba ta ce “Sai ka dawo to Yaya.”
Hannu ya daga mata ya wuce. Motarshi ya nufa kai tsaye a ranshi ya ce zai kira su a waya in ya je office.
Aliya da ke tsaye a jikin window din ta mamaki da al’ajabi ya cika ta. Me yasa yau da ya kwana a ďakin yarinyar nan ya makara? Sannan bai zo in da suke ba?
Nafi ta kalli agogonta, “Bari ya shigo taga
minti nawa ita kuma zai mata.” Tana ganin ta haka
zata iya gane wadda ya fi so cikin su uku, domin
tun a jiya ta gano matsayin waccan Mahaukaciyar yarinyar, don ita minti shidda ya dauka a gurinta.
Sai dai har karfe takwas bai shigo ba, gashi ta kasa tashi ta nemi koda abin kari, sai wani bakin ciki da taji yana yi mata tukuki a zuciya.
Amna ya soma kira don layin Aliya ya ki shiga. Ta dauka da fadin “Hello honey!” Ya ce, “My honey na makara office yau, ban shigo ba ina fatan kina lafiya?”
Ta ce, “Ina lafiya zumana.” Ya ce, “Kin ci abinci ko?” Ta ce, “Yanzun na tashi, zan sha tea ne da Indomie yau.” Ya ce, “To ki sha da yawa. Ta ce, “Jiya mun yi waya da Mom dinmu, ta ce za a kawo min mai aiki yau ko gobe.”
Ya dan yi jim, me hakan ke nufi, shi zai biya ‘yar aikin? Ta ce, “Hello kana ji na kuwa?” Ya ce, “Ina jin ki.” Ta ce “Kaga na huta.” Ya ce, “Haka ne, to sai na dawo.” Yayi shiru yana juya wayar hannunshi.
Kenan ana nufin sai ya dauki ‘yan aiki hudu ko
ko me? Ya juya ya shiga kiran layin Nafisa. A cikin dakinta ta jiyo karar wayar, ta mike tana dauka wayar tana tsinkewa, kiran ya sake
[8/18, 17:28] Ummi Tandama????: _

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button