NOVELSUncategorized

KWARATA 36

???? —— 36

           Duƙiyar ta isheni na ɗago hannuwana na rumgume kujerar da ake kira da mai zaman banza , ta kusa da Al ‘Ameen babu kowa akai dan haka na rumgumeta kawai naci gaba kuka ,


      Kallon hannuna Dikko yayi idonshi ya sauka akan wayata kawai ya miƙa hannunshi da zumar cirota daga wurina , da sauri na ƙara riƙe wayar gam tunda bana saka ma waya wasu malatsan sirri wanda saini na buɗe da kaina zata buɗe a buɗe take zaka iya shiga duk inda kake so…

      Da ƙarfinshi ya fizgi wayar kafin yayi mata kyakkyawan riƙo na fizgeta a hannunshi dan bai kamata ace anga wannan ɗaukar ba bai kamata ba , miƙo hannunshi yayi tare da kauda kanshi gefe yace bani ,

     Girgiza kaina nayi alamar a , a , cikin tausassar murya ya matso da fuskarshi kusa dani yace bani wayarki nace , matsawa nayi tare da ƙara saƙe wayar a bayana , shima matsowa yayi kusa dani yace zaki bani ko sai kinci cingom ne … ?

     Cikin kuka nace dan Allah ka shafamin lafiya , kallona yayi gefe da gefe sannan yace ta ina zan shafa miki inyi sauri dan nafi so kiyi lafiya da nisan kwana ya ƙarasa maganar yanamin kallo mai nuni da rainin hankali , nima kallon raini hankali nayi masa amma banyi magana ba ,

Shima shiru yayi bai sake magana ba kuma ya daina maganar in bashi waya , daga haka dukanmu babu wanda ya sake magana har muka zo inda zamuzo , duk sauran motocin a waje suka tsaya tamu kaɗai ce aka buɗe ma get muka shiga , bayan Al ‘ Ameen yayi parking ya fita daga cikin motar aka barni daga ni sai Dikko !

     Al ‘ Ameen na fita Dikko ya sake taro hannu in bashi waya , cikin kalar ban tausayi na maida hannuwana baya tare da cewa dan Allah kayi haƙuri , ni nace kinyimin laifi ne ? Wayarki kawai zaki bani nace ya ƙarasa maganar cikin kausasa murya yana zazzaro idanuwa , 

     Tsoro naji ya kamani sosai dan haka da sauri na miƙawa Dikko wayar , ansa yayi yana mai min ƙwafa tare tare da latso wayar haske ya bayyana , kafin ya shiga inda yake so kiran Amisty ya shigo cikin wayar , badai serving nake da sunan mutum ba lamba ce kawai , dan haka kiran sunan lambar dana ajiye number Amisty yayi sannan ya shafa wayar ya kara a kunnenshi ,

      Dafe kaina kawai nayi lokacin da Amisty ta fara watso kalamai masu zafi da ɓatanci akaina sai ta ciko bakinta da ashariya sannan ta luƙaƙamin tare da furta wallahi idonta idona sai takaini kiyama ta dawo , maganganun dai babu daɗi dan har mahaifina ta saka duka dai abun gwananin ban takaici , tana zurara zagin wayar Hafsa ta shigo , amma bai ɗauka ba saida Amisty ta sauka ta kashe wayar , har ya gama waya da Amisty kiran Hafsa daya tsinke sai ta sake kira….

     Itama Hafsa ta tata nata rashin mutunci itama a kalaman nata maganganu tayi masu kyaushi itama dai abun babu daɗin ji , idan tayi magana taji Dikko baice uhum ba , sai tace kina jina ko ? Sai yace Umm itama itace ta gaji ta kashe wayarta…

Cikin takaici Dikko ya kalleni tare da cewa fita , ina zanje ? Rumtse idanuwanshi yayi tare da sake cewa fita bana san ganin ki wallahi komai zai iya faruwa ki fita kafin naji miki ciwo , ƙaruwa hawaye na sukayi nace da Allah wai ina zanje ? Ki fita…….. Ya faɗa cikin murya maisa firgici babu shiri na buɗe mota na fito , sai yaita yin abun kamar wani shafar aljannu ,

     Ina fita Al ‘ Ameen yace muje ciki yayi gaba babu musu na bishi muka matsa , makulli yasa ya buɗe ƙofa sannan ya shiga , nima shiga nayi palo ne mai girman gaske sai wasu ƙoƙofofi biyu da bansan ko ina ne ba , makullin ya ajiyemin a saman hannun kujera yamin saida safe….

      Banyi magana ba na saki baki kamar lefen wawiya ina kallonsu suka fice daga gidan , dan daga cikin palon zuwa bakin get ba wani nisa kuma daga cikin palon kana hange duk wanda yake bakin get , wuri na samu na zauna ina maijin takaicin rashin kasancewar wayana a kusa dani ,

      A ɓangaren masu party kuwa saidai shagali yayi nisa sannan aka gane bani a wurin , nemana aka farayi amma ina mutane basu ankara ba Dikko yayi layar ɓata dani , wasa ² abu ya zama gaske yayin da wasu ke cewa sunga anmin waya na fita , nemana aka shiga yi amma babu ni kuma babu labarina….

      Dikko kuwa asibiti suka fara zuwa ya ƙara duba Sadiya da jiki yayi mata nasiha ya lallasheta , saidai tayi murmushi mai tattare da ƙuna da baƙin ciki tabi Dikko da kallo mai ban tausayi , duk da yawan murmushi ba ɗabi’arshi bane idan tayi murmushi shima sai yayi mata dan ta samu natsuwa domin shi kanshi yasan murmushin shi wani sirrintaccen sirri ne da Allah yayi masa baiwa dashi badan halinshi ba , murmushi yana ma Dikko kyau sosai kuma murmushin shi yana da ɗaukar hankali da burge duk wanda ya gani ,

      Saida Sadiya ta samu bacci Dikko yayi sallama da wanda zasu kwana da ita ya wuce gida , yana zuwa wanka yayi bayan ya fito ya saka riga da gajeran wando na jersey palo ya dawo ya zauna zuciyar shi na mishi babu daɗi , gaskiya tunda yake a shakarunshi bai taɓa cin karo da yarinya mai taurinka da rashin ji kanta cike da iskanci ba irin Sultana , a shekarunta har tasan taje ta ɗauko vidion tsiraicin uban wani ta tura ma ɗiyarshi ,

     Shi kuma Babanta shima dai anyi tsohon banza ka rasa wacce zakayi lalata da ita sai ƙawar ɗiyar daka haifa , kai abu yayi muni gaskiya , jinjina kanshi yayi shi idan shine duk su Sultana ba mata bane a wurinshi , ko iskanci zakayi da sakarci ai ka samu macen da ta cika mace ta ansa sunanta takai mace ta ko ina da ko ina mai cikakkiyar zarra ba wannan jagwalgwalon yaran ba ,

           Ya daɗe yana zaune palo yana tsaƙawa yana kuncewa wallahi zai tsaya saman ƙafafuwan shi ya cusa wa An mata soyayyarshi a zuciyarta idan ya riƙo ragamar rayuwata wato zuciya yasha da ita kuma ya gama da ita har abadan duniya , zata ga girmanshi tasan darajarshi saboda wannan kamun da yayiwa rayuwarta , 

     Wayarta ya buɗe yayi binciken duk da zaiyi bayan ya gama ya rufe wayar gaba ɗaya tare da zamewa saman kujera yaci gaba da bacci !

     A ɓangaren Babana kuma yana can gidan caca baisan wainar da ake toyawa ba a gidan , yana can ya shawu an zinatu kuma akaci gaba da caca , baya tunanin komai na ɓacin rai bare kuma halin da iyalinshi suke ciki , sabgar gabanshi ya saka a gaba kuma ita yakeyi baiji duk faɗin duniyar nan ba akwai mai iya dakatar dashi akan abinda ya saka kanshi ba….

    Gajiya nayi da tsayuwa na tunkari ƙoƙofin biyu da na gani a jere , ƙofa ɗaya a rufe take ɗaya kuma a buɗe , turawa nayi na shiga da sallama a baki na , ɗan madaidaicin palo ne da kujeru masu kyan gaske na leda , sai labulaye masu kyau da tsada wanda suka dace da kujerun , a gefe kuma ga ƙatuwar talabijin girke a tebirin ajiyarta kamar zata ɓaro ƙasa saboda girman ta , abundai zabburgewa , ciki na shiga wato ɗakin bacci babu gado sai ƙatuwar katifa da “yar ƙaramar talabijin liƙe a bango , labulayen suma irin na palo ne , toilet na leƙa sannan na fito daga ɗakin duka nayo waje inga ko ni ɗaya ce a gidan !

       Wasu irin murɗaɗin ƙattin mutane na gani marasa kyan gani yanayin duk ko wane ɗaya kamar ɗan rastilin amma su wanɗan nan baƙaƙe ne , suna gani suka yo kaina suna wata irin magana mai tada hankali wallahi saboda tsoro saida na saki fitsari a wurin , saboda wallahi siffar su bata da kyan gani abun tsoro ce abun firgici ce idan kuma sukayi magana sai kaji kamar ba duniya kake ba , tsaye nayi wurin saboda tsoro na kasa gaba na kasa baya , ruɗewa tasa na manta da ina da ƙafafuwa …

       Tunzura babbansu yayi yanayin shi ya nuna yana cikin ɓacin rai dan haka yayi wani irin kuka mai motsa tunani ya ƙara takowa dan ya samu damar matsowa kusa dani , nidai bansan ya akayi na ruga ba saidai kawai na ganni saman katifa har na lulluɓe da bargo ina kuka ! Bansan lokacin da bacci ya ɗaukeni ba ,

      Da safe Dikko daga masallaci asibiti suka nufa daga shi sai Al ‘ Ameen , har yaje ya dawo Sadiya bacci takeyi , bayan ya dawo gida ne ya kira danjin ita kuma An mata ko ta kwana lafiya , lafiyanta qalau suka faɗa tare da bashi labarin abinda ya faru , mugu yaji mugunta , dariya Dikko yayi sosai tare da cewa zaizo anjima ai ,

     Ba’a mugun sarki sai mugun bafade , Al ‘ Ameen bayan Dikko ya gama waya yace mai gida dan girman Allah ka kyale yarinyar nan tayi tafiyarta , sai kace dai itace kaɗai mace a duniya ? Yarinya mara kunya mara tarbiyya mara ɗa’a masu gajeren asali wallahi mutuncin gidanku da nasabarku da kai kanka taka mutuntakar ta wuce ace kana sauraren yarinyar nan wallahi , kana da zarrar da duk macen data ganka duniya sai tayi addu’a ta sameka a matsayin abokin rayuwarta.

     Kana babban asali ga cikar zati ga kyau ga kwarjini me zakayi da yarinya mara tarbiyar ? A hankali Dikko ya lumshe idanuwanshi dan duk duniya idan akwai kalma mafi muni da ɗaci a wurin shi bata wuce ace An mata bata da tarbiyya ba , Al ‘ Ameen yaci gaba da cewa uwa uba kuɗi kana da cikar arziƙin da zaka iya auro mace ko wace iri ce kai ko babu kuɗin sai ta so ka dan kyan ka , abin kunya daci baya ne ka auri ɗiyar ɗan caca mashayin giya manemin mat….

    Hannu Dikko ya ɗaga alamar dakatar dashi , shiru yayi bayan yayi shiru yayi masa nuni da ya fita kawai , Allah ya baka haƙuri mai gida ya faɗa cikin girmamawa sannan yabar ɗakin ,

     Fitar Al ‘ Ameen Dikko ya fara nazarin maganganun shi tabbas duk abinda ya faɗa ba ƙarya bane ba , ko wane mai asali yana so ya auro mai asali gidan tarbiyar da mutunci amma miye aibun An mata ? Duk dai haɗa jini da mutane banza bashi da wani amfani dan ba’a gane matsalar hakan sai zuri’a sunzo dan iskanci jini yake bi , tou amma mi yasa ita An mata batajin magana ne ? Wani sashe na zuciyarshi yace ba komai wata rana zata daina , idan har mace tana shakkun namiji idan dai ya shata mata doka tou fa tabbas ba zata karyata ba , wani sashe kuma cewa yayi matsalar ba’a nan take ba , tsoki Dikko yayi tare da cewa da Allah ku barni…

      A ɓangare na kuma , da asuba ina farkawa kayan jikina na cire na wanke su saboda na ɓatasu da fitsari na goge katifar dake da leda a jikinta kila ma sabuwa ce , labule ɗaya na ciro na ɗaura , bayan na gama wanke kayan a palo na shanya saman kujera na kunna fanka , ɗaki na koma na shiga nayi wanka tare da ɗauro alwalla , bayan na fito na sake ciro wani labilen na rufa dashi naci gaba da sallah…. ????

     Bayan na gama na koma na kwanta , ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni , dan banda wata damuwa saidai kaiwai ina so in tafi gida ,

     Ina bacci Dikko yazo kuma tun a palo na fara jin faɗashi wai waye yace kujera wurin shanya ne ? Da sauri na tashi na ɗauki bargo na ƙara lullube jikina a dai² lokacin da naji Dikko yace maza cire wannan tsumman kaje ka jefar dashi a waje , kutumelesi ? ???? rigata mai tsada itace za,a yadar ? Amma dai wallahi Dikko ɗan iska ne , kuɗi fa masu yawan gaske Alajina ya siyamin ita shine zaisa a yado ta ,

      Ina cikin kuka naji ƙarar takalminshi yana tahowa ɗakin da nake , ci gaba nayi da kuka ko zai tausayamin yasa a dawo min da rigata , kwance nake cikin bargo fuskata kaɗaice a waje ina kuka , ƙamshin turarenshi ya ƙara matsowa kusa dani haka ya tabbatarmin yana gab dani dan haka na buɗe idona ina kallonshi ,

      Murmushi yayi cikin natsuwa sannan ya fara magana cikin kamun kai da aji , gaba ɗaya jiya da daddare tunaninki nai tayi , da sauri nace me ? Murmushi ya sakeyi sannan yaci gaba da cewa tunanin da nayi tayi cikin dare shine nayi kuskure , sam bai kamata ace na ɗaga hannu na mari mace ba , kiyi haƙuri don Allah idan ma baki gamsu ba zaki iya rama marikin kamar yadda na mareki , ƙoƙarin tashi na farayi dan rama marina , cikin magana mai kama da raɗa yaɗan fiddo kyawawan idanuwanshi yace a haba keko ba’a nan ba kinsan babu kaya a jikinki koma kawai ki kwanta ,

     Babu gardama na haƙura na koma na kwanta , fita yayi bai daɗe ba ya shigo da wani haɗaɗɗen kwando ya ajiye a can gefe cikin magana mai laushi da kalamai masu burgewa yace kiyi kalaci ya faɗi maganar tare da nunamin inda kwandon yake , zai fita nace am da Allah idan babu damuwa rigar nan kada a yadar da ita anjima idan zan tafi ita zan saka ,

      Ba tare daya kalleni ba yace bama buƙatar ita rigar kayanki yanzu zansa a shigo miki dasu palo , wai ance jibi hutun ku zai ƙare idan zan wuce zan ajiyeki makaranta , kallo ni yayi tare daci gaba da cewa kyakkyawar fuska da kyawawan idanuwa irin naki gararin gari ba nasu bane da ilimi suka dace bada taron murnar zagayowar shekarar aihuwarki ba , yana faɗin haka yayi gaba abinshi , ni kuma nace wallahi aiko babu sakaran da ya isa yakaini makaranta tunda ba cewa nayi ina so ba , dawowa yayi tare da cewa kina magana ne ? Banza nayi dashi naci gaba da hararar ƙasa ,

     Murmushi yayi da gefen bakinshi ya fita , yana fita na ƙara cewa kuma ko ka kaini saina dawo dan kaga na kwana nan gidan nan ko an faɗa maka ni ina tsoron waɗanda ka ajiye ne ? Sake dawowa yayi yace kina so ki madani kamar wani sa’ar wasanki ko ? Tou idan kinje makarantar ki gudo mu gani , Dikko ya kaiki saboda haka Dikko zaici gaba da ɗauko ki , ke ɗaya na bayar kuma ke ɗaya za’a bani a ko wane hutu , kuma ko hutu akayi idan ba nine naje ba ko waye wallahi yarinya bazaki dawo gida ba gara ma ki fara kamun ƙafa tun yanzu ko zan riƙa ziyartarki lokaci ² idan kuma kika nunamin yarinta sai ina barki kisha baƙar wahala babu abinci babu kuɗin kashewa , yana faɗin haka ya fice abunshi ,

Ni kuma ƙasa² nace sai inyi ta iskanci da malam su sa fiddoni , in dawo gida , kuɗinkan banza kuɗinkan wofi ko an faɗa maka ni matsiyaciya ce ? Hahaha niko nace da kanki ma zaki riƙa cewa ya baki bari dai kisha azaba yarinya ….

      A palon ɗaki na Dikko yasa aka ajiyemin kayana saman kujera , shi kuma yayi tafiyarshi , saida naji fitar motarshi na tashi naje na ɗauko kayan na saka ina sakawa ina mita ni za’a bawa kwance kila ma kayan matarshi ne ya ɗibomin , kona ƙannenshi , niko nace kedai kika sani…

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button