NOVELSUncategorized

EL BASHEER 11-15

*EL-BASHEER* 

11-15


Da saurin sa yyi parking a gidan sbd wani aiki daya rikeshi yau sam ya sha’afa be kawo masa food ba, dukda dare yyi kusan 9pm yanzu bayajin zai
kyaleshi tunda yasan idan be bashi ba bazaici komi ba Suraj kenan yyi hanyar part din frnd din nasa, kamar yadda yasan zai gani haka yaga parlon komai ya koma upside down aje ledar hanunsa yyi ya fara gyara wajen dama babu me gyarawa idan bashi ne yazo ba, cike da tausayi ya isa cikin dakinsa dake sama, be samesa a dakin ba amma yaji karar zubar ruwa a toilet hakan yasa ya fahimci inda yake, zama yyi yana jiran fitowar sa, ba’a jima ba kuwa ya fito, El-bash yana ganin suraj ya saki murmushi wow ashe haka murmushi ke masa kyau? Har wasu dimples gareshi suna lotsawa ya salam!  Abin dai so Masha Allah, fararen hakoran sa kuwa har wani sheki suke sai kace ba mahaukaci ba, suraj ya mike yana masa alama da hannu yace, 

“ka sameni a kasa.” 

 girgiza kai kawai el-bash yyi batare da yace komai ba.


Kayan bccinsa yasa bayan ya mulke jikinsa da cream hade da turare me dadin kamshi, kai lamarin el-bash akwai abin mmki idan yyi wani abun kamar me lpy wani lkcin kuwa idan ya birkice sai a hankali. Sakkowa yyi kasa nan ya tarar da suraj na jiransa, Suraj ya jawo plate daya dakko a kitchen yana bude ledar dayazo da ita yace, 

“Srry na barka da yunwa ba lefi na bane kaji” 

yyi mgnr yana kallon sa da murmushi, el-bash dai sai murmushin yake shima duk lkcin daya kasance da suraj baida aiki sai murmushi kamar wanda akayi masa bushara da gidan Aljanna, Suraj kuma tausayin frnd din nasa yake sosai dukda baya amsa masa hakan bazai hana yyi hira dashi ba shima yanajin dadin kasancewa dashi aminai ne na amana matuka, suraj ya tura masa plate din yace,

 “bismillah muci,”

nan el-bash ya sake yin murmushi shima yasa hannunsa, nan suka fara cin abincin tare batare da sunce komai ba, can suraj ya sake kallon el-bash yace,

 “frnd gsky muna mssn dinka a wajen aiki munyi rashin babban gwarzon jami’i,” 

el-bash da ba ganewa yake ba ya sake yin murmushi, suraj duk jikinsa yyi sanyi sam bayason ganin frnd dinsa cikin wannan halin, to amma ya zasuyi? Haka Allah ya tsara, shima suraj din murmushin yake yyi sbd gaba1 tausayi ya lullube masa zuciya ya nisa kadan yace, 

“Allah dai ya kawo mana karshen wannan abin Insha Allahu kaine bisa kansu frnd muna tayaka Addu’ah sosai”

 yyi mgnr yana kama hannun el-bash ya hada da nasa ya dunkule yana girgiza kansa hade da murmushi, el-bash shima yyi kamar yadda yaga yyi wato ya girgiza kai yana murmushi. Kwashe komi suraj yyi ya mayar kitchen dake plate 1 ne nan ya wanke ya maida inda ya dakko dama ya saba yin hakan, dawowa parlo yyi nan ya samu el-bash ya koma kan kujera ya zauna, suraj ya zauna shima hade da kunna kayan kallo ya kamo tashar kwallo kusan 30mins lkcin 10pm yyi suraj ya kashe komi ya dafa el-bash yace,

 “frnd am going,”

el-bash ya danyin murmushi kawai, suraj shima murmushin yyi yace, 

“ok gudnyt, take care ok?”

 El-bash ya sake sakin murmushi, Suraj ya juya kansa gefe yana kokarin maida kwallar da take shirin zubo masa ace mutum har mutum baida damar walwala? Kai duniya ana abubuwa a cikin ta, kallonsa ya dawo kan el-bash ya danyi masa murmushi yana me daga masa hannu, binsa da kallo el-bash yyi harya bacewa ganin sa.

 Lumshe ido yyi yana me sake gyara kwanciyar sa. Suraj yana fitowa yaga alamar an wulga da sauri kamar inuwar wani abu, kunna wayarsa yyi ya haska wajen yaga bega komi ba, dan girgiza kai yyi yana cije lips yace,
 _yeah i know, but it’s just the matter of time._  Nan yyi wucewar sa gun motar sa yabar gidan.****

 Wanke2 take a hankali tana share kwallar da take zubo mata, ji tayi an kira sunanta “ummiii…” Da karfi, tasan me kiran dan babu me mata hakan sai ‘yar uwarta jamila, juyowa tayi tana me kokarin maida kwallar data sake tarar mata tace, 

“na’am.” 

 jamila tana daga can bakin kofa zaune tace,

 “idan kin gama ga wanki na can kiyi min kinsan abinka da amarya sai ana harhada kaya za’a bar gida” 

tayi mgnr tana dariya, yaken dole tayi tace “toh,” wata mata ce ta shigo gidan gyalenta a kai tana fadin gafaran kudai, jamila tace, “oyoyo inna ta har kin dawo? Allah sa an dace,”  inna na kokarin zama kan takalman ta tace, “kedai bari dakyar hamisu me kujeru ya bani akan zan ciko masa kudin,”


 jamila tace, 

 “kai hamisu akwai son kudi amma ina shiga gidan haruna komai zai wuce,” 

 inna tana washe baki tace, 

 “kwarai kuwa ai kin cafki dami a akala wlh yaron arziki” 

 jamila tace, 

“kuma inna karkiso kiga motar sa be dade da siya ba wani dan siyasa ya bashi kinsan shima siyasa yake,” 

inna tace,

 “ke don Allah?” 

 Jamila tace,  “wlh ai inna kin kusa zuwa hajji dan ina tunanin ya kusa zama gwamna,” inna na sake washe baki tace, “ai kuwa bashi yanzu na fara ci tunda na kusa zama surukar gwamna,” nan suka kwashe da dariya.

 Ummi na jinsu zuciyar ta na zafi saidai babu yadda ta iya dan babu me share mata kuka yanzu tasan ta kara shiga maraici sbd rashin iyayenta da kuma kakarta me sonta.****

*WACECE UMMI?* 


Asma’u Ahmad shine cikakken sunan ta, suna zama anan kano unguwa uku iyayenta sun rasu tun batafi shekara 10 ba sanadin gobara daya kamasu cikin dare lkcin ummi nagun kakarta a garko, wannan rasuwa ta girgiza mutane da dama, domin mlm Amadu malami ne me tsoron Allah dan tuni ma ummi er shekara 10 tayi saukar karatun ta, nan wata islamiyya yake koyar wa, Kakar ummi ta shiga tashin hankali matuka dan tana son danta Amadu dukda yana dan fari, saidai yafi kaninsa Sabo kirki, mlm Sabo baida kirki sam ga son abin duniya sosai yake rufe masa ido, lkcin suma suna garko saidai gadi  yake a kano gidan Alhji Usman Tafida, dake daki daya ne gobarar ta shafa sai sabo ya roki Alfarmar a bashi aron gidan kar a siyar kamar yadda akayi niyya zai rike ummi dake itama kakar ummi ciwo ya kama ta sbd shiga rudu da tashin hankali ga kuma tsufa, hakan kuwa akayi duk suka tattaro suka dawo kano da zama tare da ummi, shima yana da ‘yarsa kwaya daya me suna jamila ta girmi ummi da shekara biyu.

Ummi tana da siffar ta na hallita Masha Allah, sabanin jamila da ita baka ce gata nan dai daidai gwargwado Masha Allah. Tunda suka tasa sai ya zamana samari na tururuwan zuwa gun ummi, amman dake bata wani damu ba sai bata kula su, wani matashi dake can bayan layin su anace dashi Haruna, shi ya nacewa ummi har itama ta fara sonsa, tiryan-tiryan suka fara soyayya gwanin sha’awa har yana zance zai turo iyayen sa, ummi da wahalar gidan ta isheta dama tun da suka gama secondary babu damar yin gaba yasa tace zata fada a gida, ummi bata sani ba ashe jamila itama na matukar son Haruna kuma ba komi take hange ba sai dan kudin sa sbd ba lefi yanada rufin asiri, lkcin da ummi tayi mgnr zai turo jamila ta girgiza dan ba haka taso ba, caraf tayi dake tana wajen karma su inna su yarda tace sai ki bari ai a binciki waye shi kafin ya turo iyayen sa, ummi batare da damuwa ba tace toh. 

Bayan tabar wajen jamila ta zuga inna tana bayyana mata irin arzikin da zasu samu idan ta auri haruna, inna da son kudi tahau kai ta zauna, kawu sabo na zuwa ta gaya masa shima yace ai dole d jamila ya dace dan itace babba dole ta fara aure kafin karama, ummi duk batasan me ake ciki ba sai kulli suke mata, ranar Alhamis da la’asar yazo kamar yadda ya saba yasa yaro a kira jamila, jamila na zaune taji ana sallama da ita, nan ta zari mayafi ta fita tana ganin haruna ne ta washe baki cike  d farinciki, Daidai lkcin ummi tazo wucewa tayi mmkin ganin haruna tsaye da jamila sbd yadda yake nuna rashin son tarbiyar ta, da murmushi saman fuskar ta ta karasa wajen tace a’a yaya jamila ashe kinzo ku gaisa yau dai da alama za’ayi ruwa da kankara,

 jamila ta watsa mata wani kallo tace ke dakata ya ina hira da masoyi na kice nazo mu gaisa? Wannan wacce irin tmby ce? Baki galala ummi ta saki tana kallon ta ta maida kallonta kan haruna taga yana kada keys din hannunsa hankalin sa bama a kanta yake ba, 

Innalillahi wa’inna ilaihin raji’un ummi ta furta tana me kara karasowa wajen haruna tace ka dubi girman Allah ka gayamin meke faruwa wani abin nayi? Haruna ya dago yana binta da wani matsiyacin kallo yace dan Allah malama kija tsummman jikin ki kibar nan wajen duk kin cika mana waje da warin jaba ya karasa mgnr yana me toshe hancin sa, 

Hhhhh jamila ta kwashe da dariya tace toh ke kinji warin jaba kike dan haka kibar mana waje kar kisa masoyina ya suma dan warin ki, ummi ta bisu da kallo wasu zafafan hawaye na neman sakko mata sai yanzu ta fahimci komai wato an rabata da haruna? Gudun kar hawayen ya zuba gabansu ta juya da sauri tabar wajen tana me matse kwalla, haruna da take gani taji dadi dan shine kadai masoyin ta a yanzu shima an rabata dashi wannan wacce irin rayuwa ce? 


Tana kallo aka kawo kayan jamila, jamila sai iyayi take ana buga qirji za’a auri dan siyasa, yyinda ta bangare guda sun matsa mata akan ta fito da wani ko kuma a bata duk wanda suka so, sosai hankalin ta ya tashi tana fatan Allah ya hadata da nagari kawai dan yanzu kam ta kulle zuciyar ta babu zancen soyayya kuma.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button