FARHATAL-QALB
FARHATAL-QALB 12
“To dika dika daga karshe dai tamkar yadda muka fada a baya. Nan gidan bakuda history na sickle cells sai dai mahaifi da mahaifiya wato Hadiza ta kasance AS, hakama shi mai gidan nan shima AS ne ta haka suka samu yara biyu SS sai guda daya AS. Na farko SS ta biyu AS career na uku SS . Sai bangaren abokiyar zamanta ita AA ce agwajin da mukayi. Don haka yaranta akwai AA da kuma AS amma babu SS aciki … Wannan shine kawowar karshen bayani na. Ubangiji Allah ya ba wa marasa lapia lapia. Masu lapiar kuma Allah ya kara mana mai albarka , Aamin…”
“Uhm. Kyaji da shi ” Marka ta miqe tana Kade zaninta tayi dakinta da sauri …