FARHATAL-QALB 19
PG:19_
×××
Sannu ahankali, Kwanakin mu nata ja, Ya yinda awanni da mintuna suke shudewa. Kwanakin Umma Hadiza da fara aiki bakwai cif. Sati daya kenan
Hakan kuma yayi dai dai da kammalawar karashen aji na daya na babban sakandiren su Waheedah.
Lamarin sai godiyar ubangiji. Don zance na gaskiya Allah ya kara saukakawa Umma Hadiza da ahalinta. Ci da shan su acan acan. Don na safe kawai suke saya su ci. Na rana da wanda zasu ci da daddare Umma Hadizan na tahowa dashi daga gidan aikin na ta.
=========. ===========.
Tunda ta tashi da safe bayan ta gama zuba ruwan, Dauraye kwanuka tayi ta kife hade da kunna turaren wuta na tsinke.
Daki ta koma. Umman su na kwance . Idanunta sun kada sunyi jazir. Ya yinda jikinta ya dau zafi sosai.
Waheedan ta taba jikinta tana rausayar da kai. Cikin rawar murya tace,
“Umma .. Jikin ki zafi.”
“Waheedah ya akai?. Bari na tashi .”
“Umma baki da lapia. Muje kyamis”
“Lapia ta lau Waheedah.” Ta fada cikin dauriya.
Nan da nan hawaye suka shiga reto a kyakkyawar fuskar waheedan.
“Umma Allah ya baki lapia. Wayyo Allah na Umma.”
Umma Hadiza taja siririn tsaki. Cikin kufulewa ta dubi Waheedah
“Allah zan make ki idan kika sake mun kuka. Shikenan ni ba dan adam bace kamar kowa da ba zanyi rashin lapia ba? Haba Waheedah.”
“Ummah kiyi hakuri “
“Yauwa, Kin leqa dakin su Yayan na ku?”
“Eh ya koma bacci shi “
“Toh. Ki duba kasan samirar can akwai dari biyu ki sayo kosai ga ragowar biredin jiya nan sai ku hada ku ci. “
“Umma ke fa?”
“Je ki ki sayo ke dai”
“Tah “
Bata sake cewa komai ba, Ta miqe ta dauki kudin bayan ta zura hijabin ta.
Tana tafe tana tunanin halin da ta baro mahaifiyar tasu aciki. Ta sayo kosan ta dawo gidah.
“Umma gashi “
“Toh. Dibi naki ki kai musu”
“Umma ke fa?”
“Wai Waheedah menene haka iyye? Ina magana kina yi. Zaki tashi ko sai na bar miki wajen?”
“Kiyi hakuri Umma.”
Da sauri ta dibi nata jikinta na bari. Ta gutsiri biredin ta mayar musu nasu
Ta tashi ta kai dakin su Najib. Bayan ta kwankwasa yar kofar kafin ta shiga.
“Umma na kai musu “
“Madalla ” cewar Umma Hadiza. Ta miqe dakyar tana gyara zaman hijabin jikinta.
Tun dazu take son tatafi gidan aikinta . Amman data yunkura zata tashi sai jiri ya debeta.
Tanata daurewa dai. Har ta tsaya a tsaye. Waheedan nata kallonta cike da tausayawa.
Har ta kai kofa jikake luuuuuu! Wani jirin ya sake dibanta. Sai dabas tayi zaman dabaro a kofar dakin. Ya yinda kanta ya bugu da kofar dakin.
“Wayyo sannu Umma.” Waheedah tayi kanta da sauri cike da tausayawa
“Umma sannu “
“Uhum.”
“Ina ne yake maki ciwo Umma?”
“Ba ko’ina Waheedah.”
“Umma gashi kin fadi “
Umma Hadiza bata sake ce mata komai ba. Ta miqe zata tashi nanma ta sake zubewa a kàsa
Da sauri waheedan ta nufi wajen Yayan su Kamal.
“Yaya” tace da shi
Ya tsaya yana sauraron me zata ce? Hannun sa dauke da biredi da kosai yana ci ,
“Umma ce Yaya.”
“Meya faru da ita?”
“Batada lapia. Tanata faduwa da ta miqe “
Bai sake cewa komai ba. Bai kuma tsaya ta karasa fada ba. Ya miqe dukkuwa da shi dinma jikin sa babu kwari.
A bakin kofar dakin ya hangi Umman tasu tanata kokarin tashi. Har tayi amai awajen dan kadan sai nishi take
“Ummah.. SubhanAllah! Ashe baki da lapia?”
Ta dan juyar da kanta gefe kawai. So take ta miqe ta kasa
“Waheedah gyara wajen bara na sako riga mu tafi asibiti “
“Babu inda zanje Yayan su. Lapia ta lau “
“Ummah bakida lapia. Maybe zazzabin malaria dinnan ne da aketa yi wallahi. Kiyi hakuri “
Umma Hadiza ta sake miqewa cikin dauriya wai ita gidan aikinta zata je. Tana tafiya tana kama bango.
Marka dake kofar dakinta tana kallon su ta tabe baki kawai.
Cikin haka sai ga malam Nalado ya shiga gidan yana wakar garaya.
Yaja yai turus ganin su baki daya a tsakar gidan
“Menene haka. ? “
“Umma ce batada lapia Baba.”
“Zo nan mai sunan malam. Ni na aika na iro ya kira mun kai.” Cewar Marka cikin muryar isa da gadara.
“Umma batada lapia Baba.”
“Meye garungamun sa da ita? Iyye? Ni fa Malam nagaji da saye sayen da kukeyi.” Cewar Inna Sa’adatu data fito daga cikin dakinta. Daman tun dazun tana leken su ta wundo.
“Najib zo ka rakani mu kira Nase me kyamis.” Cewar Kamal. Ya fice dan tsabar kidimewa jikin sa ko riga babu sai dogon wando. Yayinda Najib ke binsa a baya yanata sauri shima.
Jikin su baki daya yayi laasar ganin yadda mahaifiyar tasu ke tsiyaya amai.
Marka ta ja kwafa tana girgiza kafafu.
“Wannan amai dai a bincike sa , Ahto “
Malam Nalado yayi mata alamar da tayi shiru. Fuskar sa da alamun rashin jin dadin kalaman mahaifiyar tasa.
Umma hadiza na jin su. Ta kasa cewa komai. Baki daya amai ne ke kwarara tamkar zata amayar da kayan cikinta saboda azaba harda kakkari.
“Sannu Umma…”
Kada kai kawai take. Ta kasaa amsa waheedan
Cikin haka sai ga Najan Isubu ta zo ta da sauri. Mayafinta ko gama yafuwa baiyi ba.
Ta shiga gidan cikin kidimewa . Da sauri tayo kan Hadizan tana sallallami
“Sannu Hadiza. Yanzu su Kamal ke gayamun ….”
“Gayyar Munafukai… ” cewar Marka.
“Debo kasa a waje Waheedah ki sauri “
Nan da nan Waheedah ta fita ta ebo kasar ta kawo. Najan ta zuba awajen da Hadiza ke aman. Tanata doka mata sannu.
“Ni fa nagaji da nuniyar isar da ake a gidan nan mai sunan Malam.”
“Marka kiyi hakuri.”
“Sai yaushe ne Hadiza zata bar gidan nan?”
Da sauri Najan ta juya tana kallon Marka. Hakama Umma Hadiza da Malam Na lado.
Waheedah baki daya sai kanta ya kulle sahoda meyasa Umman su zata bar gidan akan me? Bayan ga Inna Sa’adatu nan da yaranta
“Shekara nawa kenan kuna rokana da rufa rufar zancen nan? Nagaji. Nace nagaji. An kai ni makura. Ai yaranta sun girma ba jinjiraye bane. Ko yanzu aka aurar da Wahidin zata haihu. Don haka maganar a boye zance haka nan ya isa.”
“Marka d…”
“Ya isheki Naja”
“Shekara nawa Hadiza zata dauka tana zaman yaranta… Bayan tun tuni auren su da mai sunan Malam ya kare? Iyye? Nace sai yaushe zata tashi ta bar mana gidah?……..
❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????❤????