FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 20

PG:20

======

“Haba Marka…. Menene haka fisabilillahi?”Najan Isubu ta fada cikin tsantsar takaicin Markan.

“Yo ai gaskia ne. Hakurina ya kare . Sai yaushe ne Hadiza zata bar gidan nan.?”

“Marka wai meyasa kike mantawa da igiyar aure baa hannun ki take ba? Menene riba shiga tsakanin su da kike yi? Idan ya shikata na menene tana zaman yayanta za ki takura sai ta tafi?”

“Saboda bana raayin zamanta anan din.”

“To ki rabu da ita mana tunda ba akan ki take ba .”

“Kinga Najaatu tun muna sheda juna ki bar shiga hancina ki kudundune. Ina tsoron ranar da zan samu Isubu na sanar masa duk tsegemun da kike yi. … “

“Yo Marka idan kin gaya masa ma ai ba wani muguntar nake ba. Na menene don ina aminta da surukar ki zaki dasamun qusar tsana? … Me Hadiza ta miki? Tun ranar da aka kawo Hadiza a matsayin matar Malam kika tsaneta. Saboda me? “

“Saboda Tsayyabu uban Dan Ali….(mahaifin Najan) idan kin gano su wanene to saboda su na tsaneta. Akeken banza da wofi, Afiruwa. Ke ba tsaran maida magana ta bace. Kinyi kadan ” Marka ta karasa fada tana nuni da yatsanta a fuskar Najan Isubu tamkar zata tsone mata idanu.

Waheedah ta kasa magana. Ta kasa zama Kuma . Tana tsaye tamkar sanda. Gaba daya duk wata laka ta jikinta ta mutu. Sam ta kasa gane inda maganar su ta dosa .

“Umman su da Babansu auren su ya rabu tun shekarun baya? Kai gaskia bata yadda ba. Ta shiga girgiza kai ita daya. Tana yin baya da baya …saura kadan ta doka kanta a bango Najan Isubu ta riqota da sauri

“Menene haka Waheedah.?”

“Dan Allah dagaske ne? Dagaske ne auren Umma ya rabu? Dagaske ba aure?” Ta shiga tambayar Najan Isubu. Muryar ta cikin kidima da tsantsar tashin hankali.

“Kinyi wanka kinci abinci?” Tambayar da Najan ta mata kenan.

“Eh.”

“Toh zura hijabin ki. Kije gidan aikin mahaifiyar ku. Ki sanar musu batada lapia ne. Duk aikin da takeyi su gaya miki kiyi. Kafin Allah ya tashi kafadunta kinji ko?”

“Ai t….”

“Bar musu Waheedah. Jeki kawai “

“Bansan inane bangaren ba Aunty “

“Inde kin shiga gidan ki tanbayi sashen da Umman ke aiki. Kingane? Shine na fari kafin dayan sashen.”

“Tohm “

Bata sake cewa komai ba. Ta shiga dakin ta dakko hijabinta. Dan turaren ruwanta da Yayan su ya bata ta dakko ta dan diga a tafun hannunta ta shafe jikinta da shi. Ta zura hijabin gabanta na tsananta bugawa

Sai waiwayon Umman su dake durkushe tana numfarfashi take. Najan Isubu ta daga mata hannu ta nai mata alamar da ta tafi kawai.

Waheedah ta fice daga gidan . A kwanar layin gidan ta ci karo da su Kamal . Suna ganinta dukkan su su biyun suka shiga tambayar abun da ke damunta ? Ganin yadda hawaye daya na bin daya ke kwarara a idanunta.

Musanman da suka bar mahaifiyar tasu a gidah cikin matsanancin hali na rashin lapia.

“Menene wai Waheedah .. Umma ce? Wani abun ya sake faruwa da ita?”

Cikin sake fashewa da wani sabon kukan. Hadi da kifa kanta a jikin bango tace,

“Marka tace lalle Umma tabar gida.”

“What nonsense….!!! Akan wane dalili?” Kamal ya tambaya cikin zafin rai.

“Wai ba aure a tsakanin su da ….”

“Bangane ba aure ba. Wannan wane irin rayuwa ce?. A yanzu ta sa ya saki Umman kenan? Kuma dan tsabar renin hankali a ….”

“Wai yaya sun dade da rabuwa …”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!! ” Kamal ya shiga maimaitawa.

“Yaya kai ma baka sani ba da ma?”

“Bansan komai akai ba Waheedah… Yanzu ina Umman?”

“Tana can tana amai… Aunty Naja na temaka mata.”

“Yanzu me kyamis din zai karaso .. Ina zaki?”

“Gidan aikin Umma …”

“Yauwa gwara kije kar su jita shiru. Ki kuma share kukan nan haka. Nasan koma menene sharri ne na tuggun Marka. Duk ma menene itace kan gaba akan ganin ya wakana. Amman ba komai, Ai Allah ba azzalumin sarki bane. Zai ma Umma sakayya nan kusa da yardar Allah “

“Insha Allah…. Je ki “

Tafiya tayi tana waiwayon su. Kamal ya samu gefe ya tsugunna. Yayinda Najib ke a tsaye ya tokare bayansa da kafar sa daya. Kansa a sama yana tunani. Daman tun sanda Yayyun nasa suka fara magana. Zuciyar sa ke kai kawo akan zancen.

Cikin haka mai kyamis din ya zo ya same su. Daman ca yayi suyi gaba kafin ya tattara komai ya cinmasu

Najib ya yi masa iso cikin gidah. Dakyar Marka tayi shiru tana yada zance. Har mai kyamis din ya shiga yana yan gwaje gwajen sa da tanbayoyin sa akan Umma Hadiza da saboda aman data jera lokaci tanayi baki daya ta rame. Manyan idanunta sun kara firfitowa waje tubarkAllah.

×××NEW GRA SHURAH×××

Waheedah na tafe iska mai sanyayawa na kadata. Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa baka mai zanen kujera ja

Sai hijabin dake jikinta shi ma ja ne daya amshi kwalliyar jikin atamfar ja
Kai dakaga yanayin yadda kayan suka zauna a jikinta zaka rantse gugar iron ce.

Nan kuwa kayan ma ninkin guga ta musu. Ko’ina na jikinta tsaf tsaf hatta takalmin da ke dogayen sahunta na samfarin dan madina.

Sanyayyen turaren jikinta mai dadi bame hawa kai ba nata gauraye ilahirin jikin ta.

Gabanta na tsananta bugawa. Haka ta shiga tafiya a unguwar da Umman tasu ke aiki.

Karar karnuka da tsuntsaye sai tashi suke. Haka dai Waheedah ta daure ta karasa har ya zuwa kofar gidan na The Adams family!!

Daya daga cikin masu gadin yana ganinta ya tashi yana nufar inda take

“Ina kwana?” Ta gayshe shi kanta a kàsa.

“Lapia lau…wajen wa kika zo? Ko masu kawo goron nanne na sayarwa? Na shekaran jia ko?”

“A’ah bani ba ce …” Ta amsa shi cikin sanyayyar muryar ta

Dai dai lokacin da wasu manyan motoci masu nishi da kyawu suka danno kansu zuwa gingimemen gidan na the Adams family.

Nan da nan masu gadin suka bude musu gate. Jufa jufan su 3 suka kutsa kai cikin gidan.

Waheedah ta zubawa sarautar Allah idanu tana bin yadda motocin suka tulesu da kura da kallo.

“Yauwa ke menene ne? Sauri muke munada baki?” Mai gadin dazu da suka rufe gate ya cigaba da tanbayarta. Don tambayar farko daya mata bata kaiga sake bashi amsa ba baqin suka zo. Yabar inda take zuwa wajen baqin

“Sunana Waheedah. Nazo nan gidan ne taya su aiki.”

“Akan me zaki tayasu aiki. Ko irin masu barar nan ce ke! ? Malama yi gaba. Ga ki komi fes fes kankanuwar yarinyar ki da ke saboda mutuwar zuciya shine kikazo nan din maula ko? Zaki matsa ko sai na mauje keyar ki?”

Waheedah ta girgiza kai kawai

“Mahaifiyata ce ke aiki anan gidan. To yau bata d….”

“Kyaleta Labaran..Ke yar Umma Hadiza ce?”

“Eh ..” waheedan ta amsawa wata kyakkyawar budurwa data fito waje.

“Okay shigo ciki. ….” Nadra na gama fada ta karasa shiga ciki. Daman mahaifiyar ta Dr. Hameedah ce tace tazo ta ko Hadiza tazo masu gadi sun hana ta saboda baqin da zaayi. Ta shigar da ita

“Kema baki bayani ba ” cewar me gadin daya hana Waheedah shiga ciki

Bata kula shi ha. Tabi bayan Nadra da sauri. Wayar Nadra ce ta shiga karaa. Da sauri ta dauka ta kara a kunnenta.

“Bata zo ba. Amma dai luckily enough na samu daughter din ta. Har ma mun shigo tare ..”

Waheedah nata kalle kalle haka suka karasa shiga cikin gidan. Waheedah ta dade nutsuwar ta bata dawowa ba. Saboda madaukakiyar mamakin girman gidan da abunda ya qunsa…

“Nadssss .”

“Sis Ahlaaam…..”

Nadra da wadda ta kira Ahlaam suka rungume juna cikin farin ciki. Waheedah ta tsaya tana jiran su. Kai daka gansu kasan yan uwa ne. Saboda kamar su sosai .. lamarin se godiya ga Allah. . Da dimbin yabawa da ganin daraja agare shi. Domin shi din mubuwayi ne gagara misali.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button