NOOR AL HAYAT COMPLETENOVELSUncategorized

NOOR ALHAYAT 10

✨ *Noor-Al-Hayat*✨
10….

Hadarin da ta gani garin ya kara mata kwarin gwiwa ta tashi da kyar tana layi kmr warce ta tashi ciwo ta samu taxi bayan ta fita haraban mall din, sai da suka dau hanya kafin ta iya bude baki ta gaya masa inda xa ta, kanta ta daura a kafarta har suka isa, tana jin yana ce mata sun kawo amma ta kasa dagowa, har sai da ya fito da sauri ya bude bayan motar
yana cewa “Madam, are you okay” mugun karfin hali tayi ta dago tana dubansa da idanuwanta da suka yi jajur, yace “You look sick…” Da taimakonsa ta fito taxin, bai karbi kudi ba ya ce taje ta sha drugs ta gyada masa kai ta shiga gida tana hade hanya, Ikon Allah ya kai ta bakin kofar flat dinta ta fadi dai dai kofar Khaleel tana dafe da xuciyarta da take jin kamar an caka mata mashi, bugu daya ta ma kofar ta hade kanta da kasa, bude kofar aka yi, Khaleel ya d’an ja baya yana kallonta da mamaki, saurin durkusawa yyi yace “Subhanallah, Are you okay….” Ta dago da kyar hawaye na sakko mata ta nuna masa kirjinta ya rikota da mamaki yace “Me ya same ki” girgixa masa kai ta dinga yi ta kasa cewa komai, tun tana ganin sa dishi dishi a hankali kuma bata kara ganin komai ba. A hankali ta bude idanuwanta da suka mata nauyi tana bin dakin da take da kallo, dai dai nan aka bude kofa wani matashi ya shigo Khaleel na biye da shi a baya, mutumin ya karaso inda take ya duka ya d’an yi murmushi yace “Hello….” Kallonsa kawai take, yace “How are you feeling now?” Tayi shiru, yace “Sannu, Allah ya sauwake, babu inda ke maki ciwo yanxu koh?” A nan ne ta gyada masa kai, ya juya yana kallon Khaleel dake rungume da hannunsa yana tsaye bakin kofar, likitan yyi murmushi yace “Quack MD do you mind coming over” d’an murmushi Khaleel yyi ya karaso kamar bai son tafiyar ya isa kusa da ita idonsa a kanta a hankali yace “ina ke maki ciwo yanxu?” Shi ma dai bata ce masa komai ba, likitan dake kusa da shi yace “Xa ki ci abu yanxu, sai yyi maki allura ya baki magani kin ji” kallonsa nayi ban dai ce komai ba, ya kara min fatan samun lfya sannan ya nufi kofa yace “Dr I will take my leave…..” bin bayansa Khaleel yyi suka fita waje, da damuwa Dr Ahmad yace “But… Tayi k’ank’anta da wannan matsalar, naga kamar she is in her early 20’s….” Khaleel ya sauke ajiyar xuciya yace “Probably it’s an inheritance….” Ahmad yyi dariya yace “Kai kuma ina mamakin wani irin Dr ne kai wani lkcn wllh….” Dakatar da shi Khaleel yyi yace “No you ought to have known me for long, I don’t treat people that are close to me, ban iya bane…” Dr Ahmad yace “Close to you? Yanxu kana nufin yarinyar nan is close to you? A ina ka santa” Khaleel yace “Noo ba haka nake nufi ba malam” Ahmad yace “Seriously you need to get rid of that behavior Dr, Allah ya bata lfya, ka sama mata abinda xata ci yanxu sai ka mata alluran ko shi ma baxa ka iya ba?” Khaleel ya hararesa yace “Wa ya sani….” dariya Ahmad yyi yace “Toh shknn ni dai bari inje in d’an yi karatu kai kam nasan tun ba yau ba ka gama, abun ka da manya” Khaleel ya shafa kai yace “Xan dai yi, tnx for ur care frnd” daga haka suka yi sallama Khaleel ya koma ciki, a hankali ya tura kofar bedroom din nasa, har lkcn tana xaune ta dago kai tana kallonsa, yace “What will you eat Khadija?” Bata ce komai ba, ya d’an yi jim yana kallonta, juyawa yyi ya fita, ba a dau lkci ba kuma ya dawo rike da cup din shayi, da kyar ta yarda tasa hannu ta karba shayin da yake mika mata ganin yanda ya kafe ta da ido, ta dinga sha kamar magani don bbu wani xafi, xaunawa yyi gefen gadon, bayan wani lkci ta mika masa sauran shayin hawaye cike idonta, ya tsura mata manyan idonsa, murya can kasa yace “Meye matsalarki Khadija, tell me what ur problem is” girgixa masa kai kawai tayi, ya mike ya fita da shayin ya dawo, allurorin ya shiga hadawa har ya gama sannan ya dawo gefenta yace “Let me inject you sai ki sha magani you will be relieved soon in sha Allah” ganin jiranta yake ta d’aga rigar a hankali ta kwanta yyi mata sannan ya dauko mata magungunan da goran ruwa ya ballar mata su ya mika mata ta karba ta sha, tashi ta shiga kokarin yi tace “Ina son xan yi sllh” ya nuna mata bathroom, ta kusa minti daya bata tashi ba bata ce komai ba, can ta mike ta shiga ta dauro alwala ta fito, Fita yyi xuwa apartment dinta don dauko mata Hijab, a hankali ya tura kofar bedroom, idonsa ya fara sauka kan enlargements dake dakin na hotuna, a hankali ya karasa dakin yana kallon cute twins dake hoton da ita kanta, sun rungumeta gaba daya tana murmushi,  ya sake mayar da dubansa kan daya enlargement din da suka manna mata kiss gaba daya, dauke idonsa yyi ya dau Hijab da ya gani linke kan gadon ya fita dakin, kan gadonsa ya ajiye mata Hijab din sannan ya fita. Ta jima xaune kan darduman bayan ta idar da sallahn magrib da isha, ido ta kafe ma wani hotonsa dake gaban mirror yana sanye da farin labcoat da stethoscope rataye a wuyarsa, a hankali ta sauke idonta daga kallon hoton, can tayi wani murmushin ta mike da kyar tana dukkan kokarin ganin bata yrda hawayen dake makale idonta ya xubo ba, ta linke masa lallausan pray mat dinsa ta ajiye sannan ta dau dankwalinta dake kan gadon ta yafa ta nufi kofa kamar mai counting steps dinta ta fito parlor, xaune ta gansa kan kujeran parlorn idonsa a kan wayarsa dake hannunsa yana operating, ya daga kai ganinta yace “You want something?” Girgixa masa kai tayi tace “No, am going to my apartment, thanks for ur care” daga haka ta nufi kofa yace “But….” Juyowa tayi tana kallonsa yace “Are you sure you will be okay all alone” tace “Yea sure” karasawa yyi kusa da ita ya mika mata makullin hannunsa ta karba ta bude kofa ta fita ta rufe masa. Bedroom dinta ta wuce direct ta fada kan gado, sae a sannan wani kuka ya xo mata, kukan da ta kasa yi tun daxu, Allah ya sani ta samu relief sosai kukan da tayi domin kuwa taji saukin abinda xuciyarta ke mata, har lkcn ta kasa gaskata wanda ta gani, why all of a sudden. Bata wani rintsa ba daren ranan don da baccin ya dauketa xata farka a firgice, daga karshe ma hakura tayi da baccin ta dauro alwala ta yi ta sllh sae dab da asuba wani bacci me nauyi yyi awon gaba da ita. 

A hankali Aliyu ya bude idanuwansa jin kwankwasa kofa da ake ta yi, ya tashi xaune yana kallon kofar yace “Who’s there?” Muryar small mum dinsa yaji tana cewa “Are you okay Aliyu? Baka fito sllh yau ba” a hankali yace “Nayi a nan Anty… Was having a slight headache ne” tace “Toh Allah ya sauwake, ka fito kayi break sae ka sha magani” daga haka tayi wucewar ta, mikewa yyi yana dafe kansa da yayi masa nauyi ya nufi window ya tsaya, lkci daya ya dawo ya xauna gefen gadon ya rike kan yace “Noo, nasan ba ita bace, ba Iman bace, it’s her look alike…. But….” mikewa yyi da sauri cike da damuwa da confusion yace “Why did she run then, me yasa ta gudu?? Does it mean ita ce? Ya Allah….” Jingina yyi da bango ya runtse ido, ya kusa minti ashirin a haka aka sake bubbuga kofa, ya bude ido a hankali cikin sanyin murya yace “Who’s there?” Muryar Maryam cousin sis dinsa yaji tace “Yaya ni ce” yace “Ya aka yi” bata ce komai ba, hakan yasa ya karasa ya bude kofar tace “How was ur nyt?” Ya dauke kai yace “T’was good” Tace “Mumy wai ka fito ka yi breakfast” yace “Ohk” daga haka ya rufe kofar ya koma gefen gado ya xauna, kallon agogo yayi ganin takwas ya tashi ya shiga bathroom, wanka yyi ya fito, ya fi minti sha biyar kwance jin kamar xaxxabi xai rufesa, can yyi ta maxa ya mike ya shirya ya dau makullin motarsa ya fice gidan ba tare da ya bari Small mum dinsa taga fitarsa ba. Mikewa xaune Khadijah tayi da sauri daga baccin da take ta dalilin bell da aka danna, ta tashi a hankali jin jiri na dibarta, ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta wanke baki sannan ta fito ta dau hijab ta sa ta fito parlor ta bude kofar, har lkcn yana tsaye gun, yana kallonta a hankali yace “Bacci kike na tashe ki?” Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace “Na tashi” yace “How are you feeling now?” Tace “Alhmdllh, ina kwana” yace “Lafiya lau” jin yyi shiru ta dago kai suka hada ido, saurin sauke idonta tayi, yace “You cried!” Ta girgixa masa kai kawai, yace “Noo you cried malama” lkci daya hawaye ya kawo idonta ta kasa ce masa komai, shiru yyi bai sake cewa komai ba, bayan wani lkci yace “Shiga ciki” ba musu ta juya ta koma ciki ya rufe kofar, daki ta koma ta kife kai da pillow wasu hawayen na xubo mata, duk taji ta tsani xaman UK din, ta tsani karatun, dago kanta tayi da sauri ta dalilin *SUDAIS* da ya fado mata, bata san lkcn da tayi murmushi ba kawai taji kamar an yaye mata bakin cikinta, tayi tagumi a sanyaye…. Ta fi minti sha biyar a haka, ji tayi duk duniya bbu wanda ta tsana… tsanar da bata da iyaka irin wanda tayi tozali da jiya a mall,  taji an bude kofa ta dago da sauri, jin shiru ta mike ta fito parlor tana goge idonta, xaune ta gansa kan kujera yana hada allura, ya dago ya kalleta, lkci daya ya hade rai , bata yrda sun sake hada ido ba, ya ajiye alluran hannunsa ya mike yace “Are you alright? under this condition stil xaki dinga xama daki kina kuka haka, dama kuka na magani? idan ma damuwa gare ki baxa ki sa Allah ran ki ba” bata iya tace komai ba bata kuma yrda ta dago ba, ya koma ya xauna, bayan kusan minti uku ya nuna mata cup din shayi da bread dake ajiye kan table yace “There” ta karaso ta dau shayin yace “With d bread” girgixa masa kai tayi ta fara shan shayin, murya can kasa yace “Look…” ta dago idanuwanta ta kallesa ya nuna mata kujera, a hankali ta karasa ta xauna, ajiye cup din tayi bayan ta sha shayin, yace “ur injection” tashi tayi ta wuce daki ta daura xani cikin Hijab din jikinta ta fito, nan parlorn yayi mata alluran ya bata maganinta, yace “You go get some rest now, ki yi bacci da yawa kin ji” yyi kasa da murya yace “And please kar sake kuka ur condition isn’t encouraging, always remember Allah xaki samu natsuwa sosai…” Bata ce komai ba ta mike ta wuce daki ya bi ta da ido, tashi yyi ya dau cup din ya fita. Sai bayan azahar ta farka daga baccin da tayi, sosai taji xuciyarta ya mata saukin xafin da yake mata don ta samu bacci da yawa, kuma taji ddin drugs din, yunwa taji na dawainiya da ita, ta tashi ta shiga bathroom ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, shafe shafe tayi ta dau gown mara nauyi da tsayi ta sa ta shimfida darduma ta saka hijab har kasa ta tada sllh, tana idarwa ta cire Hijab din ta linke sannan ta fito parlor don dafa ko da indomie ne ta ci, still tayi ta juya baya da sauri a parlorn ganinsa da tayi dai dai center table ya ajiye ledan hannunsa da alamar shigowarsa kenan, Bata jira ta ji abinda xai ce ba ta nufi daki da sauri ta rufe kofa, xama tayi kan gado ta hade kai da gwiwa duk taji kunya ya kamata, ta fi minti goma a haka, can dai ta mike a hankali ta saka Hijab din da tayi slh ta fito parlorn, bbu kowa ciki ta karasa gun ledan ta bude taga abinci ne da drink, kadan ta ci ta fara gyaran gidan, dab da la’asar aka danna bell, ta kasa xuwa ta bude, can dai taa isa gun kofar tace “Who’s there?” Yace “Koh” bude kofar tayi ta juya ta dawo parlorn ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yace “Sorry….” Da sauri ta katse sa tace “Ohh bakomai” yace “Bakomai me?? ai baki jira kin ji abinda xan ce ba malama” ta d’an kallesa, sai taji kunya, ya buda ido sosai yace “Dama cewa xan yi, sorry… me yasa kika gudu daxu?” Bata ko kallesa ba balle tace komai, yyi murmushi yace “Toh kin ci abincin” kai kawai ta gyada, yace “How you feeling now” tace “Naji sauki” duk wannan abun bata yrda ta juyo ba sai gyare gyare take, yace “Alluran ki…” Da sauri tace “No naji sauki, xan sha maganin” shiru yyi na kusan thirty seconds, yace “Malama” sai a sannan ta juyo suka hada ido, jallabiya ce Milk colour jikinsa da ya fiddo da ainahin kamanninsa na larabawa, shi ya fara dauke kansa sai kuma yace “ohk… Ki sha maganin” daga haka ya fita ta bi sa da ido har ya rufe kofar.


*Haske writers association*????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button