Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 52

Episode 52

……….Sai dai addu’ar tata bataci ba. Dan suna shigowa falon daya raba sashensa da nasu Anne sukai kiciɓus. Sai dai Ramadhan ya ɗauke kai kamar baiga

Anne ba dan shima dai kunyar yaji. Ɗan murmushi Anne tai tana binsu da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya da numfashi tana mai binsu da addu’oin zaman

lafiya da samun zuri’a masu albarka.
       Har ya isa ƙayataccen bedroom ɗinsa da komai na ciki yake kalar royal blue and golden bata yarda ta buɗe idanunta ba. Ya direta a saman lallausan

gadonsa da yaji shimfiɗu masu inganci, anan ma da runfa ta net white color mai kwalliyar blue kaɗan-kaɗan.
      “ALLAH nauyine dake Ustazah, wannan ai sai kisa na rame”. Ya faɗa cikin kunenta tare da sumbatar kuncinta na haggu. Ita dai bata motsa ba balle ta

buɗe ido, sai da ta ɓata fuska da tura baki yace tana da nauyi. Murmushi yayi da ɗallin lips ɗin a hankali.
       “ALLAH da zafi Ya Ramadhan”.
“Ai dama dan kiji zafin nayi. Idan kuma wannan yayan bai fita bakinki ba ALLAH sai nazo na darje ciwon na banbanta miki tazarar dake tsakanin Yaya da ni”.
      “Toni mizance dan ALLAH?”.
“Oho ya rage naki tashi kisha magani kisa kayan barci kar wannan towel ɗin yasa mura kamaki”.

        Da ƙyar ya iya sakata tashin tasha magungunan da tun bayan sallar magrib aka kawo masa su. Dan tun da yaga yanda take tafiya ya yanke shawarar

nemansu. Kayan barci ya ajiye mata ya shige toilet, hakan ya bata damar sakawa da sauri-sauri tai amfani da designers turarurrukansa masu ɗan karen ƙamshi

ta haye gadon da sauri tai kwanciyar kai da kafafu tare da yin addu’a kafinma ya fito taja bargo har saman kanta. Dan tasan kaɗan daga aikinsa ya fito da

towel babu kunya a gabanta.
          Ilai kuwa hakan ya fito kansa tsaye, ya ƙaraso har gaban gadon saboda wayarsa dake ring. Kasancewar ata gefen can ɓangaren Raudha ta kwanta shi

kuma sai ya zauna a gefen gadon ta ɓangaren data bari domin shi. Yana goge ruwan fuskarsa da jikinsa yana wayar da A.J dake kula masa da business ɗinsa a

can America yanzun. Cikin harshen turanci suke maganar cike da ƙwarewa, dan haka Raudha ta shagala a saurarensa dan yanda harshensa ya karye bama zakace

yasan wani yaren Africa ba. Wayar taɗan jashi lokaci dan harya miƙe ya koma gaban mirror. Yana gyara jikinsa yana cigaba da wayar harya shirya cikin

tausasan kayan barci, kafin taji ya sake zama a gefen nata. Kaɗan ta ɗaga bargon ta leƙashi, sai tagansa da kofin tea daketa turiri sai kuma lap-top da yake

ƙoƙarin kunnawa har sannan wayar na maƙale a kunensa. Shagala tai a kallonsa ƙasan zuciyarta na godema ALLAH daya azurtata da samunsa matsayin miji. Banda

ƙaddara ita tasan ko a ƴar aiki bazata ishi Ramadhan kallo ba. Sai dai UBANGIJI shi mai rahamane mai kuma jinƙai. Sannan mai ƙaddara abinda yaso ga waɗanda

yaso koda akwai tazarar nisa ta rayuwa ko yare ko addini ko yanki a tsakanin bayinsa.
       Yaja lokaci yana aikin sai dai ya ajiye wayar tuni, har barci barawo yay tashiri kan Raudha saboda maganin data sha.

            Ramadhan da idanunsa ke faman raɗaɗin barci, ya kai hannu bisa goshinsa ya murza da furzar da iska mai nauyi. Ya gaji matuƙa, gashi abinda

yakeyin mai muhimmanci ne. Dan kayan da zasu fitarne a sabuwar shekara A.J ɗin keson ya duba abinda baiyiba su ajiyesa gefe wanda yayi su fara packaging

ɗinsa yanda ya dace da mikashi ga yan talla kafin a fitar.
       A hankali ya rufe lap-top ɗin bayan ya kashe yana ɗan danna gefen wuyansa alamar riƙewa. kofin daya sha lipton da lap-top ɗin ya sauke kasa. kafin ya

koma toilet ya ɗauro alwalar barci sanna ya hawo gadon da danna wani abu net ɗin ta buɗe gaba ɗaya ta lulluɓesu. Sai ɗan hasken fitilar cikin gadon daya

kunna ya kashe ta ɗakin gaba ɗaya. Bargon da Raudha take ƙudundune a ciki ya ɗage, sai yaga ashe kai da ƙafa take kwance. Kansa ya ɗan girgiza kawai, yasan

tadata yanzu wani aikinne kuma, sai kawai ya kwashi piilos ɗin shima ya maida inda tasa kanta dan bazai iya yarda da kwanciyar kai da ƙafa ba shida matarsa.

Gara ace ɗaki suka raba ko gadon. Dan lokaci Amnah ko faɗa sukai da ita bai yarda da raba ɗaki ba. Dole ta kwana tare da shi ko zata kwana masa kukan baƙin

cikin daya tusa mata. Inma itace tai masa laifin duk zafin da yakeji a ransa ya gwammaci su kwana waje guda ɗin, shi kuma yasan a inda zai fanshe haushinsa

ai (????????mugu ɗan masa????).

        Sai da ya janye bargo gaba ɗaya ya karemata kallon yanda kayan barcin sukai mata ƙyau kafin ya saki wani ɗan guntun murmushi da iya laɓɓa ya tsaya

masa. jikin nata ya taɓa yaji zazzaɓin ya sauka, sai kaɗan da bai ida hucewa ba dai. Filon da take kai shima ya ɗaura kansa suna fuskantar juna. Ya sumbaci

goshinta da laɓɓanta sannan yay musu addu’a yaja bargo tare da rungumeta yana sauke ajiyar zuciya.

        Da asuba ya rigata farkawa, sai dai yana motsawa itama ta farka. Gaba ɗayanta a jikinsa take lafe da alama hakan ya mata matuƙar daɗi, sai dai suna

haɗa ido tai saurin ƙoƙarin janye jikin nata kunya kamar zata nutse. Riƙota yay ya hanata damar juyawar. Cikin ɗan daburcewa take ƙoƙarin faɗin, “Kayi

haƙuri ni ALLAH ban san ma….”
      Ruf ya rufe mata baki da nashi batare daya bari ta ƙarasa faɗa ba (????ƙazanta ko brush babu????????). Duk yanda taso kwatar kanta bata samu damar hakanba.

Dole ta nutsu ta barshi ya gama yamutsata san ransa tsoro kamar ya kasheta. Dan a tunaninta za’a tafi next level ne????. Da ƙyar ya iya yakar ƙansa ya barta

jin an sake kiran salla na biyu, ya sauka a gadon da ɗan zafin nama ya faɗa toilet. Ruwa mai ɗumi ya sakarma kansa yana mai sauke nannauyan numfashi da

rumtse idanu. Sunan ALLAH ya dinga ambata dan yasan lallai akwai matsalolima ba matsalaba. Gashi da alama Raudha tamkar Amnah take itama zatai shegen raki

duk da ita daba sickler ɗin ba. Dole ya haɗa harda wankan lada. Koda ya fito yay mata maganar ta tashi bata motsaba dan kunya harya zura jallabiya yasa

turare ya fice. Sai dai ya gargaɗeta karya dawo ya sameta a kwance bata tashi tayi salla ba, ta kuma sake shiga ruwan zafi inba hakaba ya dawo da kansa zai

sake gasata.
          Raudha da gaba ɗaya a firgice take da Ramadhan ta miƙe da sauri bayan ta leƙo ta bargo ta tabbatar ya fita. Toilet ɗin ta afka itama. Ta watsama

jikinta ruwa da ƙara gasa ko’ina duk da dai Alhmdllhi garas ta tashi yau sai dai rashin jin karfi na sabo.
            Koda ya dawo a saman sallaya ya sameta tana karatun alkur’ani. Hakan ya masa daɗi sosai, sai shima kawai ya zauna suka cigaba dayi tare. Duk da

mamaki ya matuƙar ɗaure kan Raudha jin yanda yake karatu a nutse cikin daddaɗar muryarsa mai faɗi da amo da gaba ɗaya ta danne ƙarfin tata siririya mai

zaƙi. Sunyi karatun da yawa sannan sukai addu’a. Kanta a ƙasa tace, “Ina kwana”.
    Bai amsaba, sai dai ya kafeta da idanu, ɗan dagowa tai kaɗan sai suka haɗa ido, zata maida ya riƙo habarta da hanun damarsa. “Karki kuskura ki rufe

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button