KannywoodLabarai

Fati Slow ta shigarwa sarkin waka, ta yiwa Nafisa Abdullahi wankin babban bargo

Tsohuwar jarumar fim Fati Slow ta shiga rikicin da ya barke tsakanin Naziru Sarkin Waka da Nafisa Abdullahi kan almajirai.

Slow ta ce Naziru ya yi gaskiya don babu wanda aka yi asarar haihuwarsa sama da wanda zai dunga iskanci yana nunawa duniya suna zagin iyayensa shi kuma yana dariya.

Ta kuma bayyana cewa rashin cikakken ilimin addini ne ya sa har Nafisa ke zagin yaran da aka tura almajaranci Hausa Legit ta rawaito.

Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman da aka fi sani da Fati Slow ta fito ta goyi bayan caccakar abokiyar sana’arsu, Nafisa Abdullahi da Naziru Ahmad ya yi kan zagin iyayen da ke tura ‘ya’yansu almajiranci.

Fati Slow ta ce tabbass babu asararre sama da mutumin da zai dunga iskanci yana watsawa duniya ana zagin iyayensa amma ko a jikinsa.

Tsohuwar jarumarta bayyana cewa sai inda karfinsu wajen fada ma duk mutumin da zai zagi almajirai gaskiya.

“Naziru wannan maganarka gaskiya ne babu cikakken dan iska kuma wanda iyayensa ma basu san yadda za su yi da shi ba shine wanda zai yi iskanci ya turo duniya ana ta zagin iyayenshi yana dariya, shine cikakken dan iska.

“Kuma wanda yake ganin Naziru bai yi daidai ba, Naziru ya fito ya yi magana ka yi abun da za ka yi ko ki yi abun da za ki yi, ya fito nya fadi abun da ke ransa nima na fito na fadi abun da ke cikin raina.

Ai cikakkiyar jahila ce ke, abun da yasa nace cikakkiyar jahila c eke ai baki da ilimin addini, muma ba shi garemu ba don haka baki isa ki ci mutuncin almajiri ba, baki isa ki zagi almajiri ba. Zagin almajiri ba daidai bane kuma sai mun yi magana saboda ba tsoron wani muke ji ba.”

Ga bidiyon kuji da kunnen ku:;

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button