FITAR RANA 1
Agaban maimunatu da mahaifinta garba maye komi ya faru,suna kallon wutar yanaci balbal suna dariyar mugunta tamkar ma zasu saka ruwa a ƙasa susha sabida su suka shirya komi ya tafi cikin samun nasara.
Duk wani abun da suka hanɗame na gonaki da dabbobi da rumbunan abincin hassan da badiatu dashi suka cikawa rigarsu iska tunma kafin mutanen anguwa su hanƙara da abunda suka aiƙata.
Daga kauyen ringin gana kuwa matar datake riƙe da jaririyar su ganin har safiya batagansu ba yasa jikinta yay mugun sanyi,dan tamkar ɗanta na cikinta haka takejin aliyu dik dama bata haifesa ba rainonsa kawai tayi, xuciyarta sosai ya bata cewa tabbas wani mummunan abune ya afku dasu wanda yay sanadin rashin dawowarsu ga ɗiyarsu, dan dama tasan da wuyane, su iya fidda kansu a ƙaidin shaharren matsafi kamar garba maye da shaidaniyar ƴarsa anmuna.
Bayan ƙwana bakwai da afkuwar komi matar nan ta dauƙi jaririyar nan acikin mafi sirrikan lokacin dare suka yi hijira ixuwa garin jos,inda ta nemi haya acikin wata ƙauyen makiyayan fulani ,anan tay zamanta ta raine Wasimé,har ta girma. ranar da wasimé ta cika shekaru 9 a duniya anan ta ƙara hada kayansu a jaka da zimman kaita inda xatayi rayuwarta na dindin din…..