FITAR RANANOVELS

FITAR RANA 12

“Wayyo Allah na..
Ji katoton gida…..
Ahe anan kake zama yo shiyasa mana bakason daɗewa a gidanmu

Dariya ne ya kufce masa ganin yadda tayi maganan with so much ignorant sai kalle kalle takeyi abunta, jawo hannunta yy suka nufi ciki.

A bakin kofar wani katafaren palo suka tsaya snn ya danna door bell, after like 4mints mai aiki tafito sanye da blue uniform tazo ta bude mai kofa tana dan murmushi,”ure welcome sir.Babu yabo babu fallasa yace “thank u susan.”Cikin sauri wasime tace ma mai aikin ina kwana anty?Murmishi mai aikin tay saidai Kafunta amsa saheeb ya wani hade ransa tare da cewa wasime”wayace miki ki gaisheta toh? ido kawai ta tsura masa cikin rasa mezatace tuno da cewa bilti ta gargade ta akan ta rika gaishe da babba…

Yace “wann Mai aiki nace u dont have to greet her kinji?..ai itace zata gaishe ki bake zaki gaisheta ba..”da wutsiyar ido wasime ta dan sace kallon mai aikin ganin ta babba wuce sa’arta,abun saiya kuma dore mata kai yo shawarar wa zataji kenan na bilti ne kona saheeb?,mai aikin bataji dadin hakan dayay ba amma tasan bata isa ta nuna ba, murmushi tay ta gaida wasimen kawai ta wuce ta tafi tabarsu a tsaye awajen.

“Beauty Karki ƙara gaishe da kowa saina umarce ki

Kanta ta gyada mishi a hankl hade da binshi cikin wata ƙerarrayiyar royal falo daya shige dasu ciki mai niimtaccen sanyin A.c da kuma dadin turarrukan wuta masu sanyin qamshi tana biye dashi abaya har suka iske gaban wasu lumtsa lumtsan cushions milk colour da gold wanda girman su da yawansu kawai yakai acike manyan faluka uku harma ayi ƙari dasu,ga wani babban tv plasma mai girman iya dungu to dungu.

Akan daya daga ckin lumtsatsun kujerar ya dorata ta zauna,”snn ya zauna agefenta yana mai kallon cikin kwayar idanunta dasuke matukar kawatar dashi cikin wani sanyin yanayi mai rikitarwa.

Shikadai yabarwa kansa sirrin irin tunanin da zucyarsa takeyi akan wasime..danji yake kamar asalin itace matarsa in the future!

Har wani Imagining yakeyi inda ace wasime fara sol ce toh da tuni baki da idanun mutane sun kasheta har lahira,ahaka ma gani yake kamar bakar fatan da Allah ya bata ne kawai yake dan protecting dinta daga samun too much attention na mutane.

Ya dade yana kallonta ayayinda taji kirjinta na bugawa da dan karfi sabida fargaba da kuma nauyin idanunshi daya zubosu duka acikin nata yana mata wani irin mayyar kallo..a dan takure cikin sanyin murya tace..”Yaa s..aheeb..saheeb
Baisamu damar amsawa ba ya lumshe idanunsa yanajin sautin muryanta har cikin zcyarshi da duka ilahirin jikinshi

Muryanta a sarkafe tace “uhm uhmm to ina su innarkan suke ne?..
Kace…Gefen fuskarta ya shafa cikin katse mata sauran maganan snn yy dan murmushi muryansa kasa kasa kamr maijin bacci yace” hey relax they are coming okay?
So nake kidan zauna dani
Dada Mikewa zaune yay yana kallonta tay saurin sauke kanta can kasa bata ƙara dagowa ba.

,ko inje in dauko miki su ne?..da sauri ta dago kanta ayanayin fargaba “tace eh

Mikewa tsaye yy
“Zaki iya zama anan ke kadai kijirani?.kafun ta amsa harya rusuno kasa agabanta cikin marairace fuska…”i dont wanna leave u alone cuty, wani jawota jikinshi yy game da kwantar da ita akan faffadan kirjinshi kamshin turarensa duk ya cika mata hanyar fitar numfashi,a hnkli ya shiga shafa bayanta cikin wani irin yanayn nuna so da shakuwa,matseta yy gam ajikinshi yana catching breath dinsa haka ya dinga cuddling nata akan kirjinshin har jikinta yay sanyi..wani lumui fuskanta yy tana famar zazzare idanunta waje

Nannauyar Ajiyar zcya kawai ta dinga sauƙewa
Tanajin wani bambabra kwai,haka kawai ta soma jin tsoro tsoronsa acikin ranta kkri takey domin ta kwace kanta ajikinshi saiga sautukan takun takalmi bana mutum daya ba,numfashi taja hade dayin kasa kasa da idanuwanta ayayinda saheeb din ya maida kallonsa inda sautin takalman ke fitowa.

Jim kadan Wasu zugan yara yara da yan mata guda biyu suka bayyana
Yara yaran sukayo kanshi da gudu cikin murnan ganinshi” yeeyyyyyyyyyy
He is back…da faraa sosai akan fuskrsa ya tarbesu suma wasu su dale bayansa wasu suna cakulinshi dariya yakeyi sosai”..

Yan mata biyun suka tsaya kikam agefe kamar yadda wasime ta ɓata shiru awajen,dukansu kallanta suka tsaya yi barin ma budurwansa zee baby da bata gane waye wasimen ba.

Dayar kuma ƙanwarsa ce anisa dayake mutuwar kauna arayuwansa,anisa tana kama da saheeb sosai dan haka takeda kyaun fuska itama na daidai misali,wani hadadden off shulder pink flowery gown ta saka na kamfanin milano da pink glittery cover shoes na prada maidan tudu kanta yasha gyara da gel dan bata dora masa dankwali ba, but still she look bit older than her real age saboda tanada jikin girma sosai.

Zee budurwnsa data kasa hkri tace
“Babe waye kuma wannan?daga ina kasamo ta..hmm sannu sarkin kwashe kwashe

Tunkafin ya amsa tambayar zee din, anisa ta isaga wasimé,
agabanta ta durkusa Ahnkli tana mai dago kanta sama, hade ido sukay snn shiru yabiyo baya, dan shiru anisa tay snn ta canko abun tace “wow,Wasimé right?..
kece wasimen da yaa yake ban labari?
A dan rude wasime ta gyada kanta jin ankira sunanta,cike da sakin fuska anisa ta juya ta kalli saheeb snn tace..
“wowww bro she is soo cute…melanin goddess..gaskiyane yau na yarda dakai akwai bakake kyaywawa a duniya, comn check this girl out.arrghhh she is damnn…dariya sosai saheeb yay cikin jin dadin abunda anisan take fada
,hannun wasime ta rike tana dan wasa dashi sauran yaran duka suka tsaya suna satan kallonta,wanda dik kannen zee baby ne data kwasosu a gida dan su zo nan su wataya da kuma a basu kyautatuka da kudade.

Dukkaninsu bazasu wuce saoini da wasimen ba maza biyu ne da yan mata su uku sai yar ƙaramr cikinsu wanda batafi shekara biyar ba

Wani ufffff zee baby taja doguwar tsaki acikin wuyarta tana hararar wasimen da gefen idanunta’,kallon anisa tayi…oh wai kema kinsanta ne?who is she pls…abeg educate me nifa banganeta ba.

Riko hannunta saheeb yy
Yana murmushi baby baby wato ke kin rantse saikin gama sanin duka dangina ko?hey slow down badai hakan zaisa na kai baiko na gidanku bafa,acikin sigar wasa ya rada mata maganan acikin kunnenta amma sai maganan yay mata zafi, wani fauce hannunta tay tanamai hararsa kamr zata hadiyesa dan haushi riƙo hannun wasime yay ya jawota kusa dasu
“Look, She is my little cuty,she is My sugar girl..
kuma ƙanwata ce tunda dai kanwace guda awajen babban amini na taheer,wani rau rau da idanu zee tayi like she dint get him well,ji tay kamar ya kira sunan taher din daya gama walakantata ranar wani
,gyara tsayuwarta tay da kyau tana ɗana masa wasu kafuran tuwon harara,tace “babe waye kuma taheer?wani taheer kake nufi badai taheer din dana sani ba ko..
Pls dont tell me harynzu kana kula yaron can

batare da ya wani kula da yanayinta ba yace “ofcouse shine mana, TEJ din dai da kika sani
Ai ba saina kulashi kafin nayi kawance da kanwarsa ba.

Wani doguwar tsaki taja batace mishi uffan ba ta kau da kai…ranta taji yana balain harzuka,she tot saheeb will be a man and stand for her right for once arayuwa amma ina,da alama harma sun shirya da abokinsa despite marinta dayayi.

dada bin wasimen da wasu matsiyaran kallo tay”Kace wann kanwar taheer ne Nd why is she black..Keee!!!ta dakawa wasime tsawa saida ta tsorata ta kankame jikn anisa abaxata..”cikin sauri anisa ta rirriko ta “Adda zainab meye haka? Bata ko kulata ba ta cigaba da zaro ido waje wa wasime..’ke kanwar tej ne wai?.tsuru tsuru tayi da ido batako iya motsi ba bare amsawa,a take ruwa ya cika tammm a kwayar idanunta kiris ya rage ta fashe da kuka mai tsanani

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button