JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 27

Abuturrab yace “But you didn’t tell me kina xuwa Aneesah” Aneesah tayi wani murmushi tace “How will i tell you ina xuwa Aliyu, dama dalilin da yasa kake walakanta ni kwana biyu kenan, dama wata ka samu? Dama wannan ce dalili” Daga sama har kasa take kare ma Jiddah kallo tana murmushin takaici tace “Ki bar murna kin samu pilot har yana kawo ki gidansa saboda tsagwaron so, nima haka ya dinga min, but….” Abuturrab ya katse ta yace “Come off it pls Aneesah, what’s all this? I thought i explain better to you her position, she is the lady….” Aneesah ta sake kallon Jiddah da sauri, Jiddah dai banda kallonta ita ma babu abinda take, A hankali Aneesah tace “Which lady Aliyu?” Yayi kasa da muryar yace “Ba ke kika ce in kawota ta xauna gidanku ba” Sosai gaban Aneesah ya fadi don bata ta6a tunanin Jiddah ce wnn yarinya da Abuturrab ke fadi mata ba, ta dinga kallon Jiddah xuciyarta na bugawa, ta ma rasa abinda xata ce masa, Abuturrab yace “Tunda kin xo yanxu sai ku tafi tare, dama anjima nake son kai ta gidan naku, hopefully nasan Mumy ta yarda ta xauna with ur family…” Aneesah ta hadiye abu da kyar, har sannan ta kasa daina kallon Jiddah da tayi mata wani kwarjini, a xuciyarta ta shiga kokwanton anya ita ce me awaran da Aunty ta ce, or is Aliyu playing her?? Abuturrab ya juya ya kalli Jiddah bbu yabo bbu fallasa yace “Dauko mayafinki” Shiru tayi tana kallonsa, a d’an tsawace yace “Baki ji na ne?” Ta koma baya tace “Toh ina xanje idan na dauko?” Yace “Ban sani ba, wuce ki dauko” Juyawa tayi ta koma can tsakiyar parlon ta tsaya kamar xata yi kuka tace “Allah ni babu inda xanje, ba gidan Baabarmu nace ka maida ni ba, nasan ita wacece da xan bi ta” Daga maganarta Aneesah ta kara tabbatarwa ita ce me awaran, Abuturrab ya saki baki yana kallon Jiddah, Aneesah ta hade rai tace “Toh nan din gidan ubanki ne da baxa ki bari ba?” Jiddah ta kalleta, a hankali tace “Ubana fa kika ce?” Aneesah da xuciyarta ya dau tafarfasa tace “Shi din…” Lkci daya Jiddah ta fashe da kuka tace “Ba dai ubana dake kabari ba wllh sai dai naki” Aneesah ta saki jakar hannunta tace “Kika xagi ubana?” Jiddah ta goge idonta tace “Ehh an xaga, me nawa uban ya maki da kika xagesa ke?” Aneesah tayi kanta a mugun fusace, fixgota Abuturrab yyi yace “Hey are u okay, what are u trying to do?” Fixge hannunta tayi kamar wata zakanya ta nufeta, cikin tsawa Abuturrab yace “Don’t try that Aneesah, u will definitely see the other side if me by

touching her” Tuni Jiddah ta tsorata ta bar wajen da gudu ta yi hanyar kitchen hakan bai hana Aneesah bin ta ba, shakota Aneesah tayi tace “Uban wa kika xaga?” Tuni Abuturrab ya nufesu, Jiddah ta kwala kara ta gatsa mata cixo a hannu, Aneesah bata yi wata wata ba wajen sauke mata lafiyayyen mari a fuska sannan ta wuntsular da ita a kasa tana cewa “Don kaza kaxanki ubana sa’an kaf danginki ne aka ce maki?” wani ihu Jiddah ta fasa tana cewa wayyo bayanta, wayyo kafarta, Kamar daga sama Aneesah taji saukan tagwayen mari wanda sai da yasa taga duhu na few seconds, ya fixgota fiercely yace “How dare you? You bitch” with shock Aneesah ke kallonsa, ya nufi kofa ya wuntsular da ita waje kamar yanda ta ma Jiddah yyi banging kofar, Banda rusa kuka babu abinda Jiddah dake yashe a kasa take tana kiran Baabarmu, Bude kofar Aneesah tayi tana daga tsaye bakin kofa hawaye kaca kaca a fuskarta tace “You called me a bitch Aliyu?? Ni ka walakanta ka sauke yatsunka fuskata a kan wannan yar talakawan bagidajiya jaka? Ni ka ci ma mutunci haka in her present? U threw me out of ur house a kan yar talakawa me tallan awara?” Jiddah ta goge idonta ta mike cike da tsiwa tace “Idan ana tafiya lahira da arxiki sae ki daura naku a kai ki tafi da shi in ga, kuma Allah ya isana, ban yafe maki ba, axxaluma….” Fixgo hannunta Abuturrab yyi ya nufi daki, cikin kuka tana son kwace hannunta take cewa “Ni ka kyaleni, me na mata xata mareni….” Turata yyi cikin dakin ya sa makulli, sai a snn ya daga kai ya kalli Aneesah, ji yyi gaba da gwiwansa ya sace, ya nufeta, tana ganin haka tayi wani murmushi tace “Watch out for it Aliyu, xaka san ba a ta6a mu a xauna lafiya, daga yau ka kafa daka sanin abinda ka min a rayuwarka…” Daga haka ta dau jakarta xata fita parlon hawaye na sauka idonta, ya rikota yyi kasa da murya yace “But Aneesah….” Ko rufe baki bai yi ba ta sauke masa mari sau biyu, hakan bai sa ya saketa ba ta dinga dukansa a kirjinsa, ya rungumeta gamm yace “I’m sorry Aneesah” kuka kawai take, shi kam duk jikinsa yyi sanyi, cikin rawar murya tace “A kan wannan bagidajiyar xaka mareni and throw me out of ur house Aliyu??” Ya kwantar da ita kirjinsa yace “U are misperceiving me Aneesah…” Turasa tayi da karfi ta nufi kofa tana kuka ta fita, dafe kansa yyi ya xauna saman kujera yana furta Innalillahi wa inna ilaihi

raji’un, daukar wayarsa yyi ya shiga dialing number Ahmad, har ya katse bai dauka ba, yana ta xaune parlon har kusan magrib sannan ya mike da kyar, bedroom din da Jiddah ke ciki ya nufa ya bude kofar, kwance ya ganta a kasa, ya karasa ciki yana kallonta ya duka, bacci take, ya kai hannu goshinta, bude ido tayi, ya daure fuska ya mike, ta tashi xaune tana mitsika ido, yace “Kin san warce kika xaga daxu?” Ta kallesa tace “Toh ai nima bata san wacece ni ba” ya duka yana kallonta da kyau yace “Gaya min ke wacece?” Ta turo baki ta taki cewa komai, kallon fuskarta da shatin mari ya kwanta kawai yake, can ya mike jin xa a tada sllh ya fita dakin.

Abuturrab na dawowa masallaci ya ga kiran Ahmad a wayarsa, ya xauna sannan ya kuma dialing number sa ya kai kunne, daga daya bangaren Ahmad ya daga yace “Ya kwana biyu?” Abuturrab ya shafa kansa ya mike ya koma dakinsa, a hankali yace “Alhmdlh, how is work?” Ahmad yace “Alhmdlh, baka yi piloting xuwa Abuja bane yau” Abuturrab yace “Ina Abuja” Ahmad yace “Alright, ya na ji ka so calm dude?” Abuturrab bai ce masa komai ba, Ahmad yace “Xan shigo after isha” Abuturrab yayi kasa da murya yace “Ka taho da paracetamol or any pain reliever” Ahmad yace “Ko har Aneesar ta je ne?” Abuturrab ya katse wayar, ya ajiye yana tunanin where he is going to start from, sure yasan yana son Aneesah sosai baya son komai da xai bata mata rai, But why did all this happen, why did things turn out this way…. Shafa kansa kawai yayi

knowing the only way out now shine ya tura gidansu in few days time, wayarsa ya sake dauka har xai yi dialing numberta ya fasa. Abuturrab na xaune parlor bayan ya dawo isha yana jiran xuwan Ahmad, karfe takwas da few minutes Ahmad ya danna bell, ya mike ya bude masa kofa, Ahmad ya shigo parlon, xaunawa yayi saman kujera yace “After leaving me all my self with my wedding preparation, still u have d gut not to ask how everything is going…. right?” Abuturrab yace “Ohk ka fara shirye shirye ne?? Sure juma’ahn sama ne koh? I’m sorry na manta wllh, what are u up to now? Kasan ba haduwa muke yanxu a kadunan ba kamar da” Ahmad yyi dariya yace “Ya xa mu hadu kuwa, tunda ga ka ga amaryar ka Jiddah” Abuturrab ya tsura masa ido, can yace “Is there anything i will gain idan na maka karya Ahmad?? But don Allah ka gaya min me yasa kake ganin har ynxu matata ce ita?” Ahmad yace “Toh gashi nan ba sai na fada ba, da fa duk na shigo kd sai mun hadu, infact kai ma kake xuwa gidanmu ynxu kuwa kana gidanka, idan ba wanda yyi sabon aure ba, giyan auren na dibarsa waye ke yin haka??” Abuturrab yace “Ka dai jira xanyi auren kwanan nan sae kaji dadin fadin duk abinda ke ranka, amma yanxu kam i am a bachelor just as u, sae sabon title da na samar ma kaina na xama Uba, i am more like a father or guardian now” Ahmad yyi murmushi yace “Toh ka bani ita inyi ta biyu da ita Captain” Abuturrab ya kallesa, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Are you for real?” Ahmad yace “I’m serious wllh in dai Umma xata yrda i will” Abuturrab yace “Ohk, but…. How are we going to open up all this to our parent? Kasan dai ynxu banda Aunty da kai, sai ita yarinyar babu wanda yasan babu auren nan” Ahmad yace “We will cross the bridge when we reach there, yanxu dai ka amince min kai?” Calmly Abuturrab yace “In da gaske kake na amince, nima burden xai sauka kaina, if not for her da banyi making mistake da nayi daxu ba” Ahmad yace “Wani mistake?” Abuturrab ya dau remote din TV yana canxa channel yace “Ba ruwan ka” Ahmad yyi murmushi yace “Everything is settled now tunda ka amince”
Kafin karfe tara Jiddah tayi bacci bayan tayi wanka, Hijab din Aneesah dake gidan ya bata tayi sllh tun magrib. Abuturrab na xaune har sannan a parlor tare da Ahmad sae dai hankalin sa baya tare da Ahmad, bai yi tunanin Ahmad xai kai har 10 a gidan ba, Can dai Abuturrab

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button