FITAR RANA

FITAR RANA 2

Around 3pm na yamma saigasu kuwa sun iso,danta qasimu da matarsa da dansu taher wanda a shekaru bazai wuce ashirin ba,yaron kyakkawane na bugawa a jarida yafima iyayen nasa muhibba,yanada sigar mulki da kuma ƙasaita irin na wayayyu yan birni,shi tunda yaxo baiyi magana da kowa bama, Hannu bibbiyu iyayensa suka amshe zancen aurensa wanda aka ƙullasa bayan sallahn la’asar ranar jumu’a.a bakin masallacin Kofar mai kasuwan anguwan mahuta ..”Taheeeru Elqasim junaid da matarsa wasimé Aliyou denge Akan sadaki dubu dari da hamsin lakadan ba ajalan ba.,aure yaci darajar dumbin jama’ar gari sabida ranace ta cin kasuwar kauyen,da wanda yasansu da wanda baisansu ba kaf an halarta ankuma sakawa auren albarka.

Nan danan mata suka tada Yan raye raye da kade kade na al’ada guda ya cikka tsakar gidan kamar dagaske,kan kace kobo auren da akayi tsammanin yinshi cikin sirri da tsagaitawa saigashi yayi armashi har andanyi wasanni na al’ada antarawa amarya da ango kudi,Matsala daya aka samu kasancewar wasimé yar karamace batasan ma me akeyi ba,shekarunta tara ne kacal,shima taheer sam baiji dadin hakan ba a xuciyarsa dan baisan yaya xaiyi da wannan premature auren da aka musu ba,shikansa he is not ready to be a husband yet musmn ayanxu daya saka zancen karatunsa agaba,

toh inaga kuma yarinya ƙarama yar nine years wacce batama san zancen me akey ynzu ba,yasan wannan wani nauyi kawai aka dora masa,da kuma rainon ƴa wanda aka laƙa masa akansa,saidai shi mai tsananin biyayyane ga iyayensa, shiyasa bai nuna komi a yanayinsa ba,kuma yake biye musu a duk da wayewarsa da ajinsa hakan bai hana ya amshe batunsun hannu bibbiyu ba..besides kawai auren aka daura musu ,ba’ac su zamto tamkar mata da miji aynzu ba,saidai yasan ixuwa wani lokaci inta
Girma hakan zai iya faruwa,Nasiha kam sunshata awajen su innono da mutanenta da ta bawa waliyayyancin wasimé.

Yaga ba’aje koina ba har iyayensa sun kwallafa yarinyar aransu, jin cewa ita marainiyace babu uwa ba uba babu dangi sai innono.,innono tasa a hada auren da jininta ne sabida gudun hannun da wasimé zata iya fadawa ciki inta tafi ta barta awani wajen.

Yanzu da akay mata aure tun tana yar ƙaramanta ai zata iya zama a karkashin surukunanta harsai ta girma snn ta tare a dakin mijinta,
Sannan shima dahiru zai iya cika duk wani burinshi nayin karatu da zamowa duk abunda zai zamo kafin wasimé ta gama balaga ta mallake hanklin kanta,Koda bata sani ba, tasan dai rayuwar wasime na nan gaba bazai sangarta a hannun wani jininta ba.

Washe gari sassafe suka bar garin suka doshi hanyar cikin garin kaduna bayan an kammala komi na al’ada.
Innono da danta Qasimu da matarsa sai amarya da ango wanda haryanxu acikinsu wani baice uffan ma wani ba,ya zamewa taheer jiki shi baiya saƙe fuskansa da kowa,da wuya kaga dariya akan fuskansa ko murmushi zaiyi baxai wuce na gefen baki ba.

Shi wani irin murdadden mutum ne dabaison cikia magana bare zancen shirme,yana da ƙarfi da izza,shiyasa Arayuwansa
Yake mutuwar son yay millitary school ya dawo land army amma haka firrr iyayensa suka hanashi.

alhj Qasimu da matarsa
Sun nuna kamar likita kawai sukeso ya zamo,amma son da sukeyi wa dansu yasaka suka ƙasa yankemai babban burinshi na sob zama soja dan wani son zuciyarsu,Shima anashi fannin son dayake ma iyayensa yasaka ya ƙasa yankewa kanshi hukunci
Dan a duniya babu wani abunda yake tsananin ƙauna yake kuma darajawa kamar iyayensa

Kaunar da yake musu yasashi yafara pursuing careersa ta zamowa likita, amma likitan sojoji.

Wanda Yana kammala sec schl ‘dinsa at age of 16yrs ya samu scholarship mai kyau bisa kwaxonsa a NEET exams da suka zana na xuwa military school india,HPSP wato health profession schorlaship program ita ta dauki nauyinsa tana biya masa kudin makarntarsa harya kammala cos is just 4yrs alkcin,ynzu haka baifi wata biyu da dawowarsa ba,ynzu haka Mahaifinsa yana kkrin nema masa wata dama A “NAMC” nigerian medical millitary corps service,dan yayi 2yrs medical functions, wanda daya kammala zasu turashi can USU (uniformed service university of health) dats the national medical center is bethesta maryland,acan washintong D.C,inda zai ƙarkare karatun nasa sann ya dawo gida.

Dukkan wani jajircewa da tanadinsu arayuwa wa dansu taheer kawai sukeyi shima dukkan soyayyarsa da biyayyarsu naga iyayensa,sunada burin bashi ingatacce kuma tsaftacacciyar rayuwa dake shine kadai Allah ya azurtasu dashi a duniya
,Mahaifinsa al’Qasim baida wani sana’a face saida siyarwan motoci, ita mahaifiyarsa kuma malamar jamia ce amma yanzu tanata kokrine domin shiga matakin farfesa a fannin mecha-tronics and electrical engineering.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button