FITAR RANA 3

hahahaha Bilti ta kyalkale da dariyar yanayin maganan nata dayazo da yanayin barkwanci tace “kai kaka toh karki damu da wannan indan wannan ne ai zamu kula miki sosai da wasimé surutai innono ta cigaba dayi abunta,daga nan bilti batace komi kawai tajanye zanin gadon da wasime tay fitsari ta wuce bathrum dashi,ganin anbarsu su biyu ta riƙo kafadun wasimê data cuno bakinta gaba tanajinta tamkar wacce zata sakar mata kuka, “kema sai sime sime kike ban kayan toh in saka maki,tasa hannu ta fauce kayan,Riga da sket ne mai kyau na back of fish
Amber colour dinkinsu na karkara ba amasa style din komi ajiki ba,Sosai wasime ta tsane Saka sket a rayuwanta,ita tafi sabawa da riga da zani galau galau taganta Kamar yadda ta saba acan kauyansu a jos,wani langwame wuya tayi ta larne kamar zatay kuka,”Innono wannan matsatsen abun kika samin?,keyanta taji an dungure ta baya”ke kinci uwaki,ki tsaya ingama sakamiki tukun zaki gani bazai matseki ba,tafin hannunta takai saman fuskarta tana turo bakinta a shagwabe har innono ta gama sakamata kayan yai mata rass kuwa sabida tanada ginannen jiki ba ita tsiririya sosai bace”
“yawwa baga ki nan kin fito ba,innyeeeee gangariya tsiren mangu..wazai ganki ahaka fess yace katuwa irinki kina fitsarin kwance?,cikin gatse innono ta furta hakan tana hararta sabida ta tsare farfarun rikicinta dantasan wasime da naci akan abunda bataso yanzu saitasa acanza’ kayan nan,shiru wasime tay tana wasa da yatsun hannunta,kan gadon innono ta kalla snn ta kalli idanunta sai tafara mata magana ahankli Kuma cikin sigar lallami,yanzu fisabillahi wasimé saiki rasa abunda zaki kawo tsaraba a gidan surukanan naki sai fitsarin kwance?garinya akay haka..shiru tayi daga bisani idanunta ya cikko da ruwa ta dago muryanta a sanyaye tace
“Innono..ba laifina bane nifa Wani abu na dingaji yana fifitani cikin dare,sai naji kamar ana watsamin ruwa toh dana farka sainaga har waje ya jiƙa”
Wayyooo ahhhshh inno..no ..Kunnenta taji anƙama, sai kuma aka sake aka rungumeta sosai,ajiyar zuciya ta saki tanamai ƙara sakejikinta a kirjin innononta data kwantar da muryanta ƙasa kasa ta dada mannota da jikinta sosai,'”kinaji na ko?..toh karki ƙarayi ina gaya miki nan ba inda ya kamace ki da kiyi fitsarin kwance bane..nan fa gidan surukunaki ne kiyi musu biyayya kinji?..lafewa tay tanamai gyada kai childishly,jinta kawai take amma batasan komi ba, “ga nan BILTI zatana miki dukkan abunda kikeso,bance kuma ki sake jikinki ba,yadda kike aiki a gida can nan ma ki saki jikinki kiyi,nan ma gidane,inkina bukatar abu ki tambayeta kada kuma inji anyi kuka dake.
Ruwane suka cikko idanunta muryanta na rawa tace”innono wai barina anan zakiyine komi?ina zakije Ano?nide wallhy bazan zauna ba zan biki ..Ayanayin tausayawa tana kuma hararata tace “Sau nawa zan gaya miki da kizauna anan?hannu tasa a fuskanta snn ta fashe da kuka ni yaushe kika fadamin Kawai cewa kikay inshirya zamuzo binni Jiya naji kina cewa anmin aure,yau kuma shine zaki tafi kibarni anan wajen yoo akanme?ƙara sautin kukan tayi,innono cikin kyabe baki ta miƙe tsaye ta doshi kofar fita dan tasan batada amsar wannan rikici”ai saikiyi
Ni kinga tafiya,harta fara takawa sai kuma ta komo ta leka bayi lkcin bilti harta kammala dauraye bedding din ta fito dashi a bucket zatakai waje rana ya bugashi ya bushe,innono ta washe baki…”baiwal Allah bilti ni na wuce saduwar Alheri nagode nagode da dawainiya Allah yamiki albarka Allah yajikan magabata ,bilti tana murmushi tace karki damu kaka ai aikina ne.
Allah kaiki lpya ya kareki
Innono tace ameen,tana juyawa ta kalli wasime harta kammala hada jakarta ta runguma asigar bori,da sauri ta dauƙe ido kamar bata ganta ba tayo waje
Wanii fuuuuu wasimên ta biyo bayanta tafin hannunta bisa kan fusknta tanajin aranta kamar bazata ƙara ganin inonon ba,wani jan zuciyarta take dagske kamar wata mai aljanu idanunta na tara kwalla har ƙasa suka sauƙo cikin babban falon gidan,lokcin babu kowa a falon face Alhaj Qasimu da matarsa duk sun miƙe tsaye da shirinsu zasuyi rakiya wa innono,”matar gidan ne ta jawo hannunta tsakiya kowa na mata barka da safiya
Har suka kammala maganansu batace dasu uffan ba.Tana hankare da inononta,tana fita itama tabita kafa da kafa”Innalillahi wa inna ilaihi raji’un innono dan ALLAH karki tafi kibarni anan wajen.ni wallhy saina biki,ni wallh bazan zauna ba. Wayyyo Allah na na shiga uku ta tumu aƙasan tiles ta dora hannunta aka,innono na innono na wayyo innono nikam saina biki ..Acikin rudani da firgici ta furta hakan tana tsananta kukanta daya kufce mata bazata.Kuka kawai wasimê take babu kakkautawa kowa na kkrin rarrashinta
Innono kam ko ajikinta danko kallanta batayi baretaji tausayinta,
zamanta anan din shiyafi,dan wannan shine rayuwa mafi daraja da inganci data bawa wani wanda ta taimakawa arayuwanta,ta haɗa jininta da wasime aganinta tayiwa iyayen wasimé dukkan halacci da amanan daya dace ace tayi musu izuwa ynzu,acikin zuciyarta tana matkar kaunar wasimenta amma haka tayi kamr batasan anayi ba Allah Allah ma take tabar wajen “Suna fitowa waje wasimé ta bude sabuwar shafin kuka “wayyo Allah na,innono innono,innono zanbiki dan Allah zan biki,wayyooh Allah na kaf gidan saida ya dauƙa da ihun ta tana bubbuga kafafunta a ƙasa tana kuka sosai.,kusan hanklin kowa awajen saida ya tashi banda innono data cure bakinta sama tayi gum tasan sukam sabawane basuyi dajin kukan yaro ba barinma yaro mai rikici irin wasime,a sace ta kalle wasimen da’ gefen idanunta aranta ta kyabe baki ganin yadda ta turje anata fama da ita,dan kada kanta tay tace “zakimayi ki bari dan kuwa dolen ki ne ki saba da su ..”danta Alhj qasimu ne ya riko hannunta cikin lallami kiyi shiru mama na.baya taja cikin sheshhekar kuka tanacewa o o o o kanta take girgizawa tana rabza ihu tana kiran sunan innonon da ƙarfin balai,sosai hanklin matar qasim ya tashi ta rirriko kafadun wasime tanata son ta lallasheta amma duk hakan baisa tay shiru ba,sunai mata kallan yarinyane amma basusan aranta tasan mame takeyiwa kuka ba.
A Duk sanda innononta tace zatayi tafiya wani wajen dabaida suna toh tasan zata iya daɗewa sosai bata dawo ba.
Wajajen goma shaura anakan rikici da ita saiga taheer ya fito daga cikin gidan yana tfyarsa cikin sauri sauri da alaman baima san draman da akeyi anan ba.
murmurarren jikinshin nan yasha kwalliyar kananan kaya blue shit da black trousers data amshesa tamasa kyau. wani Sassanyar Qamshin turaren calvin klein dake tashi ajikinshi shiya mamaye iskan wajen wanda ya sakasu duka suka maida hankulansu kansa,yana tafiyane yana shan qamshi..idon kowa nakansa tsabar yadda rigimar tasa ke masa tsananin kyau. wasimé ce kawai batako kallesa ba dan bakaramin gunjin kuka takey ba ita kawai a kyaleta tabi innonon ta,tun daga stairs yaji ihun nata wanda hakan ya dada sa stern mood dinshi dada murduwa,he hates noise naturally bare ma ace kukan yaro ya tsane abun.,takunsa yakeyi yabi ya ƙara harɗe fuskanshi tam yanajin haushin yarinyar aransa wajen da akayi parking motar da zai kai innono kawai ya dosa,Innono da tayi tsinin baki wani jan ajiyan zuciya tayi dataganshi daga nan gyara tsyawurta tayi tana matsowa kusa da inda yake tana surutai”toh Alhamdullh shikenan ma aigama ɗaheru ya samu fitowa ni kunga tafiyata toh qasimu sai anjimanku Allah shi albarka,cikin sauri ta haubinshi abaya baya
Alhaj Qasimu ya fidda kudi mai dan yawa ya bita har wajen motar kudin yakai dubu biyar haka ya damƙa mata a hannu nashan ruwa a hanya,matarsa ma haka ta bude jakarta ta debo sauran canji ta bata duka da tausayinta a cikin idanuwansu,ba abun su rakata har tasha ba suma sauri suke zasu fita.,hannun wasime matar ta rike tam duk dama sai dukan hannun take tana tuma akasa tana ihu tana firgici.
Daga cikin mota innono ta soma ƙirar “bilti, “bilti,.,bilti tana isowa ta fito ta dauke wasimen cak ta miƙa mata ita a hannu sabida cikamasu kunne da takeyi,cikin masifa tanacewa”marar kunya kawai,ki wuce cikin gida da ita Intagaji ai zatayi shiru,da kyar bilti ta kamota ta riketa tana fifficikewa..inno zaki tafi kibarni? Bata kulata ba ta juya tana sassaka ma su qasimu da matarsa albarka wani irin horn ya danna da mugun ƙarfi da alaman kukan nan kam ya isheshi.da kyar bilti take janta,mota na tashi ta fincike da gudu ta hargitso ta wajen motar tana kokarin itama zata shige cikin aikuwa tana dososu tsigar jikinta ya wani tashi sakamakon wasu dararan idanuwan sa masu ban tsoro da taga sun tsareta masu mugun firgitarwa,
“KE!! kibace min anan wajen..a mugun razane taja da baya ta tsaya dan kamar an hanƙadata haka tsomare waje guda