FITAR RANA

FITAR RANA 3

gunjin kuka tacigaba dayi tana kallon bakinsa daya furta mata hakan wnda kamar bada ita yay ba.Tunda suke dashi sai yanxu wata kalma ta shiga tsakanin su,wani irin muguwar tsoronsa taji ya shigeta a take,tana kukan aranta tana magana tace wannan wani irin mutum ne mai ban tsoro.

Wani shiru wajen ya dauƙa bayan ya tada motar ,jan motarsa yy a fixge sanda duka suja razana,wasime ta ƙara ja baya a firgice..

hararshi innono tayi sabida sam batason rashin mutunci irin nashi,itade taja Allah ya isa in Advance dan bazata lamunci adaka mata yarinya ba tasan daheeru tsaf zai iya zane mata ƴa. mahaifyarsa tana dan murmushi tacr “anono Allah ya kare,Alhj qasimu duk suka daga mata hannu,suna fita a gidan innono tahau matse idanunta tana daga musu hannun itama cikin yanayin sacewar jiki, dan ita saiyanzu ma taji tausayin wasimen ya shige zuciyarta,Allah sarki wasimé.gashi basuyi wani doguwar xama ba kwata kwata shekarun nata tara ne kacal tayi mata aure,murmushin tasu ta tsoffi ta saki tana goge idanunta da bakin zaninta,duk abunda yakeyi taher yana lura da ita,wani tagumi ta rafka ta yamutsa fuskanta shikenan tasan hala kafin ta dawo hala har wasiménta ta ƙara girma daheeru ya maidata matarsa ,yoo koma zataxo taso shi?inshi yaxo baisonta fa!!. duk dai tunanin shiirme suka soma dagula mata kwakalwa tayi wata lakwas da ita tana sauƙe ajiyan zuciya.

sun bar gidan da kamar minti tara baice mata uffan ba ya kunna music a motar wakar sean paul get busy yasaka yaba bin lyrics din da kadan kadan..
Daga can gida kuwa biltice tay kkrin janye hannun wasime suka nufi cikin gidan wanda bacin razana datayi wani sabuwar shafin kuka da bori ta ƙara budewa, tun suna rarrashinta har suka gaji suka kyaleta,haka kowa ya fice akabarta agidan daga ita sai bilti dan tana kulawa da ita
ƙarshenta basuji sakat a kunnensu ba har saida wasime ta samu tayi bacci danko abinci taƙi sam tasaka abakinta.

Bagaren su innono kuwa har suka isa kai tasha bata dawo daga tafkin tunanin shirme data shige ciki ba,wani irin horn mai ƙarfi yay sanda ta firgita taja innallalhi a firgice sann ta dawo hayyacinta baki bude take kallonsa Babu halin yin masa magana sabida waƙar daya cikama mata kunne dashi,katon wajene mai dauƙe da yan union da fasinjoji anata hada hadan tafiye tafiye,adai dai gaban motar kauyen dazataje in yashawo kwana daf gaban wata rumfa yay parking snn yy lowering music dinsa..kansa ya maida baya ya jingina da seat ahankli alaman yana jira ta fita.nan da nan Saiga masinjojin tasha sun iso,malama tafiya ne?ina za’a kaiku,innono sai sime sime tanayi tana waiwayensa wato daheru bazai ko tanka mata ba, wani irin nauyi zcyrta yay sabida bakinta cikke yake da maganganu datake so ta masa musamman akan wasimé, zuciyarta sai halbawa yake shiko ko ajikinshi yana zaune yana jiran ta fita. saiynzu taji ta bala’in damuwa tana sonjin ra’ayin shi akan auren,tanaso ta kuma ji tabbacin amincewarsa akan auransa da wasimé daga bakinsa,waswasi duk ya cika mata kirji karfa suga tun suna yara ƙanana anmusu auren gata sudauƙa wasa ake musu ko aure bai dauru ba,in de balaga ne ai dahiru yanxu kam ya balaga,a kiyasce tasan yakai shekaru ashirin ai shikam ma ya isaa aure,..saoin sa a karkara yayansu nawa?wasime ne ma za’a ce batasan metake ba yanxu saita ƙara girma,amma tana fatan ratan hakan bazai sauya alaƙarsu ko matsayinta agunsa ba,shikam gani take kamar ko ajikinshi tuni yy buris da batun.,ta dade cikin zurfin tunani bata hankara ba tagansa a waje “glass din gefenta yay winning snn ya bude mata ƙofa yace toh mun iso saiki sauƙo ko,a hankli ta dago tadan saci kallonsa ,wai ahakan ma itace kawai takan iyayi dashi iyayensa kam duka sun sangartashi basa son masa fada sai abunda yace dadin abun dai kawai yanai musu biyayya mai tsanani shiyasa bata damu ba

Ƙamewa tay cikin kkrin nemo nitsuwa makanta
Ta kallesa cikin karfin hali tace “kai Dahiru kozan iya magana dakai?..shiru yay
Can snn ya dago ya dubeta yace miye ne inajinki..zata bude baki ya tsareta da haraara”kiyi sauri ni ina da inda zanje..wani numfashi taja babu bata lokaci tace dama Akan maganan auran nan ne dahiru kaji tsoron Allah .Hannu ya daga mata Alaman ya isa
Cikin lumshe ido da buɗewa alaman baison jin maganan yace”Kije dan Allah ai naji!!..kada kanta tayi ta sauƙo kasa idanuwanta nakansa tanamasa wani irin kallo mai nauyi dauke kansa yay akanta ya mayar gefe saiga nan yaran motan shayibu sun dosu su.

kayanta suka hau debawa suka kai mata har bayan mota suka sassaka matasu.tana samun wajen zama a motar taji kamar tsayuwar mutum ata gefen windonta tana waiwayowa kuwa taganshi a tsaye da wani abu ya dunƙule a hannunsa suna hade ido ya jefo mata ajikinta yace”toh ga wannan kisha ruwa dashi. budewa tayi da mamaki a fusknata taga dubunan kudi zasukai dubu goma sababbi kal kal wanda ko iyayensa basu bata irinsa ba ,murmushin baxata ne ya kufce mata tace toh masha Allah nagode dahiru Allah ya saka da alheri nagode ka kula da amanar da nabar maka kaji?Allah ya maka albarka,baice uffan ba ya juya ya nufi inda motarsa take abunsa.

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button