Labarai

RAYUWAR MUNEERAT ABDULSALAM: Darasi Ga Safara’u Da Rahma Sadau Da Ire-irensu

RAYUWAR MUNEERAT ABDULSALAM: Darasi Ga Safara’u Da Rahma Sadau Da Ire-irensu

Daga Imam Indabawa Aliyu

Na ga rubutun wata shahararriyar mata mai suna Muneerat Abdulsalam wacce ta ce ta yi matukar nadamar munanan ayyukanta da ta yi a rayuwarta, a halin da take ciki ta ce ba ta da ko kudin siyan paracetamol wanda hakan ya sa take rokon al’umma da su taimaka mata.

Muneerat dai ta yi kaurin suna wajen bidiyon batsa da yada hotunanta masu dauke da shigar banza sai dai zuwa yanzu tuni duniya ta yi mata atishawar tsaki domin ta yi Allah wadai da karuwancin da ta dinga yi a rayuwarta tana mai cewa rayuwarta kadai ta isa ta zama darasi ga masu hali irin nata.

Muneerat Abdulsalam

Wannan ya isa darasi ga irinsu Safara’u da suka kulla abota da shaidan suka tare a bariki da wani dan iskan yaro mai suna 442 suna iskanci da fitsara iri-iri. Hakika duniya abar tsoro ce, duk abin da mutum ya shuka sai ya girba.

Haka yarinyar nan mai suna Rahama Sadau babu irin fitsarar da ba ta yi tana shigar banza ta dora hotunan a media, idan aka yi mata nasiha har izgili take wai ai gonarta ce, a bar ta ta girbi abin da ta shuka. Saboda fitsara na yarinyar nan har fitowa ta yi ta ce wai ita ba cikakkiyar budurwa ba ce ta riga da ta rasa budurcinta tuntuni kuma ba ta hanyar aure ba. Wani labarin ma da na gani wai an ce ta ce ba ta san adadin cikin da ta zubar a jikinta ba kuma har alfahari take ko a jikinta. Ga wata nan ma mai suna Nafisat Abdullahi da sauransu suna amfani da yaren Hausa suna koyar da shigar banza. To lallai Allah abun tsoro ne idan ya tashi kama mutum ba zai ji dadi ba, don haka gwara mutum ya yi amfani da damarsa ya tuba ya koma aikata ayyuka masu kyau.

Sauran ‘yan matan fim masu shigar banza suna lalata tarbiyya wadanda suka fake da fim suna karuwanci mai lasisi suna rike manyan wayoyi da hawa manyan motoci, kuma suna zuwa kasashen duniya yawon shakatawa duka wannan ya zama darasi a gare su. Karuwanci ba abu ne mai kyau ba, kuma mai aikata shi ba zai sami yadda yake so ba. Wasu daga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni na ba su makudan kudade suna kwanciya da su. Idan muka yi musu nasiha sai su ce hassada ake musu wai saboda Allah ya daukaka su. Duk facaka da kudin da suke yi lallai Allah ya yi musu talala ne kafin ya kama su. Bariki babu riba a cikinta sai tarin nadama da azaba.

Allah ya sa wannan lamari ya zama sanadin shiriyar Muneerat da sauran masu hali irin nata. Allah ya shiryar da mu ya sa mu yi karshe mai kyau.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button