FITAR RANA 5

Take ya lumshe idanunsa yafi tsawon mintina biyu yana kallon setin wajen da karar ke fitowa wai wannan wata irin yarinya ce?fahimtar cewa wasime ke wannan ihun yasashi kara shan mamaki aransa,can snn ya dauke dara daran idanunsa dahar sun soma sauyawa kalarsu izuwa na bacin rai yanada gajen hkri abu kadan ke triggering nashi ,ajiyar zuciy ya sauƙe snn ya koma ya jinginar da kansa akan kujerar dayake zaune very calmy yanamai sauke numfashinsa a hankli calming himself down dan dole cos honestly bayason yana raxana ta duba da health condition dinta.
Ihun yaki ci yaki karewa,tsawon mintina yana matse kansa domin karya tashi amma ina lumsashun idanunsa ya wara snn ya miƙe tsaye uwa an tsakureshi yayi hanyar saman agaggauce, inda suke ya dosa direct.Ya tarar ƙofar tasu ma a bude take tun dagacan yake kallon yadda ake kokowa da wasimén wajen hadiyar magani sam taki hadiya tana ta aikin rabza kuka,tun kafin ya karaso wajen ya wani hade ransa ya murtke fuskansa,agaggauce yake dosowa wajensu
Kamar wani mayunwacin zaki,Bilti tanata Allah Allah kar wasimé ta jiyo ta kallesa dan tasan tabbas intagansa zata ƙara tsorata ta sum,mum dinshi ne ta zuba masa ido tun daga can alamar karya ƙaraso ciki amma yy kamar bai ga alamar datakeyi masa ba,
yana karasowa cikin shakakkiyar muryansa mai ban tsoro da daka tsawa yace..”salama alaikum..wani yarrrrrr tsikar jikin wasimé ya tashi..take kwakwkalnta ya tsinkayo mata sautin muryanshi mai ban tsoro bata tabbata ba saida ta ji yana tambayarsu su bilti “meke faruwa ?aikuwa tana dago kanta caraf sai suka haɗe idanunsu taga yana hararta da wani irin sigar fushi ransa a bace yana huci kamar zai hadiyeta
Dakewa yayi snn yace
“Ke?me aka miki kike mana ihu?..
Jikinta atake yahau bari tarasa mema zatace masa ta riga ta raxana tsoronta ma karya ƙara daka mata tsawa..wani irin kallo taga yana jefo mata tay saurin sunkuyar dakanta ƙasa”luiii idanunta sukayi tamkar xata zube ƙasa bilti tayi sauri ta dauketa cak ta rungumeta wani irin azababben kuka mai dauƙe da tsoronsa ta saki…