FITAR RANA

FITAR RANA 6

..”alhj Qasimu ya tsuguna agabanta cikin sassauto da muryan sa ƙasa shima”toh me kike so a kawo miki ƴata?kifadamin koma miyene Ni Zan kawo miki..kanta ta kife tsaknkanun cinyarta ta sake kukan datake dannewa dagaske gwanin ban tausayi, cikin shehsheka mai zafi tace”Nide ka kaini wajen innono na dan Allah..
murmushi yy iya abunda kike so kenan?Cikin kukan ta gyada kanta da sauri tanajan majina.matarshi ce ta matso kusa daf da ita shima tashi yy ya zauna daf da ita yanamai dage kanta dakansa har sanda suka hade idanunsu waje guda dashi”kallonta ya shigayi itama tana kallansa,idanunta duj sunyi jajur tsoro duk ya kama zcyrta sosai ya nakasata.sosai tausayin ta ya kama zcyarshi,

muryansa dauƙe da salon lallami wanda ya fi na da yace “kinaji ko?kwarjinin sa yasa ta gyada kanta a ladabce Yace”nida kaina zan kaiki Wajen Anono inhar zakiyi duk abunda zamu ce kiyi agidan nan…Ga matata nan,ga kuma bilti akwai ɗana dahiru agidan nan karkiji tsoronsa,shi yawan kukane kawai bayaso amma yanada dadin zama zaki saba dashi sosai,kedai kizauna da mu kiyi musu biyayya..musamman ma dahiru..nikuma sai inga ko kincancaci in kaiki wajen anononki!!

shiru tay kamar bata fahimce shi ba sabida magana yay mata a nitse kamar yana magana da wata babba wacce ta mallaki hanklin kanta.Haka ma matarsa ta sako baki tana mai ƙara lallabarta hardai ta samu nitsuwar zuci sosai tayi shiruu tanajinsu sosai da sosai
,sun dade a dakin suna kkrin shawo kanta tazauna din
,maganganunsu kuwa sosai yy tasiri a zcyrta halinka da yaro tadauka dagsken suke intayi abunda sukace din dagske zasu kaita wajen anono,daga nan bata ƙara wani fitina ba.

Fannin tej kuwa tunda ya shiga dakinsa ya sauƙa akan tebirin karatunsa yama manta da cewa wani abu ya afku dazu,halayyarsa ne shashantar da abu cikin sauƙi,he is so self absorbed nd discplined in harkan gabansa ya taso mai kusan mancewa da komi yakeyi a duniyar nan shiyasa zakaga kamar babu abunda yake iya shiga ransa bare ya damesa.

A ranar bai fito ba sai washe gari da sassafe,7am ya dawo daga wajen motsa jiki ya samu kowa ya hallara wajen abun ƙari kamar yadda aka saba hanklinsa ne ya kwanta sosai da baiga wasime anan din ba,waje ya samu ya durkusa adan gefe ya gaida iyayensa cikin ladabi da biyayya sannan ya haura sama yakimtsa kansa ya dawo cikin shigarsa ta kananan kaya,a nitse yanemi seat ya zauna ya fara cin abinsa kominsa a nitse faten wake ne da miyan dage dage na manyan manyan kifin tuna,iyayensa dake zaune awajen basu wani takuramai da wani magana ba harsaida suka tabbata yaci abincinsa ya koshi.

hamdala yy zai miƙe tsaye kenan mahaifinshi yay gyaran murya snn ya kirawo sa. dawowa falon yy ya nufi inda suke zaune ya same su duk dama Tafiya yake kamar baxai karaso ba dan yanajin ance “son i want to talk to you”..yasan doguwar nasihace ke jiransa, atake yaji kamar ciwon kai yakamasa.

fuskansa adan takune ya zauna dan yagama sanin akan meye ne za’a yi maganan bai wuce akan wacan yarinyar ba da baison fitinarta..

idanunshi a kankance ya zauna tare da nitsewa, kansa na ƙasa can dan ma karsu fahimce rashin intrest dinsa akan topic din,as xpected nasiha iyayen nasa suka dinga masa akan yabi wasimé ahankli yarinyace,wani bin saiyaji kamar ma wasiyya ake bashi akanta,shidai tunda suka fara maganan su yana shiru yana sauraran su bai tanka ba har suka kammala snn yace musu yaji,daga nan yay musu sallama ya tashi ya fita.

Haka rayuwar tasu ta kasance harna tsawon kwanaki goma amma babu abunda ya sauya a fannin wasimé don sosai ta kasance acikin yanayin zazzabi da damuwar da ta cusa ma ranta da tsoran taher datakeyi..ji take kamr komi ya cirke mata musammn shegen sanyin a c wanda bawai ta saba da shi bane inyana kadata cikin bacci sai taji ta daban wanda hakan yasaka tafiye yin fitsarin kwance,kullum ta farka ta dinga rakube rakube kenan tana bobboye jikinta dan kunya,gashi ba su fara barinta tanayin komi ba,bilti ne take tsaftace ta fes.kusan ako wani rana zatayi mata wanka ta wanke mata kayan datayi fitsarin ta shanya su a rana,ahankli har wasimé ta zo ta fara samun sauƙin jikinta.,
saidai tsoron taheer shaf yanahata motsawa daga cikin dakin kullum tana kumshe kamar wata amarya,haryau gani take kamar inta fito zata ci karo da shi wanda a yanzu bata sani ba shi harkan karatunsa kawai yakeyi.

kwance tashe ba wuya bayan wata guda wasime ta fara sabawa da bilti ta kuma soma sake ranta da kadan kadan tana dan saukowa tana biyota su fito har kitchen tana tsaye agefe haka har bilti zata kammala ayyukanta subi su dawo daki tare.

Yau asabar antashi da haddari sosai,karfe 6 saura wasimé ta farka a bacci duk ta jiƙe jikinta da fitsari,kamar zata saki kuka take kallon sket dinta, Ganin bilti bata shigo ba yasata saurin dirowa ƙasa cikin sauri ta wuce bathrum ta cire kayan jikintan duka snn ta dora sabon zaninta a kirji.,dauko bucket tayi da omo ta tattaro kayan datayi fitsarin bata tsaya koina ba sai bakin famfo dake can waje,lokcin koina shiru babu wani mahaluki a tsakar gidan.

a hnkli take takawa tamkar wacce bataso aji karar sautin tafiyarta harta isa bakin famfo,aje bucket din tay da sauri abakin tap din sann ta kunna ruwa ya fara zuba shaaaa ta tara acikin bokiti,dan kadan ta saka omo acikin ruwan sann ta kada yay kumfa sosai,a nitse take tsoma kayan tana shafawa a hankli saida tafi awa abakin wajen tana abu guda,wani motsi ta faraji ata bayanta,haka kawai taji ta raxana da motsin duk tsoronta gamuwarta da taher ne,cikin sauri ta tsane hannunta tana dago kanta kuwa sukayi ido hudu da tolu. ajiyar zcyane ya kufce mata as usual tagansa ne ayayin da yake sanda tare da wata yarinyar daya kwana da ita a dakinsa.

baida kunya sai famar shafa kugunta yakeyi yana lallashe bakinsa
,halinka da yaro wasime sai ta zuba musu ido tana ta kallonsu bata dauƙe kanta akansu ba har suka bace ma ganinta”yarinyar ce ta soma hankara ta nuna ma tolu wasime..yana kallonta tana kallonshi
,acikin sauri tolu ya tura yarinyar waje ya rufe kofar gidan snn ya dawo ciki cikin gaggawa,bakin famfon ya nufa inda wasimen take durkufe tana shafa kayanta dan tsawon lokacin nan bata taɓa magana da ma’aikatan gidan ba sabida tsokanrta da sukeyi sonyi akan yawan kukan datayi farkon xuwanta..

ya dade akanta yana tsaye amma kota kulasa,sai juye juye take duk yarasa yadda zai tambayeta yaji kota fahimce abunda ta gani ynzu,tsoronsa karfa ta je ta tona masa asiri,ta gabanta ya dawo inda zai kalle fuskarta da kyau, tsantsar kyaun halittar fatarta ne ya soma dauke masa hankli haƙika shi kansa
Bai taɓa ganin baƙin fata mai kyau irin na wasime ba,babu dandanin tabo ajikinta gashi sai sheƙi fuskarta yakeyi, gyaran murya yy da ascent dinsu na yarbawa yace”Iya rigimou,.tanajinshi ta basar sanda taja masa aji can snn ta Dago kai ta wani kallesa..”washe bakinsa taga yanayi yace..”kai yarinya meya kawoka nan wajen dis hearly morning,bilti nko?..bata wani fahimce mai yace ba dai ta dauke kanta snn ta amsashi
‘Nima bansani ba wanki nakeyi”snn tacigaba da abunda takeyi.

Durkusawa yasoyi agabanta yaga tayi maza tabar wankin ta miƙe tsaye tana hararsa
“nika tafi wanki fa nakeyi”..da kallo yabita snn ya miƙe tsayen shima yana mamkinta aransa yace Ashe tana magana har haka?

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button