FITAR RANA 7

Amma Saboda fitsarin kwancen nan yasaka duka wani kuzarinta ya gushe agidan,kallon kanta take kamar wata kazama.
kunyar bilti takeji aboye har cikin kokon ranta tanajin nauyi shiyasa kawai ta yanke hukuncin wanke kayan fitsarinta dakanta Basai an wanke mata ba.
Duk shiyasaka bata son fitowa bare ta samu kyakkywar fahimtar juna tsakaninta da surakunanta gani take kamar izuwa ynzu duk sun san tana tsula fitsarin kwance,abun nasaka taji kunyar kanta bakadan ba.
Washe gari jumu’a da alaman yau babu kowa a gidan,bilti ce kawai a kitchen alhj qasimu da matarsa sun tafi ikko dansu basa wani zama.
Kirjinta na mata ciwo yau haka ta farka a bacci wani iska mai sanyin gaske ne yake kadawa yana ratsata har cikin kasusuwanta tanajinshi
,mikewa zaune tay akan gadonta snn ta kama handle din windown ta leka kadan ganin gari ya rufa,lekewa ta dadayi taga wani bakin haddarine a sama Cikin sauri ta ja windown ta rufe sabida wani iska mai ƙarfi daya busota hancinta.Tana kammala rufe windown ta sauƙa kasa ta tattara inda tayi fitsari snn ta nufo waje.
Ko takalmi bata saka a kafafunta ba tashiga saukowa ahnkli cikin sanɗa zatayi waje,kwata kwata batason bilti taji motsinta a sanyin nan tasan bazata taba kyaleta ta fita ba,ita kuma batason tazauna da kayan fitsari a daki mostly shitake fara kawarwa snn tayi alwala duk hanata da bilti takeyi amma batajin magana.
Yauma babu motsin kowa a waje ita kadai Tana durkufe agaban tap tana wankinta as usual tanata shafawa kamar wacce batada jini ajikinta,gabanta ne taji ya fadi,barin wankin tayi a hnkli snn ta juyo tana dago kai kuwa suka hade idanuwansu waje guda da wani kywkkwan saurayi wanda tunda take arayuwanta bata taɓa ganin mai irin kamanninshi ba.