SULTAAN 19-20

???? *S U L T A A NMss Flower????
*FITATTU HUƊU????
_RESEMBLANCE OR SIMILARITIES OF STORY/LIFESTYLE SHOULD BE CONSIDERED AS TOTAL COINCIDENCE_
*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*
*19-20*
AST FREE PAGE*
A tsorace ina kallonsa ina kukana, lumshe idanunsa ya yi tare da dafe kansa ya yi baya tare da zama, ya jima a haka, Ni ma kuma ina nan yadda ya bar ni sai kukana nake tamkar wadda ake wa zarar rai, zuwa can ya miƙe tare da nufo ni, tsugunnawa ya yi tare da kama hannayena ya lumshe idonsa tare da cewa “it’s okay” in a very cool voice.
Kukan nawa ban san dalili ba sai ya ƙara yawa, na kifa kaina saman cinyarsa ina rerawa, hannunsa mai faɗi ya ɗora ya shiga bubbuga bayana yana cewa “kukan ya isa” cikin muryarsa mai sanyi
A hankali na ɗago kaina cikin shagwaɓar da ta zame min jiki na ce “me ya sa ni ka tsaneni ne?”
Girgiza kai kawai ya yi tare da tashi sannan ya ɗagoni muka koma bakin gadon muka zauna, jingina kaina na yi a kafaɗarsa ina sauke ajiyar zuciya kafin na ce “ba ka amsa ba”
“It hurts!” Ya ce a sanyaye
“Me?” Na ce idona a kansa, bai bani amsa ba sai murmushi kawai da ya ɗan yi.
Gane ba ya son magana ne, sai na yi shiru na cigaba da jan ajiyar zuciyata, har lokacin bacci ya yi muna tare da shi, don bayan mun gama cin abinci farfajiyar wajen muka fita ina ba shi labarai na almara.
Washegari ina cikin kitchen na ji an dafani, a zabure na juyo don ban ji taku ba, tsaye na ga Prince Wahid sai dai fuskarsa babu alamun walwala, da gani yana cikin matsananciyar damuwa, hannuna kawai ya kama ya fara ja na.
“Ina za mu?” Na tambaya, amma bai bani amsa ba har muka ƙule ƙaton lambu da yake da ƴar duhuwa, cikin tashin hankali ya turani jikin bango idanunsa sun yi jawur wanda hakan ya matuƙar tsoratani na ce “me ke faruwa ne?”
Ya tsuramin firgitattun idanunsa da suka yi jaa sosai sannan ya ce “Zeena ina sonki, ki aminta da zuciyata, zan miki gatan da ba a taɓa miki shi ba, zan ɗaukaka darajarki, zan kuma fito da hasken tauraronki, ki aminta da ni, na rantse sai kowacce mace ta yi kishinki!” Ya ce idanunsa cikin nawa.
Kasa wani ƙwaƙwaran motsi na yi sai kallonsa da nake cike da mamaki haɗe da tsoro.
“Ki ban amsa! Kin amshi zuciyata ne ko a’a?” Ya ce cikin faɗa
“Wai me yake faruwa ne?” Na ce ina kallonsa cikin ƴar jarumtar da na tattaro.
“Ina buƙatarki kamar yadda kike buƙata ta, na gaji!, Ba zai yiwu a ƙwace min abin da na saƙala rai a kai tun ina ƙarami ba, abin da ya zama mallakina ba zan mallakawa wani ba, sai da ke zan iya ƙwace abuna da ake shirin mallake min, mu amfana da juna, ki taimakeni, Ni ma na miki taimakon da duk duniya Ni kaɗai zan iya miki shi” ya ce a sanyaye
“Ban gane ba” na ce ina duban yadda duk ya haukace yana surutan da ban ma gane inda suka dosa.
“Komai na ce miki ki yi, komai na hana miki ki hanu, komai aka yi a gabanki ki kauda idonki ki koma makauniya, haka komai kika ji ki koma kurma kuma bebiya, in kin yi haka na rantse sai kin fi kowacce mace daraja da ado a *WHITE PALACE* Zan wadataki da suturu na alfarma, zan baki dukkan wani ƙyale-ƙyale na duniya, kowacce mace za ta dawo ƙarƙashin ikonki a wannan masarauta, me kika ce?”
Sosai na din ga jujjuya maganganun ina son gano inda ya dosa amma na kasa, sai dai zuciyata sosai ta kwaɗaitu da tarin alƙawarukan da ya ɗaukar min, a hankali na ɗaga kai na kallesa na ce “na aminta, sai dai abu guda ne ba zan maka ba, ba kuma na so ka kuma roƙo ko tambaya akan sa”
“Mene?”
“Zuciyata! Ta mutu tun a lokacin da mammalakinta ya bar duniya, abadan babu ni babu soyayya, in ka aminta da sharaɗina kuma za ka cika alƙawarrukan da ka ɗauka na aminta da dukka batunka”
Ya saki wani murmushi ya ce “an gama!”.
Haka na juya na koma sashenmu ina ta jujjuya maganar don sam na kasa gane manufarsa amma kuma lallai ni ɗin ai me daraja ce, dole na aminta da dukkan batunsa ko don tabbatuwar burina na ɗaukar fansa akan wanda ya cutar da Ni, ya ja min asarar rayukan masu soyuwa a gareni. Babu ɓata lokaci na kwashe abincin da ya riga ya nuna na nufi wajensa da shi, zaune na taddasa ya yi kyau sosai, yana tsaye bakin window yana kallon tsuntsayen da ke ta tsalle da wasansu, murmushi na saki tare da cewa “ga abincinka”
Ya waiwayo da kyakyawar fuskarsa ya sauke a kaina, sai ya sakar min wani murmushi wanda ya sa zuciyata ta shiga harbawa da mugun gudu, na yi saurin sauke kaina ƙasa, takowa ya yi har inda nake ya kamo hannuna cikin lallausan hannunsa sannan ya ja ni har gaban window ɗin, nuni ya yi min da wata ƙaramar tsuntsuwa da ke ta koyon tashi mai matuƙar kyau, in ta yi firrr ta tashi ɗaya biyu sai ta faɗi, sosai Ni ma ta burgeni na kuma shiga dariyarta don ta ƙi haƙura da gwada tashin, sosai nake dariyata akan lamarin tsuntsuwar cikin nishaɗi, idona na sauke akan sa yana ta kallona tamkar ya samu abin burgewa, sassauta dariyar na fara yi, murmushi ya ɗan yi min tare da jan hannuna zuwa wajen da na ajiye abinci, serving ɗinsa na yi na koma gefe ina satar kallonsa, rungume hannayensa ya yi a ƙirji alamun ba zai ci da kansa ba, hakan ya sa na ɗauki bowl ɗin na ɗebo a spoon na kai bakinsa, girgiza kai ya yi tare da min nuni da kaina da kansa, fahimtar yana nufin na fara ci ne ya sanya na kai bakina na ɗan ci, sannan na kai bakinsa, haka muka shiga cin abincin duk da ba na kirki nake ji ba don wani nauyi da kunyarsa nake ji ban san dalili ba.
Da yammaci na fito ɗibar ruwa a ƙatuwar rijiyar da ke cikin gidan mai wani irin wawakeken baki kuma mara tudu, dalilin ruwan famfon da ya ɗauke, da ƙyar na ja guga ɗaya sai haki nake don ban taɓa jan ruwa ba sai a yau ɗin, hasalima ko a kogi wasa ke kai Ni ba dai ɗibar ruwa ba don ni *ƳAR SO* (na Mss Flower????) a gidan namu. Ina ajiye gugar sai haki nake na ɗago idona ya sauka akan sa, murmushi ya sakar min tare da saka hannunsa zai amshi gugar, da hanzari na girgiza kai na ce “a’a”, bai ce komai ba sai kallona da yake kafin ya kuma yunƙurin karɓa
“A’a ba ka da lafiya” na ce ina kallonsa a tsorace.
Lumshe idonsa ya yi tare da ɗaga min kai ya miƙo hannunsa alamun zai iya na ba shi gugar, hakan ya sa na miƙa masa, zurawa ya yi tare da janyowa babu ɓata lokaci, take ya cika min ƙaton tulun, cikin jindaɗi na ce “na gode, bari na juye na dawo, sai a ƙara ko sawu ɗaya ne gidan babu ruwa”
Lumshe idonsa ya yi tare da gyaɗa kai.
Ɗauka na yi na nufi gidan tare da juyewa a ƙatuwar tukunyar ruwa sannan na fito zuciyata cike da nishaɗi, wata ƙara na ƙwalla yayin da na ga Prince Wahid ya hankaɗa shi cikin rijiyar ya kuma tafi cikinta, tulun faɗuwa ya yi jikina ya ɗauki kyarma ina girgiza kai, gani nake kamar mafarki, wata zabura na yi tare da son nufar wajen, ta bayana na ji an riƙeni tare da rufen hanci da ƙyalle, take na fara ganin wani irin buji-buji, ƙafafuna suka shiga kyarma, yayin da nake miƙa hannuna ina kallon rijiyar da ta koma kusan guda ɗari…
*NA DAKATA A NAN!*
*YA LABARIN SU AMMA, ABBU DA HALIME?*
*YA LABARIN SULTAAN DA YA FAƊA RUWA?*
*YA LABARIN LAILA?*
*YA HAƊUWAR SULTAAN DA ZEENA ZA TA KASANCE?*
*SHIN HINDU ZA TA HAƘURA TA ƘYALE ZEENA NE?*
*WAYE WANNAN ƁOYAYYEN ƊAN SARKIN?*
*WA ZAI CECE SHI, YA KUMA CECI ZEENA CIKIN WANNAN HALIN?, KO ZA SU RASA RAYUKANSU?*