HAJNA 9-10

*Bismillahir Rahmanir Raheem*
PAGE 9-10
Wannan page ɗin sadaukar wa ne gare ki Nana khadi ❤️❤️❤️❤️ma rubuciyar almajiri ko attajiri, Allah ya ɗaukaki ya ɗaukaka Alqalami min ki, wannan page ɗin naki ne ke kaɗai ex mom????????????????????, kiji daɗin ki.
***********************
Bayan kwana huɗu, Fahna da Alhaji musa suka shirya tafiya, in Qaseem ya ɗauki dubu ɗari biyar ya bata kyauta, tafiya suke yi a mota suna fira, “wai dan Allah Alhaji Qaseem da gaske yake yi da yace zai bani kyauta kuɗi da mota? “, Fahna ta tambayi Alhaji musa cikin firar da suke yi, kallon ta yayi sannan yayi murmushi yace “har abunda yafi haka zaki samu in dai Alhaji Qaseem”, jinjina kai Fahna tayi, idon ta fal cike da tambaya, Alhaji Musa yace “can da kike ganin shi, ɗan iska ne na ƙarshe, idan ya sauke ido akan mace baya ɗaukewa “, Fahna tace “wai wannan gidan sa ne”, “ƙwarai kuwa, Qaseem da kike gani babban Alhaji ne, yana da kuɗi amma yana ɓoye wa, wata ma’aikata yake aiki, amma yana ɓoye musu koshi wanene, saboda ɓoye asalin sunan ahalin shi “, Fahna tace “amma miye ribar shi na yin haka”, Alhaji Musa yace “nima fa ban sani ba “, Fahna tace “to ina iyayen shi suke”, Alhaji Musa yace “ai baya da su, yana da yaya mace, kuma ba musulma bace, yana zuwa gurin ta ne duk bayan wata biyar “, Fahna tace “ikon Allah, amma to miyasa be yi aure ba”, Alhaji Musa yace “a cewar sa wai matar aure bata gyara kanta kamar yadda karuwa ke yi, akwai lokacin da macen gida in ta kai bata gyara kanta musamman idan ta haifi yara da yawa, amma ita karuwa mai wayau bazata bari ta tsufa ba”, Fahna ta jinjina kai cike da mamaki a ranta, suna cikin firar motar shi ta ciji burgi, dai ƙiiiiiiiii kake ji, motar ta tsaya, da sauri ya fita domin duba me ya faru, yafi awa ɗaya akan motar amma bata gyaru ba, gashi daji ne, sun yi nisa da gari sosai, Fahna ce ta fito daga motar “Baby me ya faru? “ta tambayi Alhaji Musa dake tsaye gaban motar, “Baby motar fa ta ɓaci ya kenan?”, kallon shi tayi tace “mu ne mi mai gyara “, “ai babu mai gyara anan” ya faɗa, suna tsaye gaban motar ya taɓa wancan, ya taɓa wannan har dare yayi, agogo Fahna ta duba ƙarfe 10:00 na dare gashi barci take ji, gashi gobe da sassafe Baba zai zo ɗaukar ta, gashi basu ma ji rabin tafiya ba, basu da wani zaɓi daya wuce su kira Qaseem a turo musu mota, da wannan tunanin tayi barci cikin mota, Alhaji Musa wayar shi ya ɗauka ya kira
Qaseem ya shaida mishi abunda ke faruwa, da asuba motar da Qaseem ys turo musu ta iso, tsoro da fargaba fal ran Fahna, suka kama hanyar kusa wanda suke da kusan awa huɗu kafin su isa
**************************
A ɓangaren Baffa kuwa tunda ya fita sallar asuba be dawo ba, dan hankalin shi yaƙi ya kwanta da tafiyar da Fahna tayi, saboda haka ana gama sallah ya wuce tashar mota, motar ƙarfe 6:30 ya bi.
Awa ɗaya yayi a hanya ya isa Gusau, kai tsaye adai-daita sahu ya tara ya nufi gidan aunty kareema , a ƙofar gidan ya haɗu da ɗan ƙaramin yaron Kareema, “Muhammadu zo “, da gudu yaron yazo, “ina auntyn ka Fahna”, “ai bata zo ba, naji mama na faɗin yau zata dawo daga Abuja sai ta zo gidan mu, wai kai zaka zo ka ɗauke ta”, mamaki fal ran Baba, zuciyar shi har buguwa take yi, me zai kai Fahna Abuja, “to shikenan, kar ka faɗa ma kowa na zo, zan zauna daga nan har ta dawo, je kayi wasa”, ba tare da Muhammadu ya kawo komai a ranshi ba, ya koma gurin da suke wasa.
10:30
***************’
Shigar su garin Gusau kenan Fahna ta azazzali Alhaji Musa akan ya fara aje ta gidan Aunty Kareema, dan ta san duk inda Baba yake ya baro shinkafi yanzu.
(rashin sani yafi dare duhu)
A ƙofar gidan Aunty kareema ta saka Alhaji Musa gaba sai ya fito ya gaida Aunty Kareema, fitowa yayi daga mota sannan ya zagayo ya buɗe mata mota, wani murmushi ta sake mishi, yace “Baby bari na miki rungumar bankwana kince sai an daɗe zamu sake haɗu saboda kar baba yayi zargin wani abu “gaɗa mishi kai tayi sannan ya rungume ta batare da ya kawo komai a ransa ba kasancewar unguwar cikin lugu take ba’a ganin su, kawai ya haɗe bakin shi da na ta ta ya fara tsutsa kamar ya samu sweet, sun fi minti uku a haka kafin ya jaye jikin shi daga nata yace zamu iya shiga, Baba dake zaune ƙofar gidan zuciyar shi kamar zata fashe, be taɓa tunanin haka daga gurin Fahna ba, ba san lokacin da hawaye suka fara zubo masa a ido ba????????????????.
Masu karatu abun da ciwo iyaye su ga ɗan su ya lalace ????, kira zuwa gare ku ƴan mata kuji tsoron Allah, nasan bazaki so la’anar Allah ba, kar ki bari shaiɗan ya ruɗe ki, ki zama sanadin zubar hawayen iyayen ki.
Gani Baba a ƙofar gida yasa Fahna tayi saurin sakin akwatin ta ƙasa, ƙoƙarin jaye hannun ta take yi daga hanun Alhaji Musa, da gudu ta isa gaban Baba tace “Baba wal-laaa-hi” cikin tsarƙewar zanxe, bata samu ƙarasa ba jin yace “babu komai shiga kiyi musu sallama kizo mu tafi, nagode miki sosai da irin sakayyar da kika min “, Alhaji Musa kuwa saurin tafiya yayi ganin Mahaifin Fahna, shiga tayi jikin ta ba ƙwari suka gaisa da Aunty Kareema, “Bari a kawo miki abinci kici” Aunty Kareema ta faɗa, Fahna tace “a’a…… “, bata ƙarasa maganar ba taji muryar baba yana sallama, zuwa yayi suka gaisa da Aunty Kareema, “tashi muje ko” ya faɗa, Aunty Kareema tace “ka bari taci abinci mana”, “ni sauri nake, ta bari in mun je gida taci, ita ta miki kwana biyar a gida ai ko taci abinci har ta ƙoshi”, Aunty Kareema tace “eh wallahi gaskiya naji daɗin zuwan ta ga Fahna da son aiki, kaga ma kayan yaran nan duk ita ta wanke su, ɗazu take cewa zata goge sai gashi aka ɗauke wuta “murmushi ƙarfin hali yayi yace “ai haka Fahna take, mu zamu wuce”, “to shikenan sai kin sake dawowa “Aunty Kareema ta faɗa tana sauke wata irin muguwar ajiya zuciya, dan ita duk ganin ta Baba be san Fahna bata zo gidan ta ba, Fahna kuwa duk tsoro ya cika ta, dan tasan kawai Baba yayi shiru ne dan baya son ya tara musu jama’a a gidan mutane.
To fa akwai chakwakiya next chapter ????????????????????????????.
Sannan ƴan uwa kuyu haƙuri zaku jini shiru na wasu kwanaki, sakamakon rasuwar da aka yiwa ɗaya daga cikin ƴar ƙungiyar wato princess fateema mazadu. Ina miƙa saƙon gaisuwa ta zuwa gareki, Allah ya jiƙanka da Rahama HRH. ALH. ABUBAKAR MUHAMMAD KWAIRANGA.
LOVE U ALL MY FANS.
Haɗin guiwar :Queen Nasmerh & Rabiatul Adawiyya
ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️✍️✍️⚔️
COMMENTS PLSSSS ????