Lu’u Lu’u 7

*7*

 

Ta b’angaren wurin kwanan hadimai da bayin gidan suka bi suka wuce, yanda hadiman suka yi tsuru suna kallo cikin jimami ana wucewa da sarauniyarsu yasa duk suka ji ba dad’i, a sanyaye take wucewa har saida suka kusa shiga ta wata kusurwa, d’aga kanta tayi dake k’asa ta kalli wani d’aya daga cikin fadawan gidan, wani k’ayataccen murmushi ta sakar masa ta juya harshenta zuwa larabcin parsi tace “Ko ta halin yaya kayi k’okari ku had’u da ita, ka sanar mata ta fad’a musu su ninka kulawarsu da saka ido a kan ta, dan komai ya kusa fitowa fili.”

Sake fad’ad’a murmushi tayi ta d’ora hannunta akan shi kasancewar matashi ne tace “Ka kula da kan ka.”

Duk da hawayen dake taho mishi saida ya rusuna mata yana jinjina kai alamar karb’ar sak’onta, wucewa sukayi haka hadiman wasu ke kuka wasu kuma jimamin ne kawai a fuskarsu, a haka aka shiga da ita wata hanya dake sadar da mutum zuwa k’asa, tafiya sukayi mai nisa a cikin wurin da zaka rantse a wata duniyar kake ko kuma wani ramin b’era ne, banda jan fitilun da suka haska gurin da zai kasance mai duhun gaske.

A hankali suka fara isowa kurkukun inda d’akunan suke a laye kowane mutum d’aya ne a ciki, k’ofofin bak’in k’arfe ne da manyan kwad’on da ake datse k’ofar, daga sama kawai ake k’aramar tagar da iya fuska zata iya lek’awa ta ga na ciki.

A b’angaren dama ya bud’e mata wani d’aki ta shiga sannan ya mayar ya rufe, babu komai a d’akin banda shafaffen simiti, baya ga haka babu komai a d’akin dan ko wuta babu kuma ba wata taga bayan wacce ke jikin k’ofar, ko haske iya na fitilun dake corridor wurin ne ke d’an haskaka sauran d’akunan.

A hankali ta sulale ta zauna a wurin tana fashewa da kuka, kukan ba wai na canjin daya risketa bane a take, na yanda ‘yarta da kuma marik’anta zasu kasance, tasan dole su sake jajdadda nemanta, suna samunta kuma kasheta zasuyi, wannan tunanin yasa ta yin kuka kamar zata shid’e.

*Giobarh*

 

Suna had’uwa da mutumin ya mik’o masa k’aramar farar takarda a nad’e, karb’a Haman yayi ya bud’a takardar ya karanta sannan ya kalleshi yace “Ka tabbata?”

Jinjina kai yayi yace “Na tabbata yallab’ai.”

Shi ma jinjina kan yayi ya fito da dunk’ulen kud’i ya bashi yace “Nagode.”

Da sauri ya karb’a yana fad’in “Ni ma nagode yallab’ai, idan buk’atar wani abun ta taso ka nemeni kawai.”

Jinjina kai Haman yayi amma bai ce komai ba, lafiyayyar motarshi ya shiga cikin salo da k’warewa ya tayar ya bar gurin, tafiya yayi mai nisan gaske kafin ya isa ga lambun da aka bashi kwatancen.

Fitowa yayi a motar ya tunkari shiga ciki, k’ofar da akayi da siraren k’arafu na ya tura ya shiga yana ta kalle kalle da son hango mutum, saida ya kai tsakiyar lambun ya ji motsi ta gefensa, waiwayawa yayi hakan yasa shi ganin mutum tsaye ya d’ana bindigarsa a kan shi yayi shirin kare kansa.

Gyara tsayuwa Haman yayi ya fuskanci mutumin ya d’aga hannayenshi sama yace “Kwantar da hankalinki, ban zo nan dan na cutar da kai ba, ni ba mugu bane.”

Saida ya sake saitashi da bakin bindigar yace “Ta ya zan yarda da kai? Waye kai ? Kuma me ya kawoka sansani na?”

Hannu d’aya Haman yasa aljihu ya fito da bajon shi ya nuna masa yace “Ni sunana Haman Bahar, jami’in bincike ne na farin kaya, na rok’eka ka tsaya muyi magana.”

Kallon tuhuma ya masa yzce “Na kasa yarda ba cutar da ni za ka yi ba.”

Cikin ankarewa Haman ya zura hannunshi bayan rigarshi a k’ugunshi ya ciro bindigarshi mai lasisi ya jefa a k’asa kusan k’afafun mutumin yace “Wannan shi ne, na rok’eka ka saurare ni, na zo ne muyi magana akan b’atan yar sarki Musail, an tabbatar mana da kai ne bafaden da kasan jakadiyar sarauniya Juman, dan ku ne masu gadin bakin k’ofar shiga masarautar kai da mijin ta mai sunan Utais.”

Sak’e yayi tare da sauke bindigar yayi k’asa da ita, ba tare daya daina tsareshi da ido ba yace” Me kake son sani daga gareni?”

Gyara tsayuwa ya sake yi yana sakin numfashi yace” Kai ne mutumin da ka san mutanen nan guda biyu, sannan daga majiya mai k’arfi kai ma nemanka akayi aka rasa shekara d’aya da b’atan gimbiya Zafeera, dalilin b’acewarka nale son sani, da kuma inda zan samu Habbee da Utais.”

Wani d’an murmushi yayi tare da juyawa yana tafiya yace” Tambayarka ta d’aya kam zan amsa, amma ta biyun ka manta da ita.”

Da sauri ya bi bayanshi tare da sunkuyawa ya d’auki bindigarshi ya mayar a mazauninta yana fad’in” Me yasa ka ce haka?”

Bai amsa mishi ba har saida suka shiga wani falo, wuri ya nunawa Haman ya zauna yana k’arewa d’akin kallo, tsaye yayi a kan shi yace” Shayi zan kawo maka ko ruwa?”

Girgiza kai yayi yace” Ko d’aya, nagode.”

D’aga kafad’a yayi irin oho d’in nan sannan ya zauna kujerar dake fuskantar Haman d’in, k’urawa juna ido sukayi kafin yace” Ina jinka.”

Gyara zama Haman yayi yace” Me yasa ka bar masarautar Khazira?”

Cikin sakin fuska yace” Dalili ne mai k’arfi, umarta ta akayi da na bar k’asar, ba ni ne bari dan ina so ba.”

Da mamaki yace” Waye ya umarceka?”

Ba tare da kwalo kwalo ba yace” Sarauniya Juman ce.”

Wani sabon mamakin ne ya kama shi yace” Sarauniya Juman kuma? Amma me yasa?”

Gyara zama yayi ya sauke ajiyar zuciya yace” A duk masarautar ni kad’ai na iya yaren k’asar Azarbhaijan, hakan yasa ni da su Habbee muke hira a tsakaninmu dan su ‘yan k’asar ne.”

Da matsanancin mamaki Haman yace” Akan haka ta umarceka kayi nesa da masarauta?”

Jinjina kai yayi alamar e, ba tare daya shanye mamakin ba yace” In hakane kuwa kar ka ce min sarauniya na da hannu a b’atan yarta?”

Wata yar dariya yayi sannan yace “Ka canka daidai.”

Girgiza kai Haman yayi yace “Amma ta ya ta iya jurewa haka? Me yasa ma tayi hakan?”

Cikin rashin sani yace “Wannan ne kuma ban sani ba, abinda na sani kawai shi ne ta kub’utar da ‘yarta.”

Jinjina kai Haman yayi yace “Na ji wannan, yanzu zaka taimaka min ka fad’a min inda zan samu su Habbee?”

Girgiza kai yayi yace “Kamar yanda na fad’a maka ka manta da tambayar nan, dan ni ma ban sani ba.”

Murmushi Haman yayi yace “Kaga, ka daure ka fad’a min, idan ma wani abu kake so ni ka fad’a min zan baka, binciken nan yana da mahimlanci a gareni.”

Mik’ewa yayi tsaye yace “Na fad’a maka ni ban san inda suke ba, sak’o kawai nake isar wa da sarauniya.”

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button