Bakar Inuwa

BAKAR INUWA 16

Typing📲

Episode 16

……….Tunda mai-martaba ya sako zancen Ramadhan a cikin meeting da yakeyi da ƴaƴansa da matansa a duk irin wannan ranar hankalin Gimbiya Su’adah da Fulani da Adda Asmah yake a tashe. Ba komai ne ya tada hankalin nasu ba kuwa sai jin mai-martaba yace har Alhaji Hameed Taura yayima Ramadhan ɗin mata. A cikin satin nan ma zasu tuntuɓi iyayenta dan baya buƙatar abun yay nisa.
    Duk yanda gimbiya Su’adah taso daurewa saboda ƴan uba dake a wajen kasawa tai. Ta ɗago a firgice tana kallon mahaifin nasu. Cike da ƙasaita yace, “Mamana kinada magana ne?”.
    Kowa yasan irin son da yake mata saboda sunan wadda taci, dan haka suka shiga ɗan taɓe baki suna maida kawunansu gefe rayukansu fal hassadar jin Ramadhan zai fito takarar shugabancin ƙasar NAYA a dalilin kakansa.
      “Abi maganar yimasa matar ne sai naga kamar anyi gaggawa, tunda kaga abinda ya faru a baya kamar ya kamata a bari ya nutsu kafin a sama masa wadda zata dace da shi da matsayin da muke fata zai hau”.
       Mai-martaba da ke kallon television kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ɗan murmusa. “Mamana banda abinki wace nutsuwa Ramadhan ke buƙata bayan wadda ya samu a shekaru biyar da faruwar rasa iyalinsa. Kece fa kike damuwa da rashin aurensa har kike damuna, yanzu kuma an sama masa kina jayayya?. Alhaji Hameed bazai taɓama Ramadhan zaɓen matar banza ba, sannan yanada iko akansa irin wanda ni bani da shi matsayina na kakansa ta ɓangaren mace. Inaga addu’a da fatan alkairi ya kamata mu masa, dan bazasu taɓa zaɓa masa matar da bazata dace da matsayin da kike kallon ba”.
     “Amma Abie….”
Kansa ya girgiza mata. Kafin cikin ƙasaita ya ce, “Na gama magana Mamana”.
     Dole tai shiru, sai dai zuciyarta tafasa take tamkar zata kama da wuta. Fulani da bataso Gimbiya Su’adah yin maganar anan ba ta ɗan harareta ta wutsiyar ido itama. Dole tai shiru har aka tashi taron kowa ya koma sashensa.

★★

      “Ammi wlhy bazan amince ba a wannan gaɓar, wai taya za’ace ni da Basheer dake mahaifin Ramadhan bamu isa yanke hukunci akan ƴaƴanmu ba musamman ma Ramadhan sai dai tsoffin nan dake matsayin kakanninsa.”
    Gimbiya Su’adah daketa kaikawo a cikin falon hutawa na Fulani ta faɗa cikin tashin hankali. Kafin Fulani tace wani abu Adda Asmah ta amshe rai ɓace.
     “Maganar gaskiya wannan fin ƙargine Ammi. Amma ni ina ganin tun farko harda sakacinmu. Taya zaki sakar musu ragamar ɗanki bayan shi kaɗai ne tilon ɗa namiji a gidan. Daɗin daɗawa shine kuma babba…..”
     “To Adda ya kike so nayi?, bayan kinsan tun daga yayen Ramadhan suka riƙesa suka hanani, wane kalar abune banyiba amma sukai kunnen uwar shegu dani tsoffin nan”.
      “Amma ai basai ta wannan hanyar ne zaki dawo da Ramadhan jikinki ba. Tun a lokacin ya kamata kiyita jan ra’ayinsa cikin hikima shi da kansa zai dawo gareki batare da kin nuna musu koda a fuska ba. Amma ai wannan ƙarfa-ƙarfar tayi yawa. Dan wlhy yanda yakejin maganar waɗan nan tsoffin da mutuwa ke gab da su bayajin taki ma”.
        Tsaki Fulani tayi, hakan ya sasu kallonta su duka. Ta gyara zamanta na ƙasaita tana hararsu.
       “Kunfa dameni da surutan banzarku. Ku miyasa a komai baƙwa nutsuwa kuyi abun hankali sai shirme. K Su’adah yanzu kamata yay ki lallaɓa musan wacece zasu aura masa. Ni yanzun zan tuntuɓi mai-martaba da batun ƙudirinmu na haɗa auren Aynah da Ramadhan ɗin naji mizaice, duk dai abinsa ai bazaiƙi jikarsa ba ko?. Indai Ramadhan ne a wannan gaɓar zai dawo garemu, dan bazamu amince ya samu mulki su Firdausi su cigaba da juya manashi yanda suke so ba. Shine babban jikana na farko, dan haka nima inason abina”.
       Sosai shawarar mahaifiyar tasu ta ɗan basu nutsuwa, dan haka gimbiya Su’adah ta zauna tana sauke numfashi da ajiyar zuciya….

TK SPECIAL HOSPITAL

         “Kai wlhy idan sama da ƙar zata haɗe yau sai na shiga naga halin da gudan jinina ke a ciki, kajimin mara mutunci. Bar ganin kasa waɗan nan kayan kai tunanin zanji tsoronka, kai fa ba komai bane sai mai gadin gate ɗin asibiti mun sani, ni da kake gani na anan ba ƙaramin tantiri bane, duk wani gidan shege da shegiya dake ƙasar NAYA da mu akai taron bikin buɗesa saboda gawurtarmu a iya shege. Idan kaji ƙarya cigaba da nunamin yatsa kaga idan ban karya shege ba naga miza’ayi min”.
    M. Dauda ne ke zuba ruwan bala’i a gaban gate ɗin Tk special hospital. Dan security ɗin gate ya hanasu shiga ciki, shine suka tafi da kokawa akan sai fa sun shiga ɗin. Ganinfa da gaske suke security ɗin ya ɗaga waya ya kira ogansa. Jin hayaniyarsu ta cikin wayar ne ya tilastama Dr Shamsu fitowa da kansa dole har wajen gate ɗin.
         “Kaga matsa masa Daniel”.
Dr Shamsu dake ƙarasowa wajen gate ɗin ya faɗa cikin ɗagama security ɗin hannu ganin su M. Dauda na neman ɓalla masa kunkuru. Dan sun haɗu su biyu sun ƙadandanesa adole sai sun ɗagasa. Ga Daniel ɗin kuma yayi huɗunsu dan su taba duk ta gama ragaɗe naman jikin nasu.
    Cikin bin umarni security ɗin ya janye jikinsa yana ƙwafa da hararsu. Suma harar tasa suke da cigaba da kumfar baki har sai da Dr Shamsu ya dakatar dasu.
        “Kunga Baba ya isa haka dan ALLAH, mike tafe da ku?”.
    Da farko M. Dauda shima kallon sama da ƙas ɗin yay masa zai yaɓa masa bagaƙar magana M. Gambo ya dakatar da shi ta hanyar zungurinsa, shi ya fara magana da sauri.
     “Ranka ya daɗe dama munzo duba yarinyarmune da aka jima ciwo a dalilin Alhaji Hameed Taura. Wannan mahaifintane, ni kuma abokinsane kuma ɗan uwansa na ƙut-da-ƙut”.
      Dr Shamsu ya ɗan rumtse ido dan shi surutun M. Gambo hawar masa kai yake, a ƙasan ransa yana auna Raudha da wanda aka kira mahaifin natane. Tabas M. Dauda ƙyaƙyƙyawa ne, sai dai taba duk ta gama cinyesa ta sake sakashi komawa baƙi. Idan mai nazari ya nutsu tsaf a kallonsa zai ɗanga yanayi na jini dake tsakaninsa da Raudha, sai kuma kamanin su Fatisa da shi tafi rinjaye duk da suma sun fisa ƙyan gani da ƙuruciya a yanzun.
     “Maganar gaskiya bazai yuwu na yarda daku kai tsaye ba, saboda dalilai masu yawa. Yarinyar nan kowama zai iya basaja yanzu domin farautar ranta ko nuna dangantaka da ita domin idasa mugun nufinsa akan Taura. Dan haka kuyi haƙuri idan an sallameta zaku ganta. Dan a yanzu dai babu mai ganinta saboda tana ƙarƙashin kulawar ƴan sanda”.
       “Kutt… Bantan uban can kayyasa. Kai awa da zakace bazanga ɗiyata ba. To wlhy yau an taɓo bala’i, ai dama nasan za’a rina shiyyasa na shirya tsaf dan yin kayayatu a gidan redion jaharmu. Zan tafi bazanƙi ba, amma Taura ya saurari saƙona, dama ba’ance mana anji ƙishin-ƙishin ɗin takarar shugaban ƙasa zai hito ba, to wlhy nine zan fara masa ƙafar angulu ni Dauda uban Raudha mijin Asabe baban Ɗanjuma da Garbebe………”
       “Ya ALLAH”. Dr Shamsu ya faɗa yana ɗan ja da baya danjin kansa na sara masa bisa surutun M. Dauda. Su Malam Dauda na ganin haka suka faki idonsa suka kwasa da gudu zuwa cikin asibitin. Securitys ne suka rufa musu baya. A taƙaice dai cikin ƙanƙanin lokaci suka nema harmutsa asibitin, sai securitys sukai kama-kamar ɗakkosu zuwa waje. Ganin abun nasu bana masu hankali bane ga marasa lafiya da basa son hayaniya yasa Dr Shamsu ɗaga waya ya kira Bappi batare da tunanin zai ɗauka ba. Sai dai Alhmdllhi tana a ringin na uku aka ɗaga. Cikin girmamawa Dr Shamsu ya gaishe da Alhaji Hameed Taura, tare da jero masa bayanin abinda ke faruwa duk da shima daga can yana iya jiyo hayaniyar.
       “Oh ALLAH waɗan nan wane irin mutanene haka? Doctor Please saka wani ya kawomin su gida yanzun nan”.
       “Okay Ranka ya daɗe yanzu insha ALLAH ”.
     Bayan ya yanke wayar ya dakatar da hayaniyar su Malam Dauda da ƙyar yay musu bayani, amma sai suka ƙi yarda a cewarsu raina musu wayo Dr Shamsu zaiyi dan su bar asibitin. Anyi-anyi amma sunface basu yardaba, babu inda zasuje. Idan gaskiyane shi Tauran yazo ya samesu a asibitin inyaso sai su bisa.
     Sosai zancensu yasa mutane sake musu kallon mahaukata. Yo inba mahautaba taya zasuce Taura da kansa, mutum lamba na biyu a masu kuɗin africa, na ɗaya a NAYA yazo nan domin su kawai.
    Shidai Doctor Shamsu rasama yanda zaiyi yay, sai dai cikin ikon ALLAH yana tunanin miye mafita sai ga Bappi ya kirashi. Cikin rawar jiki ya ɗauka, ya kora masa bayanin halin da ake ciki. Murmushi kawai yayi da cewa, “Karka damu ina zuwa”.
    Idanu Dr Shamsu ya ɗan kwalalo da hangame baki na mamaki, sai dai kafinma yace wani abu Bappi ya yanke wayar.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button