Labarai

Yadda saurayina ya lakaɗa min dukan tsiya bayan kwashe shekaru mu na zaman dadiro, Muneerat Abdulsalam

A wani bidiyo wanda Muneerat Abdussalam, fitacciyar mai sayar da magungunan mata da maza a kafafen sada zumuntar zamani ta saki cike da hawaye ta yi karin bayani.

 

Dama tun safiyar Litinin ta bayyana yadda bariki tayi mata atishawar tsaki inda yanzu haka ta rasa makama kasancewar ko kudin magani ta rasa.

 

A bidiyon wanda aka ga yadda saurayinta ya molar mata da fuska saboda tsabar dukan da yayi mata, ta bayyana yadda ta kai kara caji ofis amma ‘yan sanda su ka mayar da maganarta shirme.

 

Ta ce ta kwashe lokaci mai tsawo su na zama da matashin wanda yayi alkawarin aurenta, ashe dan daba ne kuma cikakken dan ta’adda ne bata sani ba.

 

Ta shaida yadda yake zuwa dakinta da tsakar dare tare da balle mata kofa sannan ya tumurmusata da zarar ta yi masa kankanin abu wanda ya hassala shi.

 

 

 

Ta ce ya tsere mata da kayan da ta aike shi ya sanya mata a mota masu kimar dubu dari uku da ‘yan kai. Ta ci gaba da shaida cewa har guduwa tayi daga garin da suke don ta tsira daga sharrinsa bayan samun labarin ta’addancinsa.

 

A cewarta tana neman taimakon jama’a kuma ta yi nadamar gabadaya abubuwan da ta aikata a rayuwarta na bariki da biye-biyen maza.

 

Ta bayyana yadda take rayuwa cike da tashin hankali sannan saurayin nata yana ba ta hakuri idan sun yi fada daga bisani kuma yayi mata abinda ya zarce na baya.

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button