GOJE

GOJE 29 and 30

Ad

_____

       FREE PEGE

29&30
Kusan a tare suka d’auke idonsu daga barin kallonta, Asp din yayi magana amma shi uffan bece ba har ta gama harare-harare! ta fita daga ofis din. Ya d’an ja k’aramin tsaki da fadin.” Yarinya nan babu tarbiya a tattare da ita duk kuwa da cewa ta fito daga tsatso mai kyau, ba ta gaji dattako da karamci irin na mahaifinta ba, duk da ba a garin kano muke zaune ba muna da labarin dattakon mahaifinta mutum ne mai karamci da mutunci yana aiki da hankali da ilimi yana kuma gudanar da mulki a bisa tsari na isalama.”

Beso ya tanka a cikin al’amarin yarinyar ba amma ganin yanda Asp din yake jaddada maganar yasa yace.” Akwai irinsu da yawa wa’inda suka dauki mulki wata tsiya idan akace mahaifinsu nada sarauta ko wani muk’ami sai su dauki girman kai su dora a kansu suna ganin babu wanda ya isa dasu, hakane maganarka mutumin kwarai yana iya haifar baragurbi acikin al’umma jarabtace kawai daga Allah.” Yace.” Kwarai kuwa wannan haka yake sai dai kawai mu roki Allah ya shirya mana zuria baki d’aya.” Ya amsa da ameeen ya Allah.

Shuru na minti biyu ya ratsa gurin, cikin ‘yar tsokana Asp din yace.” Akwai abinda na manta ban tambayi MAI DAWA! ba.”?
Murmushi yayi da fadin.” Akwai sauran tambayoyi kenan.”? Girgiza kai yayi da fadin.” Tambaya daya ce shin kana da iyali kuwa.”?

Girgiza kai yayi gami da dan ta’be bakinsa………Asp ya dan zare ido da fadin.” Kana nufin babu iyali kenan.”
Kai ya daga masa still da murmushi a fuskarsa.

Sai kawai ya shiga girgiza kansa da fadin.” Gaskiyar magana yanda kake jarumin namiji mata hudu suka cancanta da kai amma ace ma ko daya babu.” cike da alhini ya kare maganar.

Sai abun ya bashi dariya ya dan dara kafin yace.” Asp matsalar mata nada yawa shiyasa nayi zamana a haka ba wai don bani da bukata ba, kawai nafi bukatar kwanciyar hankalina nayi duk abinda nake so ba tare da wani ya caza min kai ba.”

Yace.” To ai hakan nan ake hakuri dasu da matsalarsu Umaru kowane maigida yana da matsalar iyali mussaman idan mace fiye da d’aya yake da ita, dole ba zaka rasa shi da matsala ba, nima matana biyu sai dai kowacce da gidanta kuma yanzu haka ina shirin yin ta uku da yardar Allah sai na cike domin ina da ra’ayin hakan.”

Ya girgiza kai da fadin.” Kayi kokari sosai kuma ka aikata sunnah Allah ya baka ikon yim adalci a tsakaninsu.”

Ya amsa da “Ameen ya Allah ina fatan kai ma kayi koyi dani.”

Girgiza kai kawai yai baya tsammanin hakan domin baya san damuwa ba lallai sai ka tara mata a gidanka za’a tabbatar da jarumtarka ba, shi a ra’ayinsa zai iya ‘kare rayuwarsa da mace daya, sai dai kuma duk yanda Allah ya shirya masa rayuwa to zai kar’ba hannu biyu tare da godiya a gareshi.

Ad

Ke’bantacen guri aka ajiyeshi shi kad’ai ba tare da da sauran yaran sa ba, sai dai su an tattarasu guri guda da sauran masu laifi gama gari. wannan karamcin da Asp din yayi masa ya tsaya masa mutuka a rai yayi ta tunanin irin alkairin da zai saka masa.


Uwale duk atamfofin da take k’uzu tana tarawa a cikin adaka fito dasu tayi ta siyar. ta dinga bin tsangaya-tsangaya tana bayar da sadaka domin almajiran suyi mata saukar al’kur’ani akan bukatarta, Allah maji rokon bawansa addua ta kar’bu.

Washe garin ranar da ita da Mahaifin Hamra’u da ita Hamra’un suka yanke shawarar zuwa headquarter ‘yan sandan domin samun cikkenan bayani.

Sun jima a tsaye kafin wani jami’i ya sauraresu, Malam Hafi’i mahaifin Hamra’u shine yayi masa bayanin abinda yake tafe dasu.

Yayi jim! yana kallonsu kafin yaja tsaki ya barsu a gurin……Uwale da sauri taje tari gabansa kuka ta fashe dashi ta zube gwiwa biyu a gabansa tana rokonsa, hakan ya janyo hankalin ma’aikatan dake gurin suka fara tambayar ba’asi.

Cikin kuka tace.” Me yasa dukkaninku baku da imani ne? tunda muka zo gurin nan babu wanda yayi mana kallon mutunci Allah da Annabi sunfi karfin wasa amma gabadayanku bakwa tsoron Allah.”!

Daya daga cikin musulman dake tsaye gurin ne yace.” Tayi masa bayani abinda yake tafe da ita.

Hanci ta fyace kafin.” Tace “Mun zo gurin UMARU wanda ku ka d’aure kuna zarginsa da ta’addanci bayan ba haka gaskiya take ba.”

Yace.” Yi shuru ki kwantar da hankalinki ki daina kuka zanyi miki kokari yanzu.” Ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta, tace.”Nagode sosai Allah yayi maka albarka.” Ya amsa da ‘ameen kafin ya umarcesu da suje su zauna a wata rumfa.

Sai da yaga zamansu sannan ya bar gurin, kai tsaye ofis din Asp ya nufa domin sheda masa abinda ke faruwa.
Ya k’ame da sarawa kafin ya sheda masa abinda ke da akwai, kai tsaye ya bashi umarnin shigowa dasu.

Da kanshi ya nuna musu gurin zama yana musu sannu, Malam Shafi’i da ‘yarsa suka zauna kamar yanda ya umarcesu Uwale kuwa kai tsaye kujerarsa ta nufa, ya dinga kallonta har ta iso inda yake ta zube gabansa kawai sai ta fashe da kuka tare da rirrike masa kafafu! kuka take sosai tana bashi hakuri.

Tausayi ya rufeshi da kyar ya iya mik’ewa tsaye sakamakon rikon da tayi masa, ya sunkuya tare da sanya hannu ya dago ta ta mike tsaye, rungumeta yayi yana rarrashin gami da bata hakuri.

Ita kuma fadi take.” Ku za’a bawa hakuri ku dubi girman Allah kuyi adalci kada ku yanke hukunci akan wanda bashi laifi bashi ne wanda kuke zargi ba.

Ad

_____

1 2 3Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button