NOVELSUncategorized
BARIKI NA FITO (BOOK 1) 22

*PAGE 22*
Kuka tayi Mai isarta, sannan ta wanke fuskanta tare da shafa powder dan Kar Yarima ya gane, saida ta tsaya ta seta kanta sannan ta fita…..
Tunda ta fito yake kallon fuskanta wanda dama tunda ta shiga
idonshi nakan kofar gidan, tun Kafin ta karaso ya gane tayi kuka domin idonta yayi ja, dan farar mace Indai tayi kuka sai an gane dan fuskanta zata canza tayi ja ja……
Isowarta ne yasa tunanin da yake ya kawar
Bayan ta bud’e motar ta shiga da sallama muryanta a dashe….
Amsawa yayi tare da fad’in my princess yau kwata kwata na rasa gane maike damunki? Mai yasa kikai kuka da kika shiga ciki?
Gabanta taji ya fad’i ya akai yasan nayi kuka toh kodai ya biyoni ciki ne kai Anya a’a Toh y……
Katse mata tunani yayi tare da kiran sunanta da zainab
Da sauri ta d’ago ta kalleshi dan tasan magana zai Mata Wanda yake bukatan hankalinta tunda ya kirata da sunanta….
Yace I don’t know why yau kaman you are not happy, plz Idan kina da wani matsala ko damuwa let me know, ban son kiji shakkan fad’amin wani abu da kike bukata ko kunya, plz tell me maike damunki?
Muryanta na rawa tace Yarima Ina son inyi maka wata tambaya, ina son Kuma ka bani amsa…
Murmushi yayi tare da fad’in go ahead….
Tace kasan al’amarin aure yana da abubuwa da dama, yau Idan akace mutum zaiyi aure sai ayita kushe shi, ko kuma azo ana ya’da Labarin karya akan mutum yan…..
Dakatar da ita yayi da fad’in enough my princess it seem like wannan mafarkin da kikayi yasa kike wannan maganan, na fad’a miki zina ne kawai zaki aikata in fasa aurenki….. Bayan haka banga abunda zaki aikata ba ince na fasa auranki ba, sannan ina so ki sani sonda nake miki ba Wanda wani zaizo ya fad’a magana akanki bane in yarda I trust you nasan bazaki taba bani kunya ba
A hankali tace in fah wani yazo yace maka ni karuwa ce ya Z……..
Yace ya isa haka ya isa yana maganan ne cikin jin haushin abunda tace, yace karki kara danganta kanki da wannan Kalman infact ma ban son ki karamin wannan maganan plz….. Let change the topic
Shuru tayi ba tare da tace komai ba, Satan kallon Yarima tayi wanda taga gaba d’aya yana yinshi ya canza alaman ranshi a jagule yake…..
Katse mata tunani yayi tare da fad’in Zainab kinsa naji babu dad’i, mai yasa zaki damu da mafarkin da kikayi haka har kike zargin wani abu? Har kike dan ganta kanki da wannan mummunan Kalman, Zainab duk Wanda ya kiraki da wannan Kalman sai Nayi karanshi dan ba haka kike ba, I trust you more than my self, ina jin kaman na sanki tun tuni karki manta tun a mafarki na Fara ganinki ban taba ganin Fuskanki ba a mafarki ba sai a zahiri na ganki sannan na gane Kece….. Hannunta duka biyun ya ri’ke yace Zainab nasan had’uwa na dake had’in Allah ne, babu wani abu da wani zaice a kanki yayi tasiri a wajena Indai ba gani nayi da ido naba, so inaso ki daina duk wani tunani akan sonda nake miki
Wani hawaye mai zafi ne ya fito mata daka ido, gaba d’aya jikinta yayi sanyi, tana son Yarima kuma tana son fad’a mishi ko ita wacece gashi ta d’auko hanyar fad’amai ya dakatar da ita, lallai in Yarima yasan wacece ita bazai aureta ba, zan Bari saiya aureni in fad’a mishi koni wacece na tabbata zai fahimce ni S……..
Katse mata tunani yayi tare dasa hannunshi yana goge mata hawayen idonta, yace Zainab bana son ganin wannan hawayen naki, kina min asaransu…..
Murmushi tayi tare da fad’in na daina Yarima na daina bazan kara ba.
Hancinta yaja tare da fad’in yauwa my princess
Murmushi ta saki
Yace ya maganan Walima dinki? Mai zamu shirya?
Tace banda wani Abun cewa sai yanda kace.
Yace Nop ina son in San mai kike so….. Yauwa you never tell me what you like nd dislike
Tace Yarima komai kake so shi nake so
Murmushi yayi tare da fad’in toni ke nake so….
Dariya tayi tare da fad’in ni kuma?
Yace eh ke nake so,duk wannan abunda suke hannunshi na ri’ke da nata
Sakin hannunta yayi tare da matsawa ya d’auko wani karamin akwati ya bata yace gashi sai kiyi abunda ya dace, sannan akwai check a ciki nasa iya kudin da za’a cira amma ban sa suna ba Wanda zai cira sai yasa sunanshi, kiba ma islamiyya din, gudun mawarki….
Tace Yarima nagode Allah ya saka maka da gidan Aljanna ban San wani….
Ya dakatar da ita tare da fad’in ya isa haka my princess
Tace Yarima amma kaman hidiman yayi yawa Sosai
Yace komai na miki baiyi yawa ba, u deserve it
Tace ngd
Ido ya kura mata yana kallonta ko kyaftawa bayayi
Ganin irin kallon da yake mata yasa tayi saurin yin k’asa dakai
Hannunshi yasa ya d’ago Mata fuskanta yace my princess d’ago ki kalleni….
Ido ta rufe domin bazata iya kallon idonshi ba, dan yana mata wani irin mugun kwarjini Sosai
Ganin ta rufe ido yasa yayi murmushi tare dakai bakinshi kusa da kunnenta yace I want my kiss now, Bayan ya fad’a mata hakan yayi baya tare da kallon fuskanta yaga har yanzu idonta a rufe, iska ya hura mata a fuska tayi saurin bud’e ido, murmushi ya sakan mata idonsu duka yana kallon na juna, fuskanshi ya fara matsawa kusa da nata kaman zaiyi kissing dinta ganin haka tayi saurin rufe ido, murmushi yayi yakai mata peck a goshi jin a goshi yayi mata yasa ta sauke ajiyan zuciya har yana ji, baya yayi tare da fad’in I don’t want the kiss now
Kallonshi tayi suka had’a ido da sauri tai k’asa dakai
Murmushi yayi yace wannan kunyan yayi yawa but very soon zan rage miki shi
Murmushi tayi ba tare da tace komai ba
Yace Zainab very soon you will be mine
Ganin taki magana yasa yace bari inzo mu wuce tunda my princess ta k’osa in tafi
Da sauri tace nifa bance haka ba…
Murmushi yayi yace kina son in zauna?
Murmushi tayi tare da fad’in wannan tambayar..
Sai kuma tayi shuru
Yace Ina ji fad’a min?
Tace Mai zance?
Murmushi yayi yace say you love me
Itama murmushin tayi tare da fad’in yaushe zaka tafi?..
Dariya yayi yace oh saboda karki fad’a kike korana koh?
Tace a’a nifa ba haka nake nufi ba
Yace anyway ya kamata inzo in gudu naga yamma yayi Sosai gashi an kusa kiran sallah magrib…
Tace toh ka Bari in kukai sallah saiku tafi.
Yace OK my princess, yace banga mutumina ba yau?
Tace habib?
Yace eh
Tace baya nan amma zaka iya ganinshi ya fad’o yanzu
Yace OK…. Dan shuru yayi Kafin yace naso inzo saukan ku but I will try in samu inzo
Tace a’a Yarima basai kazo ba, ka Bari kawai duk abunda akayi zan turo maka, ranan fah shine Washe garin auranka kaga karka shiga hakkin amarya
Idonshi na kanta yace Kema ai tawa ce, sannan Idan abun murna ya sameki dole inzo in tayaki
Tace Yarima plz basai kazo ba Wlh na yafe maka, abunda bazan so ya faru akaina ba banso Ayi ma wata akai na
Yace really?
Tace eh
Yace Sai yasa nake sonki, but amma duk da haka Zanzo
Tace shikenan tunda haka kace, but Ina son Yarima na ya zama mai adalci, tunda ni nace na yafe
Murmushi yayi tare da fad’in shikenan Yarima dinki zaiyi adalci insha Allah tare da ja mata hanci
Tace akwai zafi fah
Murmushi yayi yace am so sorry my princess, jin ana kiran sallah yasa ya fita dan yayi sallah
Itama gidan ta shiga tare da ajiye jakan da Yarima ya bata, zama tayi tana tunanin firansu Tana murmushi, Yarima I promise ranan daka aureni zan fad’a maka koni wacece Bazan bari ka aureni ba sai Nayi istabra’i zama tayi tana ta tunani dan tana fashin sallah, karan wayanta yasa ta d’auka ganin Sunan Yarima tayi ta danna tare dakai wa kunnenta
Yace come out in ganki mu kama hanya
Tace OK tare da kashe wayan tana murmushi fita tayi a waje ta ganshi a tsaye
Inda yake taje yana ta murmushi a tsaye suka tsaya yace my princess zan wuce sai yaushe kuma?
Tace sai Bayan bikin ka
Murmushi yayi yace bazan iya ba, Kema kin sani
Tace Yarima daka jibi fah zaku Fara abu
Yace how did you know?
Tace naji Ai kana fad’ama amaryanka
Yace hakane na k’osa ma a kawo ta, yana maganan yana kallon bariki
Ganin ta d’an bata fuska yasa yaci gaba da fad’in bari inje in samu muyi waya ma….
Gaba tayi tana fad’in saida safe tana fad’in haka tayi cikin gidan
Murmushi yayi tare da girgiza kai kiranta yayi amma taki d’auka
Message ya Mata tare da fad’in haka za muyi sallama din?
Ganin batai reply ba kuma bata fito ba yasa ya shiga mota yace suje, kara tura mata message yayi yace ok na tafi kin San hanya zamu kama but kinsa na tafi ba tare da munyi sallama Mai Kyau ba, may be ma wannan ne last maganan mu……
Tana ganin message din ta fito da sauri amma ina motocin sunyi gaba…
Yarima yana kallonta murmushi yayi tare da fad’in I love you my princess
Bariki komawa tayi ta doka ma Yarima kira amma yaki d’auka, message ta tura mishi Tana fad’in plz pick my call I need to talk to you
Yarima yana ganin sa’kon yayi murmushi tare da kashe wayan dan yasan zata kara kira kuma bazai d’auka ba har sai yaje gida, domin bazai iya waya da princess dinshi ba a gaban driver domin sarautar shi bazai Bari driver yaji Kalan kalaman da zaima baby dinshi ba
Bariki kara kira tayi taji wayan a kashe kanta taji ya Sara, jiki a sanyaye ta had’a kayanta tabar gidan dan zuwa d’akinta, tana zuwa d’aki ta ajiye kayan tare da had’a tea tasha, jakar da Yarima ya bata ta bud’e kud’i ta gani makil da yawa dubu d’aya d’aya bandir bandir har guda ishirin million biyu kenan, ido ta d’an zare tana mamaki check din ta d’auka shima taga million uku ya rubuta, a hankali tace Yarima kud’in yayi yawa har 5mil, hawaye ya zuban Mata tace yanzu duk wannan Abun karya nayi maka ka d’auki wannan kud’in kaban, ba tare daka nemi jikina ba lallai Yarima inna Bari na rasaka Nayi babban rashi, duk yanda zanyi dole In boye koni wacece har sai ka aureni zan fad’a maka Nasan zaka fahimce ni, wani hawayen ne ya kuma zubo mata……. Muje zuwa muga ko Asirin bariki zai rufu ko kuma akasin haka
~MARYAM OBAM~