KWARATA RETURN 5
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* ????
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-
*KWARATA RETURN…*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa…
*JAMILA MUSA…*
*SAI NA AURI D ‘ K*
???? —— 5
Ai ba maganar inyi haƙuri bane ba. Idan dai na fahimce ka kawai dai kana mana kora da hali ne. Ah² yi haƙuri ba haka nake nufi ba , yayi maganar yana nunawa da hannunshi da yanayin ladabi. Inda ya ajiye rigarshi daya cire ya matsa ya ɗauka yana cewa ai duk abun bai kai haka ba , nayi wankan ma da daddare idan sun tafi , da ka rufawa kanka asiri. Ɗan shafa gefen fuskarta yayi yana murmushi tare da cewa idan akwai sauran abincin ki bani sai in tafi can shagon Salihu inci….
A tsiwace tace na ajiye maka sai naga bai ishemu ba. Kawai dai mun cinye nasan ka siya can waje idan ka fita. Da kinɗan silalamin ko taliya tunda akwai miya wallahi yunwa nakeji sosai , abincin sayen nan ina ci zuciyata tanamin ba daɗi , tsoki tayi ta fice tana gunguni har palo ba tare data bashi amsa ba. Tana isa wurinsu Hadiza taci gaba da cewa wallahi babu wanda zaisani tsira wata girki yanzu danni ba jakace ba , gidajen abinci nawa a garin nan ? Dan dai kawai kar ya fita ya isa. A shi a dole sai yazo gida yaci shi mai mata….!
Hadiza tace ya akayi ne ? Shi mana , shi waye ? Abdul mana , meya faru ? A dai² lokacin daya fito dan fita ita kuma tana cewa wai in dafa mishi abinci. Ko tausayi na ba’ayi a gidan nan , tun safe nake hidima da mutane a ya kamata na riƙa hutawa. Cike da ladabin ɗan ƙunama Hadiza tace haba dan ɗan wannan ? Ai komu kika ce a cikin mu wani yayi zamuyi , ba komai ki huta bara a dafa maka tayi maganar tana miƙewa , Halimatu tace ai da kin barshi tunda fita zaiyi ai yace zai siya a waje. Hadiza tace ah yi haƙuri Oga a girka babu jimawa , tayi maganar tana shiga kicin… Salam² ya koma bedroom.
Ita kuma Halimatu ta zauna a palo cikin ƙawayenta akaci gaba da maida yadda akai ana shewa…. {{ Kina aikin me “yar uwata…? Ƙawar banza ƙawar wofi…? Wace ce ita ? Me kike nema a wurinta da har zaki fi²ta ta akan miji ? Wacce yau tana iya canja ki , shifa miji ? Ko kun rabu idan da zuri’a an zama “yan uwa. Hmmm ki kiyayi kanki da duniya kinji ko….??? Murmushi , kuma bawai nace kici ƙaniyar ƙawarki ba , a , a adai riƙa abun da lissafi… Karki canja ma ƙawarki fuska tace ƙawata lafiya ? Kice Jamila Musa tace a sakeku a riƙe miji , ba haka nake nufi ba , kudai fahimci inda na dosa. }} cikin ƙan²nin lokaci ta gama dafo abincin ta kawo mata , da farko tace Hadizar ta miƙa mishi , Zainab tace a , a ki kai mishi mana… Wai ita a dole nan tayi fushi wai wallahi bara takai mishi ba tunda jiya yace ana cinye abinci da wuri , {{ ba dole yayi miki faɗa ba ? Kin san wahalar daya sha ya samo ? Wace ce ke da baraya yi miki magana ba ? Ke kaɗai ya ɗauki alƙawari zai ciyar , yasharwa , tufatarwa , ilimantar magani idan baki lafiya wurin zama da kuma kyautatawa a gaban magabatanki haka ya ɗauko alƙawari , baice dake da ƙawayenki ba , ke kaɗai ya biya sadaki aka bashi kuma yayi alƙawari ya ɗauko ki. Duk abinda yayi ko ya bari kikayi da dukiyarshi ko abincinshi da komai nashi tou wannan shine kyautatarwa. Idan kuma bai fita haƙƙin naki ba zai haɗu da sakayya. Akan me zaisa ya samo abunshi ki wulaƙanta mishi ne ? Ko kece kike nemo mishi kuɗin ? Ba kuma nace ki riƙa yiwa mutane rowa ba , idan kinji maƙota ki noƙe risho. Ba rowa zakiyi ba , (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); abinda ka bada shine naka. Kar kuma kina cin abinci idan wasu suna zuwa ki ɓoye kiƙi basu. Ko ki daina fita haƙƙin masu haƙƙin ku basu ba , kar abun duniya ya rufe miki ido. Ki bada , wanda kika bashi zaiji daɗi. Kuma zaiyi godiya da addu’a wa mijinki Allah ya ƙara buɗi da rufin asiri. Bana nufin kiyi rowa wa mutane a , a , ba haka ba , ina nufi dai abun komai kiyi shi dakai… Bawai duka “yan anguwar ku zaki ciyar ba , sai ki duba dai² ƙarfin mijin naki , wani yana da ikon ciyar da jaha ɗaya ma , amma mugun marowaci ne , tou karki almubazzarar masa amma a hankali ki riƙa nuna masa matsayin kyauta da kuma kyautata ma wanda baya da ƙarfi sai kiga a hankali yau da gobe ya rage , wani kuma yana san ya ciyar amma baida ƙarfi , kawai dai duk abinda za’ayi a riƙa sa nazari tunani da kuma lissafi… }} shine take fushi dan yace abinci yana saurin ƙarewa. Shin tasan dalilinshi nayi magana ne ? Ga nauhi yayi mishi yawa , gidansu shine yake riƙe dashi , ga Allah suka dogara shine sukayi ma zuru , itama gidansu Halimar ana aika musu da kasafi duk watan duniya , tou ke zaki nuna masa yadda zai kyautata a rayuwa ? Wace ce ke ? Daga “yar karo baki kau ba fa….. Sai wani kumburin banza take tana cika fuska tunda taga gareta ya miƙa wuyanshi. Mai abun hana miji idan ya buƙata , waye yace miki hana miji haƙƙi shine zai siya miki mutunci ? Tou idan dai wannan shine mafita a gareki zero…….
Dakel Zainab tasa Halimatu takai ma mijinta abinci , tana zuwa ta dungura mishi tayo waje. Shi kuma yaso taɗan zauna yana ci ana ɗan tattaunawa irin nasu na ma’aurata , amma ita ba ruwanta tunda dai ta samu ya ɗaure mata ƙugu zataci tasha tayi gulma tou an biyata , sai idan an kawo kayan mata ta loda ta riƙa mishi ƙarya yana bata kuɗi , ita kuma taita loda ma cikinta kamar akuyar mahaukaciya…..
Yau babu abinda na girka dan tunda na kwanta bacci sai bayan la’asar na farka , bai kuma wani tasheni ba saida na gaji na tashi dan kaina. Babu inda ya fita yaje saboda bayajin daɗi kuma ma ai dama shi ba ma’abocin fitar rana ba ne. Ganin na kasa tashi ne yasa aka kawo mishi abinci daga gidansu , na nashin dandai ina da cikin amman da ko ba abinda zanyi mishi saiya tasheni dan dai ya ɓatamin rai. Ba abinda naci tun kalacin safe sai bayan sallah isha’e na jiƙa garin rogo { garin kwaki } kuma Dikkon nasa da kanshi a siyomin , dan bana ra’ayin abincin da aka kawo. Shine yasa aka kawo buhu ɗaya. Bayan yayi faɗa wai salan inje inba babynshi wahala zanci wani gari bana daijin magana , nace baby ne zaici garin ai bani ba , wai babu wani ya faɗa yana hararata nace da gaske shine yasa aka kawo.
Bedroom na sameshi zaune saman gado da irin zaman ɗazu yana kallon ƙwallo. Kusa dashi na zauna , ina zama ya gyara min zamana tare da matsowa ya kwanta ya ɗora kanshi a jikina ya riƙe ƙuguna da duka hannayenshi yana kallona , nima kallonshi nayi tare da cewa tashi muci , ɗauke idonshi yayi daga kallona yana kallon tv yace me ye ? Gari , murmushi yayi me sauti yana cewa Allah ya sawaƙe , garin ne Allah ya sawaƙe ? Ah ni bana iya cin garin gaskiya sai kace inyamuri….? Aini inyamurar ce shi yasa zanci , shiru yayi bai sake magana ba , ya ɗauki wayarshi yana duba dokuna…. Shikenan tunda bara kaci ba bari in tafi nayi maganar ina ƙoƙarin tashi , riƙeni yayi sosai yaci gaba da abinda yakeyi a waya….
Ni tafiya zanyi , ba tare daya kalleni ba yace kinyi fushi ? Ey , tou ina ci kawo min cokali , ai bada cokali akeci ba , da me akeci ne ? Da hannu , tou bani ya ƙarasa maganar yana buɗe bakinshi ba tare daya kalleni ba… Ai haka kayimin haggunce , ya zanyi ? Ka tashi…. Tashi yayi zaune amma har yanzu hankalinshi yana kan wayarshi saidai bakinshi a buɗe yake , bashi nayi , riƙeshi yayi a bakinshi tare da ɓata fuska ya taɓe baki yana juyashi , ƙara ibowa nayi. Da garin a bakinshi yayi magana cewa dan Allah An mata ki kyaleni kinga banda lafiya….. Dan Allah kaci , kallona yayi a sakace yace baya tafiya , jeka dashi kawai ka kora da ruwa….. Idan banci ba zakiyi kuka ? Dariya nayi dan yadda yayi maganar kamar ƙaramin yaro wallahi. Shagwaɓa tana mishi bala’en kyau kuma yana burgewa idan yayi , hada hawaye. Na faɗa ina kallonshi da irin kallon da yakemin. Ɗan kauda kanshi yayi gefe tare da shafa kanshi yaci dakel , yace ngode. Hahahaha bawan Allah , yau da Jiddah tana nan da nace mata Dikkon ma da kowa da kowa yake taƙa dashi ni nasa ma yaci garin kwaki dan ubanta….
Aimu dama mun saba , kuma ni ban manta ba har yanzu nasan martabar gari , duk irin matsayin da nake a yanzu baisa na manta da rayuwar baya ba. Ai gari yayi mana kuma mu bama wulaƙanta shi duk matsayin da mukaje muna tare da gari gaskiya , kuma ina ƙara godiya da Allah yasa nake a wannan matsayin , haka nan naji ina sha’awar garin. Na ɗan haɗo rayuwar baya da yanzu ! Nayi tunanin nima bazan iya ci ba , ashe dai zan iya ? Allah ya ƙara yalwata arziƙin Dikko amin…. Da gefen ido yake kallona har na gama ci. Saida na gama ya kalleni ta gaba yace sannu , yawwa na faɗa tare da tashi dan fitar da filet in , idan kin jiye kizo , ni bazan dawo ba , ki dawo nace miki , ban sake magana ba na nayi gaba , tana fita ya tashi dakel yaje ya ɗauki cingom yabi bayanta…..
Ɗakina na sameshi kwance yana waya , ɓata rai nayi tare da samun can gefe na zauna na ɗauki wayata , text in Mai gilashi ne kaɗai , ban zo ba , me yasa ? Idan naga D ‘ K baya nan in kirata dan Allah , yau D ‘ K bai fito ba lafiya ? Ko har yanzu baida lafiya ne ? Inyi ƙoƙari in riƙeshi gida na kwana 3 kar in barshi ya fito in rufa mata asiri don girman Allah za tayi wani aiki , kuma inzo makaranta duk yadda za’ayi idan Allah ya kaimu inzo makaranta dan Allah…..
Taya zan riƙe Dikko a gida in hanashi fita ? Abinda ma baya yuwuwa ne gaskiya. Wane aiki ne zatayi ? Koma dai miye Dikko bai zama , yanzu ma jira yake dare yayi ya lallaɓa ya fece abunshi , zuciyata kuwa cewa tayi ai saidai ki jashi kuyi faɗa kawai tunda dai (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); yace bazai dakeki ba tunda kina da ciki. Ci gaba nayi da cika fuska ina ɓata rai , bayan ya gama waya yace An matana miye ? Dikko wai mema yasa kaje kayi ma karuwa liƙi ? Da yanayin rashin jin daɗi yace ba karuwa bace ba , Mamanta fa ƙanwar Dady ne. Ni bana san sanin wani dangantaka ko alaƙa , amma me yasa baya bakimin magana ba sai yanzu ? A lokacin abun bai shafeni kamar yanzu ba , yanzu kinajin fitina kenan ko ? Ey fitinar nakeji , tou ai ba ƙyaleki zanyi ba , zaneki zanyi. Fashewa nayi da kuka sai abun yaci gaba da zungurar min zuciya kamar yanzu ne akeyin abun wani irin azababen kishi yaci gaba da ƙwal²rmin zuciya. Da videon da Yusra ta turo mishi gaba ɗaya na ƙwace na fara ɗuɗɗurma ma Sharifa da Yusra zagi , da sauri ya taso yazo kusa dani yace haba An mata meye haka ? Cikin kuka nace dama ai dole zakace zaka dakeni tunda na taɓo karuwowin ka , kiyi a hankali kinsan bamu kaɗai ba a gida , so kike ace kin rainani ne An mata ? Ace na rainanka kaima ai raini yasa kaje kayi mata liƙin a gabana , da Jiddah ce ka isa ? Saini duk wani shararka da komai akan An mata. Saina faɗar da ƙarfin dandai kar asirinka ya tonu asan kana da karuwowi , salati Dikko yayi tare da cewa idan dai kika kasheni hankalinki ya kwanta… Nine ma nake da karuwowin ko ? Ni An mata ? Ya ƙarasa maganar yana riƙoni jikinshi , fizgewa nayi na miƙe naci gaba da kuka ina zagin su Sharifa.
Riƙeni yayi da ƙarfi. Ya rumgumeni jikinshi , bayan wani lokaci ya sassauta riƙon zuwa riƙo da tako mai kyau ya fara maida lumfashi da salon da yasan zaisa na ɗauke wuta da wuri , ƙasa² na farayi da murya cikin shashshekar kuka ina cewa amma ai kasan baka kyauta ba , yi haƙuri yarinya na yake faɗa yana ƙara sautin. Kasala ta fara zuwa. Dakel na sake furta kuma na ɓata dakai , ai bamu ɓatawa An mata yayi maganar yana fara kukan kissarshi , wani ɗan iskan kuka yakeyi cikin kurman sauti maisai jiki ya mutu da sauri , sai ya riƙayin wani jaririyar ƙara “yar ƙararrama yana numfashi , shidai yasan yadda yake abunshi amma dole dai idan kikaji sautin sai tsikar jikinki ya tashi , kasala da san kasancewa dashi ya tattaru ya lulluɓeki a lokaci guda dan da shagawaɓe yake fitar da sautin sai kuma ya ƙadaddabe ki da raunanannen riƙo , hmmm Dikko ? Bayajin magana kona misali. Saida ya gama sinsineni ya fara lasar bakina , muƙus nayi shiru , a gajiye yaja ni ya ɗora saman tsakiyar gado dakel. Yana maida numfashin wahala da yanayin rashin lafiya cewa bakijin magana kuma tunda kika ɓatamin rai naushin mai ƙarfi zanyi , riƙeshi nayi ina kuka , kallona yayi a shagwaɓe yace me ye kuma ? Yayi tambayar yana ɗaure fuska , na bari , a , a ya faɗa badai bakijin magana ba ? Yi haƙuri. A wahalce ya gyara kwanciyarshi yana cewa tou zoki bani haƙuri ya ƙarasa maganar yana min dogon kallo ranshi a haɗe…….. Matsawa nayi kusa dashi nace yi haƙuri , kallona yakeyi har yanzu , bayan kamar mintuna biyu yayi murmushi tare da ɗan tattauna cingom da salon jan rai sannan ya huroshi irin abun nan kwai ya kuma riƙe kwan. Da kanshi ya nunamin in sauka muje , sauka nayi. Shima ya sauka ya biyo bayana har ɗakinshi , inda aka ajiye kayan da ya dawo dasu daga tafiya yace in buɗe inyi ta sakawa yana gani. Ya ƙarasa maganar yana kwanciya saman gado,
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Wasu irin riguna ne masu kyau da tsada , bawai baƙaƙe bane ba dukansu kaloli ne masu kyau launin “yan gayu , takalma masu kyau haɗaɗi suma , sai sarƙa da “yan kunne “yan hannu da zobe kala biyar kuma duk na zinari ne masu masifar tsada. Manya² bawai “yan kucilaye ba kamar na wasan yara. Jakunkuna turaruka masu ƙamshin gaske da dai duk abinda yasan zai haɗani ya siyo , haka naita gwadawa ina saka takalmi ina bada step yana daga kwance yana kallona , idan bai burgeshi ba sai ya gyaramin , idan na burge shi da yawa yana daga inda yake zaice inzo , idan naje saiya sumbace ni yace An mata mai kyau. Ko kuma yace bara in miki hoto Yarinya….
Mai gilashi yau ta kasa fita zuwa wurin Alhaji. Sai zagaye takeyi tsakanin ɗakinta da ɗan madaidaicin tsakar filin BQ insu , meke faruwa ne ? Sultana ba reply kuma ba fita ba kira ? Kardai zuwa tayi taje ta nunawa Dikko cht in ? Kila ana can ma ana faɗa , ta shiga 3nta , ɗaki ta koma ta ɗauki wayarta ta fara kiran Sharifa…..
Babu wani daɗewa ta ɗauka , ko gaisuwa babu Mai gilashi tace alherin Allah dai ya kaimu wannan rana amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida , ni Mai gilashi ? Oh , naga Nana Ade a gidan amarya , ashe ina da rabon ganin wannan rana……….? Hmmmm , ׳ Sharifa tayi dariya cike da izza ita amaryar Dikko , Mai gilashi taci gaba da cewa ni ina nan na duƙa addu’a Allah dai yasa karya haɗaki da matarshi. A yatsine Sharifa tace ni wannan ai ban ɗauketa a mace ba. Kinsan da haɗemu zaiyi sai nayi wani nazari nace masa bana so kowa ya raba mata gidan ta , yanzu ke ina ne zai ajiyeki ? Cike da kwarin guiwa tace G R A , wannan gidan duk ke ɗaya Sharifa ? Cass ni ɗaya abuna daga ni sai bataliyata ga kuma Dikko nawa abuna , kai zanfa zuba tasha danni wannan banzar matar tashi banajinta wallahi. Dan bata da ban²nci ita da kashin da nayi a toilet ruwa kawai zan sheƙa tabi 5v abunta…. A hankali dai Mai gilashi taci gaba da zungurar mata ciki , daga ƙarshe tace ko tayi magana da Dikko ne ? Tace ai zasu haɗu 1:00am a G R A , Mai gilashi tace idan sauran kishiyoyin naki sun bar miki shi ya samu zuwa wurinki ko ? Sharifa tace waye su ? Bana ce komai ba , amma ni na faɗa miki yau gobe da kuma jibi Dikko ba naki bane ba , na waye……? Murmushi Mai gilashi tayi tare da cewa na wata gogaggar ce , tana can ta ɗaukeshi sai sun dawo………. Tana faɗin haka ta tsinke kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya….
Ya Yazeed ni wallahi na kasa gane wannan farashi da kake magana. Jiddah da Yazeed zaune a mota kuma a gidan Rabiya ake zancen , dan jiya da Dikko ya dawo daga tafiya da Papi ya maƙale yace shi zai zauna wurin Nabeela sai Momy tace ita Jiddah ta tafi can gidan Rabiya ta zauna , kora ce da hali akayi mata amma ta kasa ganewa jakar. Shiru Yazeed yayi yana kallon sitiyari , Jiddah tace Ya Yazeed kayi shiru baka ce komai ba…..!!!
Cike dajin haushi yace tunda bakya ganewa a daina maganar ko dole sai anyi auren ne wai…? Haƙuri ta bashi tare da cewa bara in kira Nabeela. Tayi maganar tana danna wayarta dan neman lambar Nabeela , anshe wayar Yazeed yayi daga hannunta yana cewa kema kanki zawara baki fahimta ba taya ita Nabeela zata sani ? Shiru tayi tana saurarenshi , Yazeed yace waye zai saci kayan wani tou inba ɓarawo ba ? Jiddah tace gaskiya , shi kuma yaci gaba da cewa ni sakarai sai in biya sadaki lefe wurin zama abincin da zakici har na tsawon sati biyu da kuɗin hidima sai su tashi a banza bayan kwana biyu in sakoki alhalin ban gama gurje kuɗin ba….? Tou ya akeyin abun ne ? Yadda akeyin abun tsarin da komai kawai ki bada miliyan 5 zanji da komai , Ya Yazeed yanzu banda kuɗi duka² fa a account ina baifi miliyan ɗaya ba ,
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kallon rainin wayau yayi mata yana cewa karki ɗauki Yazeed sakarai mana ? Wallahi kuwa Yaya ta faɗa kamar zatayi kuka , kina nufin duk zaman da kikayi da D ‘ K haka nan kika fito fayau ba wasu manyan kuɗi a account ? Yaranshi ma sunyi kuɗi bare kuma ke matarshi ? D ‘ K da macen zai bari kiyi talauci ? Nafa san D ‘ K fiye da yadda ke kika sanshi. Halinshi da komai na rayuwarshi ni ina iya rubuta littafi Jiddah , ai bana tunanin nan da shekaru biyar miliyan biyar za tayi miki wahala wurin bayar da ita a matsayin kyauta. Bare kuma wannan ba kyauta zaki bayar ba kece za’ayi ma hidimar dasu , ina gwala²i ? Ina kuɗi Jiddah……? Wallahi duk na siyar na ba malamai , sakaran kallo yayi mata , taci gaba da farfaɗo mishi irin manyan malaman data bi amma har yanzu shiru kuma kullum idan ma Ya D ‘ K ya ganta kamar zaici ƙaniyarta ne. Yazeed yace tunda kinbi malamai ba’a dace ba ki zubo hannun jari a asusun banki na , zaki sha mamaki , Yaya banda kuɗi wallahi , Yazeed yace idan ba kuɗi ba aure karta sake kiranshi idan bata samu ba , daga haka fira ya tsaya. Yazeed ya tafi ita kuma ta koma ciki da tashin hankali , ita dake so suyi aure ya sakota ta koma gidan Dikko ? Ya kuma Yazeed zai rusa mata bajet haka ? Dole ma a samu kuɗin a daren nan…
Tunda ta shiga take tunanin inda zata samu kuɗi. Ta juya ta zaga ta rasa yadda zatayi , tayi waya wa ƙawayenta ko zata samu duk kowa yace babu , Ashiru ta kira yace shi baima san yadda miliyan take ba bare kuma miliyan 5 , tambayarshi tayi idan ta tambayi Dikko zai bata ne ? Ashiru yace tou shidai bai sani ba amma ta jaraba kila ta dace tunda su ɗin “yan uwane. Bayan Ashiru ya gama waya da Jiddah ya kira Dikko yake faɗa mishi. Tun kafin Jiddah ta kira Dikko ya tura mata miliyan goma , shi a ganinshi idan ta nema bata samu ba zataje tayi iskanci ne , shi kuma dudduniya abinda ya tsana yaga mace tana barbaɗewa….. Shi kuma Ashiru wallahi da yasan Dikko zai bata kuɗin da bazai faɗa mishi ba , dan koshi yana iya bata kuɗin amma haushinta yakeji kamar ya babbakata da wuta tunda taba Papi fiyaya². Dan yasan bata iya tunkararshi da zancen ya bata wani abu saboda abinda tayi ma ɗanshi. Shi kuma Dikko ba haka yake ba , idan dai ta haɗoku zaiyi hayaniyar shi yayi bobbotanshi tare da rufe idanuwanshi ya zazzaga ma mutum rashin mutunci dai² iyawarshi , kuma wani dalilinshi bazai hana shi ya kyautata maka ba , haka ta faru dashi da Yazeed ai. Lokacin da yake tarayya da Sultana akace ya korashi daga company yace su ƙyaleshi , yanzun ma bashi ne ya koreshi ba. Ashiru ne kuma ya kawo Abbakar ya ɗora , da Dikkon yayi magana yace Mai gida haka za’ayi , kuma shikena ya wuce wurin……
Wani irin ihun farin ciki Jiddah ta kwarara , lokacin da taga kuɗin da ya shigo account inta kuma daga Dikko ne , tayi murna sosai ta fara kiran wayarshi , a kashe yake , ita kuma a tunaninta na neman biko ne , dan haka ta zauna ta tsara yaudararrin kalamai ta aika dasu ta whatsapp tasan komai dare zai hau kuma zai gani , kila yana jin kishi ne Yazeed zai aureta shi yasa ya fara neman shiri , ita kuma batayi tunanin Ashiru ya faɗa mishi ba a ganinta kai tsaye ya bata dan kyautatawa , ai tasan wannan sharar fage ne idan manyan suka taho account inta baya ɗauka. Kai Yaya D ‘ K mahaukaci ne , aiko bayan kwana biyu zatace ya bata 20 tasan zai bada 40 ne kaɗan ne daka aikinshi , kai ai dole ma ta koma a ci duniyar nan da ita , tayi murna har ta rasa irin wacce zatayi , gaskiya Dikko baisan darajar kuɗi ba haka nan yake nemansu mutane na cinyewa , a nata tunanin kenan………..
Bakajin komai sai ƙarar ragonshi dake fita { munshari kenan } kwar , kwar , kir² kwar² , da sanɗo ta shiga ɗakin bayan ta tabbatar da babu mai ganinta har jikin wadrof, a hankali ta buɗe wadrof ƙiyyyy , ƙarar buɗewa , a ɗan tsorace ta cije haƙoranta tare da yaƙewa cikin yanayin tsorata ta kallo inda Dady yake kwance yana jan rago. Maida hankalinta tayi wurin neman takaddun gidajenshi , saida ta sabko kayan tass sannan ta taka tayi sama bayan wani lokaci ta sauko da wani fayil , a ƙasa ta ajiye ta dudduba tsadajjin gidaje da Dady yake taƙama dasu a cikin anguwannin “yan gayu da akeji dasu ta ɗauko har 3 ta ajiye ƙasa sannan ta maida sauran ta mayar da kayan yadda suke , ta rufe weldrop in ta fice yana nan kwance kamar asarar safe yana bacci….
Itama a wurin Sultana haka ta kasance , tana kwance gefen mijinta kamar asarar itama shi kuma yana cht. Murmushi yayi kaɗan tare da juyawa ya ɗauko bluetooth wurin dawowa ne ya bugeta , da sauri ya ajiye wayarshi yana rirrigata irin yadda akeyi ma yaro idan ya farka , riƙeshi tayi taci gaba da bacci , ajiyar zuciya ya sauke. Cikin jin daɗi ya lumshe idanuwanshi a gajiye yana (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); numfashi kaɗan. Saida ya tabbatar ta koma bacci ya cireta daga jikinshi ya gyara mata kwanciya ya lulluɓeta , a hankali ya sauka daga saman gadon ya ɗauki wayarshi ya koma palo….. { kunga bai iya gani ba , amma yau da gobe tasa zaije ya kalla , tou a hankali suke raka mana mazaje suna dawowa , idan abun ya ɗaure haka tun tana mishi tayin kanta yana a , a , a hankali zata labbaceshi ta nuna mishi ai ba wani abu bane ba. Da kaɗan take ɗorawa idan kuma tafiya tayi nisa haka zata rufta miki miji , daga nan sai ta Allah , karuwa ba…. }}
Kashe fitila yayi bayan ya shiga palo , ƙasa ya kwanta saman kafet ya sargafa bluetooth a kunnenshi sannan ya buɗe cht in da Yusra ta turo mishi. Hotunan ya fara kallo da yanayin mayata , bayan ya gani ya kunno voice note ya saurara a kasallance ya furta mata yana ci gaba da kallon hoton Yusra , a voice note kuwa lallausar magana ce da manyan kalaman irin na “yan tasha wanda yaji sunyi mishi dai² da sauron kunnuwanshi , daya kai ƙarshe sai ya sake kunnuwo , taɓe bakinshi yayi tare da fara kallon video , da sauri ya rufe idanuwanshi yana murmushi , amma yanajin maganar da takeyi lokacin tana video , buɗe idonshi yayi ya sake kallo yana murmushi , bayan wani lokaci ya sake rufewa yana dariya….. Gyara kwanciyarshi yayi yana miƙa alamun saƙo ya fara shiga jikinshi. Dariya ya sakeyi mara sauti sannan yagoge ya kifa kanshi saman pilown da yake kwance yanajin wani baƙon yanayi yana shigarshi. Bayan wani lokaci ya ɗago yaci gaba da dubawa bai bawa Yusra amsa ba , ya duba saƙon Sharifa itama baice mata umm² ba ya wuce wurin na Jiddah , kallon hotonta yayi data turo tayi kyau sosai wai ga Jiddah tana godiya Yaya , itama bai bata amsa ba , ya duba saƙon da wata number ke turo mishi hotuna , gani yayi ya wuce yana duba na abokanshi , zuciyarshi kuwa sai san ƙara jin labarin Yusra takeyi , komawa yayi ya gogeshi da hotunan yasan idan An mata ta gani kuka zatayi…. Ɗayar wayarshi ya ɗauka ya fara kallon hotunan da yayi mata ɗazu , da wanda itace tayi musu tare , bayan ya gama gani yace An matan Dikko……
Yauma shirye na fito cikin kayan makaranta amma Dikko ya rufe ido wai babu inda zanje , ai da kwata² na daina zuwa makaratar. Dan naga ya dawo daga tafiya yana huta gaji shine zance makaranta , kuka na farayi tunda yanzu na lura kukan shine ƙarfina a wurinshi , shikenan muje in kaiki ya faɗa yana cewa jirani ,
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
_kiyi ƙoƙari ki riƙeshi gida na kwana3 karki barshi ya fito…._ maganar Mai gilashi ta dawomin da turomin a saƙo jiya , binshi nayi ciki ina ƙara yawan kukana nidai bazanje dakai ba , idan dai ba tare dani ba saidai ki fasa zuwa , zama nayi gefen gado nace tou naji na fasa ina cire takalmina. Kallona yayi cikin ɓacin rai yace wato ni ban isa in jera dake mu fita tare ba ko ? Ko kuma karki tafi dani ace kinzo da tsoho ? Tou sai kinje makarantar wallahi , kuma nine da kaina zan kai daga yau ma idan ina nan nine zan riƙa kaiki ko ina tunda na lura so kike ki ɗaukeni wani bansan abinda nake ba , nine ma tsohon ? Yayi maganar yana shafa gefenmu , to idan dai dan wannan na zama tsoho yau saina kwasheshi , da sauri nayi wurin nace yi haƙuri dan Allah , rufe idanuwanshi yayi da yanayin haukarshi yace ke…….. Saina cireshi duka wai shekarata nawa ne ? Ke baki da lissafi ne ? Ko dan kinji ina ce miki yarinya ne ? Tou nima bara in dawo yaron tunda kin rainani dani dake duk mu haɗu muyi yarintar , ya ƙarasa maganar yana nufa hanyar toilet , da gudu nasha gabanshi cikin kuka na haɗa hannayena ina cewa na roƙeka da girman Allah kar kayi min haka , daka min tsawa yayi tare da cewa matsa ki bani wuri ya janyeni ya shiga toilet in , binshi nayi ina ƙara yawan kukana dan Allah Dikko kar kayi , so kake idan na fita naga masu gemu in riƙa kallonsu ? Nayi maganar cikin sanyi , tou me yasa kikemin abinda bana so ne ? Bazan ƙara ba , nunani yayi da ɗan yatsa yana cewa daga yau ko me kikayimin zan cireshi kuma banajin yi haƙuri , goge hawaye na nayi tare da jinjina kai nace na yadda , maimatawa yayi a karo na biyu cewa ko me kikayimin. Zan , ya nuna da hannunshi yana fitar da sauti mai kamar fito , kenan zai cireshi. Nace na yadda , tou wuce muje yayi maganar yana murmushi , fitowa mukayi saida ya tsaya gaban madubi ya sake gyarashi kalar fizgar hankali sannan yace muje yayi gaba…..
Binshi nayi ina sauke ajiyar zuciya. Gaskiya yana da kyau maza ku san abinda yake ɗaukar hankalin matayenku daga gareku , kuma ku ɗan riƙa cancaɗewa kuna yin kalar burgewa a gaban matayenku , ita fa mace abu kaɗan ke ɗaukar mata hankali , idan dai bakayi ma matar ka gayu ba tou gaskiya baka haɗu ba , wallahi wasu mazan ko ɗaki ɗaya baka iya haɗawa dasu , ba wanka bare kuma kasa ran samun ƙamshi a jikinsu , yadda yaje kasuwa ya dawo haka zai dawo ba wanka ba wanke baki duk ƙurar kasuwa ta gama barbaɗeka , ita kuma matarka tasha wanka taɗauki fili da gayu kamar zataje gasar wanka , ta haɗu tana ta zuba ƙamshi kamar matar sarki sai kace a haka zaka zo ka wani rungumeta , tsakanin ka da Allah kayi mata adalci kenan ? Gaskiya duk mu haɗu mu gyara gaba ɗaya sai a zauna lafiya. Idan kuwa ba haka ba ta sauke ka daga saman gadonta har sai ka koyo wanka wanke baki da kuma shafa turare…. {{ ba cewa nayi ki saukeshi ƙasa ba , ah kidai ɗan gyara mishi dan kema zakiji daɗin tafiyar idan da ƙamshi , ai kindai gane ba , kinsan wasa bai tafiya idan ba abokin wasa haka kuma baya daɗi idan babu abun wasar , kenan wancan hikimar da nake magana tafi daɗi idan da gyaran fili }} haba kuma kuyi koyi da Dikko mana. Ku zama “yan gayen mazaje shalelen matayenku.
Da sauri Ashiru ya fito yana cewa Mai gida bari in kaita , bai mishi magana ba ya wuce wurin mota ina bin bayanshi , da kanshi ya buɗemin na shiga ya rufe , wurinsu Ashiru ya koma suna gaisawa , duk banajin me suke cewa bayan ya gama ya dawo yana ɓata rai , juyar da kaina nayi nima ina fushi har muka fita daga gidan…..
Har mukaje makaranta baimin magana ba , nima banyi mishi ba. Tuƙinshi ya jawo hankalin mutanen dake kusa dan baya tuƙi da natsuwa kwata² , fita. Yace bayan yayi (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); parking , matsawa nayi na shafa fuskarshi nace amana nayi maganar idona cike da hawaye , naji jeki , saida na sumbaci gemunshi sannan nace ina sanka na faɗa ina kallon idonshi , murmushi jin daɗi yayi yace Allah yasa da gaske kike , da gaske nake Dikko , riƙeni yayi tare da cewa zanzo in ɗaukeki idan kun tashi , kuma ki daina ɓatamin rai An mata kinga banajin daɗin abinda kikemin , wallahi maganar da kikamin shekaran jiya bakiji yadda naji ba har yanzu zuciyata ciwo takemin , ki daina haka babu kyau , to , ngode ya faɗa yana ɗan gyarawa. Nima godiya nayi mishi tare da fita , addu’ar Allah ya tsare yaimin nima nayi masa Allah ya tsare hanya , saida ya tafi na wuce……
A aji kuwa Mai gilashi ta tambayeni yadda aka ƙare jiya , kai tsaye nace mata janshi nayi mukayi faɗa duk dai abinda ya faru na faɗa mata. Cewa nayi kuyi faɗa ? Ta tambayeni ? Waike baki iya irin ɗan karuwancin nan ba ? Waye yace miki da faɗa ake hukunta namiji ne ? Ai namiji bakiyi mishi hauka , da sannu kike latsashi , kuma da kinja kika ga yaja sakar mishi ki kuma bishi da swry My President. Shiru nayi bayan wani lokaci nace nima yadda kika ganki a da haka nake , wani abokin Babana ne yayi min asiri naɗan firgice bayan kuma an samu nasara lalatawa na zama sai a hankali , tunda kinga abinda nakeyi dama bani ce nakeyi da kaina ba , tsoki Mai gilashi tayi. A hankali ta ɗan (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); fara labarta min halin Sharifa tare da cewa kuma idan ta faɗamin na daina zuciya ina aikawa Dikko da saƙon zagi , in kwantar da hankali in bata haɗin kai yauma inyi ƙoƙarin riƙe Dikko karya fita domin tana shirya ma Sharifa gadar zare ne , so take ta rifto cikin rami ita kuma sai ta bita da ƙasa ta rufe , tana min maganar taga wani malami ya wuce , miƙewa tayi tare da cewa bari inje wurin wancan mai zanzaron inji me yasa zai ɗauro mana ƙugu yana tayar mana da hankali , tana faɗin haka ta fice daga ajin.
Har aka tashi makaranta Mai gilashi bata dawo ba , Dikko ne yazo ya tafi dani gida , ina ta tunanin yadda zanyi in hanashi fita a daren yau , dan nayi imani yadda ya samu sauƙin nan tou fa lallai babu abinda zai hanashi fita………
*JAMILA MUSA….* ce.