
Ta idar da Sallar mangariban kenan sai ga shi ya shigo Cikin Jallabiya Sabuwa mai Ruwan Madara Ruwa na Diga ajikinsa Mikewa tayi Hijabi ne ajikinta suna kallon junansu kamar wasu masu warkewar makanta.
Ganin Ruwa na Diga Daga wuyansa ne Tace”Ya Imu baka Shafa mai bane..?
Yana yin gaba Wajen Darduman yace”Ni bai Dameni ba..Taho muyi Sallar..!
Yana gaba tana bayansa ya Tada Salla Sai da sukayi isha”in suka idar kana Sukayi Sallar Raka”a Hudu na Godiya ga Allah bayan sun Idar Imran ya Daga Hannu yayi ta addu”a Duka Rabin addu”ansa na Allah ya Jikansu Anni ne har Sai da ya kusa kara saka Inteeesar kuka,Sannan ya Rufe da addu”an zaman lafiya a tsakaninsu.
Sanda suka Shafa addu”an ya juyo yana kallonta Wayarsa yadan Danna yana so yaga Lokaci 10 ta wuce na Dare yana kallonta yace”Kina jin yunwa..?
Kai ta girgirzamai alamun A”a ajiyar rai ya sauke yana fadin”Kinsan me..?ni fa imran na Dabam ne shiyasa ko Irin kazan nan da ake siyoma amare bansani ba Sagir ne ya san irin abubuwanan ni Shirme na Daukesu yace a gayamiki zai kawo miki..!
Kanta na kasa tace”Bakomai..Ni na yafe..!
Imran kallonta kawai yake yi yana jin wani Salama kafin yace”Gobe zaku Fara Jarabawa ko..?
Ta gyadamai kai kafin ya cigaba da Fadin”Nima gobe zani wajen aiki Karfe nawa ne sai na Fara ijiyeki kafin na wuce..!
Tana kallonsa tace”8:00am na Safe ne..!
Kansa ya gyada kafin ya Mike yana Fadin”Is ok..Ki kwanta Kiyi Barci and Don”t Stress ur self kice zaki karatu kin ji ko..?nasan ai baki da wasa Insha Allahu komai zai zo da sauki..!
Gyadamai kai Tayi tana Mikewa Idonta yayi Raurai ita kadai Zata kwana.!?
Bata samu bakin mgana ba Har ya Fice Lokaci Daya yana Fadin”Kiyi addu”a…!
Daga haka ya jawomata Kofar ya Nufi Dakinsa yana Sauke Numfashi.
Shifa bai iya kwana da Mutum a Daki ba Ko Namji ne ballatana Mace baisan ta ina zai fara ba..!
Bama haka ba ai in taga yanayin kwanciyarsa sai ta Rainasa.
Inteesar kuwa haka ta kwanta a Darare tana jin Tsoro ba batajin Motsin kowa ko agida Watarana Ita da Umma Take kwana,yau dai taji kewa sosai haka ta Dungule ita kadai Tana Jin Tsoro gata a sabon Wajen da bata Saba ba ita kadai Saboda gajiyan Biki Da suka sha yasa Barci ya kwasheta bata sani ba barci mai nauyi kamar yadda ya sace Imran yana Tsaka da Duba wani aikin da zai bama Manager Mr Sulaiman gobe.
Shakira..
3/28/22, 18:35 – Ummi Tandama😇: GMB2🅿ï¸?25
Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488
Barci ne suka yi na gajiya Wanda yasa suka makara basu sani ba Kuma Dayake Kusa da gidan ba Masallaci Sai Dagachan nesa ne,Shiyasa har akayi Sallar asuba aka idar Imran bai ji ballatana Inteesar Datake baje Tana Barcinta Bilhakki da gaskiya..
Allah ne ya Tada Imran da Misalin Karfe 6:30am na Safe Koda ya Farka ya Duba agogon Wayarsa sai ya Zaro ido ya Mike Zaune da Sauri Lokaci Daya yana Dirowa Daga kan gadon laptop dinsa ya Tattara wacce barci ya Kwasheshi yana aiki akanta ya Fada Tiolet ya makara shiyasa bai Fara yin wanka ba ya Dauro alwala ya Fito Tunani yake yi ko Inteesar ta tashi..?
Ko Itama bata tashi ba..!
Agurguje ya Saka Jallabiya ya Fita Zuwa Dakin Inteesar Knoking ya fara yi mata yana Kiran sunanta a Hankali bai ji ta amsa ba yasa ya Tura Kofar ya Shiga..
Yanayin Kwanciyarta Kadai ya tabbatar mai da itama Barcin Gajiya n e ajikinta yadda ta Karkace kai gefe ko Filo bata Nema ba ko kuma Zamewa yayi bai sani ba.
Kusa da ita ya isa yana Kokarin Tashinta din Gefen katifar yake Duka Kadan kadan yana kiran sunanta Kamar a mafarki haka taji Kiran nata Sama sama yasa ta Bude Idanuwanta Cike da Barci akansa Da Sauri yace Mata”Ki tashi mun makara fa..!
Mikewa Tayi Zaune a Hankali Tana gyara Wuyan Rigarta Daya Zame Imran kansa ya kauda yana Kokarin Daidaita Natsuwarsa baya so idonsa ya kara kaiwa kanta Zata Sa ya rasa Duka Natsuwarsa da Jarumtarsa.
Da Sauri yace mata”Ki tashi kiyo alwala muyi sallah ina Jiran ki..!
Cikin Kasala da alamun Barcin a Idonta ta mike Tana Fadin”Karfe nawa ne Ya Imu..?naga kamar gari ya waye..?
Tafada Tana kallonsa shi kuma yana Kokarin Daidaita Darduma bai kalleta ba yace”zaki wuce kiyo alwala ne ko Zaki Tsaya Tambayan Lokaci..?
Lokaci Daya yana Sakarmata Manyan Idanuwansa,Tura baki Tayi Lokaci Daya Tana yin mika da Sauri ya kalli Gabansa yana Kokarin gyara Tsayuwarsa ganin yadda ta bangaro Kirjinta Sama in ya cigaba da kallonta Wlh alwalarsa sai ta samu Rauni Cikin Dakewarsa yace”Wlh zan yi Sallata in yaso sai kiyi Taki..Bana son Shanshancin banza..!
Ya karishe Fada yana Hade rai jin Haka yasa ta Zagayasa ta Shige Tiolet ya Bita da kallo ta kasan ido Gwara ya Rika mata jan ido kada ta Rainasa Daman ta Fara Rainansa.
Agurguje tayo alwala ta Fito Hijabinta ta Sanya Dake kan gado kafarta ya gani a waje yasa yace”Ke ahaka zaki Sallar..?
Kallon kanta Tayi kafin tace”Rigar fa Doguwa ce Ya Imu..!
Tafada Cikin Shagwaba Dauke kai yayi yana Fadin”U are not Serious..Oya Dauko Wani Zani ki Rufe wannan Siraran Kafafuwan naki kafin Ranki ya baci..!
Yafada Cikin Kaushinsa Kamar ko yaushe kallonsa Tayi sai ta kama kanta Kada tasha mari ganin ya koma mata Imu dinsa Sak.
Wardrope din Dakin Ta Bude ta Dauki Zanin Wani less dinta ta saka tazo Ta Bisa suka yi Sallar suna Idarwa ya Mike da Hanzari yana wani cin mgani ya Fice yana Cemata”Make sure kin Shirya da wuri..Bana son Jira..In kika batamin Lokacin kin san Sauran..Ni ba irin Ya Yusuf bane yana Jiranku kamar wani Direbanku..!
Ai Tana jin haka ta Mike ta Fada Tiolet Tayo wanka Sai da ta Fito ta Duba agogon Wayarta da Munari ta bata Jiya da Zasu tafi 7 ma Tayi a Gaggauce ta Shirya Cikinta ke kugin Yunwa Daman Tun Fara Shagalin nan bata wani ci abincin Kirki ba.
Riga da Sikat ta saka na atamfa Cikin Kayanta ne na Gida da Munari ta Hado mata,Kayan sun kamata sun mata Das.
falo ta Fito sai alokacin ta Samu Damar karema Gidan kallo Tana kara Jinjina ma Baffa Kabiru yayi kokari Sosai Kitchen ta Fada Domin samo musu abunda zasu karya Tayi mamakin ganin Harda Cefene sai dai ba Lokacin da Zata Sarrafa wani abu Gas ta kunna ta samu karamar Tukunya ta Dora Ruwan Zafi Tana kara Duba Kitchen din Tana Godema Umma da Daddy dinta da Kokarinsu akanta.
Ta Duba Taga Harda da kayan Tea,Mirmishi Tayi Munari ta Fadamata aikin Ya Yusuf ne ai kuwa yayi Taimako don inta Ya Imu ne yau da yunwa zasu Fita.
Ruwan Zafi ta Juye acikin Flaks ta Dauko Mug din Kofuna Guda Biyu ta Wanke ta Zubo Ruwan Zafi ta Kwaso kayan Tea din zuwa Falo Saman Dan Madaidaicin Dining din Dake yamma da Falon
Komawa Tayi ta Bude Store ta samu Karamin Filte ta Dibo Snak din da Umma ta saka akayi mata su Donot su Cincin su Cake da sauransu ta debo su kadan bada yawa ba Tana Fitowa Imran na Fitowa Daga Dakinsa Lokaci Daya yana gyara Zaman Net Tie din Dake Wuyansa Shigar Suit Green yayi yau Dayan Hannunsa na Dauke da Jakar Briefcase dinsa da Key din Motarsa.
Ido suka Hada Dashi Shagala Tayi da kallonsa Shi kuma bai bari ta gane Kallinta na kayatar dashi ba Sai ya Kauda kai Daidai Lokacin Data kariso gaban Dining din Tana Fadin”Gud Mrning..!
Yana Duba agogon Radon Dake Hannunsa yace”Mrning..Kin gama Shiryawa..?
Kai ta gyada Tana Fadin”Yes..Ammh ga Tea bazamu sha kafin mu Fita ba..?
Yamutsa Fuska yayi kafin yace wani abu da Sauri Tace”Nidai plz ka bari nasha Kada naje Exams ina Zare idon Yunwa..!
Dariya taso kamasa sai ya Dake ganin yadda Tayi mgana kai ya gyada mata yana Fadin”Ok.5Mn..!
Da Sauri Taja Kujeran ta Zauna Tana Fadin”Bazan ma kai ba..Ya Imu kazo sha faa ba wani abu bane mai Nauyi ba..!
Bazai iya mata gaddama ba yasa ya ijiye kayan Hannunta ya Isa Kusa da ita ita tajamai kujeran Dining din ya Zauna Ta Turamai Mug din gabansa da Flaks Zata Zubamai ya Dakatar da ita yana Fadin”Barshi sha..Kada ki batamin Lokaci..!
Yar Dariya Tayi ta sakarmai ya Tsiyaya Kadan ya Zuba Madara da Bonvita da Siga kadan ya Fara kurba Filet din gabanta ta Turamai Tana Fadin”Madadin Bread..!
Kallonsa yayi kafin ya Dgo yana Fadin”what is dis..?
Inteesar ta waro ido Tana Fadin”Baka sansu ba..?tab ka bar Dadi..Ci wannan kaji..!
Ta Dauko Cake ta Mikamai Bazai iya Ture Mganar Inteesar ba yasa ya Karba ya Gutsira Da Sauri Tace”Ya kaji..?Cake ne ana shansa da Tea..!
Bai ce mata komai ba,sai da yakara Cake din Guda Biyu ya Hada da Tea din kadan ya Mike Duk Saurin Inteesar yana kallonta Tana Turawa cikin Bakin ganin ya Mike Dariya Ta basa yasa yace”Kici a Hankali kada ki tura da yawa kije kina Amai kuma..Ba Ruwana..!
Yafada yana Wucewa Jakarsa ya Dauka yana Fadin”ki Tafi dashi ma in kin Fito Exams din sai kici..!
Mikewa Tayi Tana Fadin”Am ok..Bari na Dauko mayafina da Jaka da wayata..!
Bai mata mgana ba ta kwashi Gudu Zuwa Cikin Daki da kallo ya Bita Kafin ya Girgiza kai Bata Dade ba sai gata ta Fito da bakin Mayafi da bakar Jakar sai Takalminta mai Tudu Duk Cikin kayanta na Gida ne.
Kallon Sama da kasa yayi mata Lokacin Data Tsaya agabansa Tana Fadin”Am Ready..!
Hararanta yayi Ransa na Bacin yadda Zataje Cikin maza da Gyale kuma Sikat din ya kamata Cikin Dakewarsa yace”ba hijabi ne sai wannan Mayafin..?
Inteesar tace”Wlh babu..Duka suna Kaduna Guda biyu ne kuma suna Cikin kayama na gidan mama Duka Goggo Maimunatu Gyale ta sakamin..!
Tafada Cikin Muryan Shagwabar da ya Zame mata jiki.
Karamin Tsaki yaja Kafin yace”Sako sa saman kanki..Da kika saka sa a Kafada kin manta ke da da yanzu ba Daya bane..?
Yafada yana Sakarmata ido Zatayi mgana yace”Bana son gaddama Do as I say..!
Bata da yadda Zatayi ta Warware ta Saka saman kai Allah yasa Babba ne,Makullaye ya mika mata ta saka Hannu ta karba ya Fice yana Fadin”Key din duka Doors din Gidanan ne.in kin dawo ki Rika amfani Dashi Wajen Bude get din zuwa Kofar Cikin Falo..!
Da Toh ta Bisa kafin ta Bi bayansa Shi ya Rufe Kofar Falon Tana gani kana suka Taka,wajen Mota ita yace ta shiga Shi kuma ya isa ya Bude Get din Kana yazo ya shiga Motar sai da ya Fito kana ya kara Fitowa Daga Motan ya Kulle Get din da makullin Dake Hannunsa Tunda guda Biyu ne Daya ya bata ne a Hannunta Saboda ba Lokaci Daya Zasu Dinga Dawowa ba.
Sun Fara Tafiya ya Dauki Hanyar Buk Ba wanda ya kara mgana Wayarta Tana Cikin Jaka Munari nata Kiranta bataji ba suna gabda isa ya kalleta yana Fadin”Ina za”a samu Hijabai..?
Yafada Lokaci Daya Hankalinsa na Wajen Tuki Inteesar kai Tsaye tace”Kasuwa mana..!
Acikin Ransa ya maimata kasuwa Tabdijam to ina ma yasan kasuwan..?
Ganin bai kara cemata komai ba yasa itama bata kara mgana ba har suka Shigo Cikin makaranta Har Kofar Department dinsu ya kawota Ta kallesa Tana Fadin”Daman kasan Department din mu Ya Imu..?
Bai kalleta ba yace”kina so na makara ne..!
Da Sauri ta Bude Motar tana Fadin”Allah ya Kiyaye ya bada Sa”a..!
A saman lebe ya amsa da Ameen yana Fadin”Good luck..!
Ta Kada mai kai Har zata Rufomai Motar ta Tuna da Sauri ta Dawo Ta Zauna Tana Fadin”Ya Imu plz in mun gama Exam din yau nabi Munari naje Gidan Abba..?kaga duk yau baki zasu koma muyi sallama..!
Kallonta yake yi kawai bai ce komai ba Ganin haka yasa ta marairaice Tana Fadin”Plz Ya imu don”t say No..Please..!
Tafada Cikin Shagwabarta Baisan Sadda yace”Ok..!
Da Sauri ta Yada kanta Saman kafadansa Cikin Murna Tana Fadin”Tanque..So much..In ka Tashi Daga Wajen aiki sai ka Biyo mu koma Gidanmu ko..!
Kamar wani Gaula haka ya gyada mata kai Hannunsa Guda Dayan Dake saman Cinyarsa ta kama ta Sumbata Tana Fadin”Ya Imu na..See u later..!
Tafada Lokaci Daya tana Ficewa Daga Motar ta Rufemai ta Dago Tana Dagamai Hannu Baki Sake yake kallonta Gabadaya ta gama Sakamai kasala Dakyar ya Daga mata Hannu Lokaci Daya ya Tada Motar yayi kwana ya Fice Daga Wajen.
Sai da ya Dauki Hanyar Bankinsu ne ya Tuna bai bata kudin Mota ba..?kansa ya shafa yana Fadin”Su Imran miji manya..?miji ya bar Matarsa ba kudin Mota..!
Yafada yana Dariya to me ya sani na Daukan Nauyi shifa Nauyinsa kansa ba Duka yake Dauka ba Har yakai Cikon Bankinsu yana Dariyan kansa .
Intee kuma Tana waigen Neman Munari bata ganta ba ta karisa Cikin Department dinsu ta Fara gaisawa da Course mate dinsu Da suke ta mata Fatan Alheri Wayarta Take Kokarin Cirowa taji an Riketa ta baya tana Juyawa Taga Munari suka Saka Ihu atare suka Rumgume juna.
Kafin Munari taja Hannunta su samu Waje su zauna Tunda da Sauran Lokaci..
Nan fa Hira ta Tsinke Munari sai Tsiya Take mata tana kallonta Tana Fadin”Uhm..Amarsu ta angonta..ai na ganku..Aure mai Daraja wai yau Ya Imu ne da kawoki makaranta..!
Duka Inteesar ta Dagaamata suna Dariya Munari na Cemata ta Kira wayarta tace bata gani ba yana Jaka Munari sai Faman kallon Inteesar Take Tana Dariya Lokaci Daya Tace”Allah kadai yasan irin Romin amarcin da Ya Imu ya kwasa yau ya kawoki makaranta..Muma mun kusa shiga wannan karnin domin Khalil yace yana komawa zai gabatar da mganarmu..!
Inteesar na Dariya tace”Munari ana son Aure..Wai daman yace yana sonki ne..?kun dace fa..!
Tafada Bayan ta boyema Munari Wani abu bai Faru Tsakaninta da Imu ba.
Munari tace”lalle Tun yaushe…Sagir ma ya kafa Gwannatinsa Wajen Hafsah..!
Inteesar ta Zaro ido Tana Fadin”Ki bari don Allah..!
Munari tace”Ki zauna mima mun kusa Shiga Daga Ciki yarinya..!
Dariya suka saka Inteesar ta nuna jin Dadinta sosai aman take Fadama Munari in sun gama jarabawar yau Tare zasu tafi gida ya Imu ya barta Munari tace aiko kin ji Dadi kya yi Sallama da yan”uwa.
Tsaida Hiran sukayi Suka Fara Bitan Jarabawar da zasu yau duk da basu da Mtsala suna Karatin Jarabawa tun Lokacinta batayi ba Karfe 8am na Safe Daidai suka Shiga Paper 1 sai 11am suka Fito basu Zauna wani hira ba suka koma Wacce zasu shiga karfe 12am na Rana Har zuwa Lokacin.
Karfe 2pm na Rana suka Fito Shikenan sai kuma Gobe Suke da Guda Daya Daganan Inteesar da Munari suka samu adaidaita zuwa Gidan Inteesar sai Murna take kamar Wacce ta Shekara Kamar ba Jiya bane,Tabar gidan.
Koda suka isa Ya Basheer da Anty Hauwa da Anty Uwani da Maman Nasara da ita kanta Nasara sun kusa isa kaduna Harda Umaima Data Bisu Zata kwana anan Kaduna Ya Basheer zai siyan mata Tiket Tabi Jirgin kasa zuwa Abuja.
Inteesar bataji Dadi ba Domin ai tasan Daman bazai Tsaya ba Ya Basheer baya son Tafiyar Dare,Inna Maimunatu ma Ta mika Hanya ita dasu Zainab,Inna Bintalo ma ta wuce ita sai ta Biya wajen Daada Dukku.
Sa”id ne kadai ya Rage basu Tafi ba sai Sadam su yan Gida ne.
Kowa mamaki Dayaga Inteesar Munari ce ke azarbabin cewa Ya Imu yace ta Biyo ta nan in ya baro Wajen aiki zai Biyo ya Dauketa Shiyasa Abba yayi Shuru
Sai Gabda La”asar su Sa”id suka Tafi da Hafsah bayan sun gama Sallama da su Munari da suka Hada kai suna ta ma Inteesar Tsiya Harda Tasleem da itana Sallar La”asar kadai sukayi Ita tatafi Gida,Bayan La”asar kuma Ya Sadam da Tawagar Matarsa da ya”yansa suka Wuce gida,Gida ya Rage Daga Anty Safiya sai Abba Dashi ma bai jima da dawowa Daga Office ba.
Ya Yusuf bai je aiki ba Ranar yana Gida Sai da suka ci Abinci suka koshi kana Inteesar ta Tambayi Abba zuwa Gidan Mama ta kwaso sauran kayanta ya barta Munari ta Rakata Mama Taji Dadi Itama Gajiyan Biki bai Saketa ba Ta kara yima Inteesar Nasiha sosai kafin ta Dauki Sauran kayanta Saura kuma Tace Mama ta bada su kawai basu wani jima ba Saboda Abba yace Kada su zauna suka Dawo gida.
Gyaran Gidan suka Taya Anty Safiya Kafin su Shiga Kitchen suka Dora Girki,Farar shinkafa da Miya Sukayi da Nama Sai mangariba suka gama bayan sun Jera komai Saman Dining kowa yaje yin Sallah kafin su Fito su Abba suka shigo Harda Imran Daya Dawo da Sagir a masallaci suka Hadu Nishadi yake ji kamar ya Shekara baya Gidan..
Ranar Gabadaya suka Hadu Saman Dining Harda Imran da Sagir sukaci Abinci Cikin Farinciki,Bayan sun gama Abba bai yi kasa a gwiwa ba ga kara Yi Musu Nasiha sosai mai Shiga Jiki basu sukabar Gidan ba sai Wajen 9pm bayan Hankaluna sun kwanta Baki sun koma Gidajensu Lafiya..
Suna komawa Gida sun gaji sai Barci Kowa ya Nemi makwancinsa.