Wani mutum ya kashe N5.6m don ya koma kare

Mutumin dan asalin kasar Japan ne kuma ya je har Tokyo don ya mayar da kansa kare da taimakon masu hada kayan.

An kai masa kayan kare a watan da ya gabata inda ya dinga yada bidiyonsa sanye da kayan karen ya na rawar wakar karnuka.
Bidiyon nasa sun nuna yadda ya dinga juyi a kasa kuma ya na amsa umarni tamkar kare.
A bidiyonsa na farko ya bayyana cewa:
“Na zama collie ne saboda ina son komawa dabba. Amma yanz ina ta tunanin yada bidiyona”, a cewarsa.
Kamar yadda labarun Japanese su ka nuna, ya kashe £12,500 inda ya siya kayan karnukan daga Zeppet wanda ya ke shirya kayan dabbobi don fina-finai.
Bidiyoyin nasa sun janyo surutai daga mutane da dama.
Yayin da wasu su ka dinga yaba masa, wasu kuma sun ga wautarsa.
“Kalli wata sakarar hanyar kashe kudi! Amma ya yi kamar karen gaske, kamar kyakkyawan kare. Ina gaisuwa,” kamar yadda wani ya yi tsokaci.
“Wannan ai wauta ce,” inji wani.
Asali LabarunHausa
[ad_2]