GOJE 11 and 12
Gabadaya sai suka rasa inda maganarta ta dosa, ta mike tsaye tana gyara lifayar dake nade a jikinta, sunkuyawa tayi da fadin.” A tashi lafiya.” Bakinsa ne ya mutu kawai ya bisu da kallo a lokacin da suka kama hanyar fita, Ya girgiza kai yana jimanta al’amarin wato dai har yanzu Safa taki zama cikkakiyar mai ‘yanci a gidan auranta, tana biyewa Aysha suna zuwa har gabanshi suna masa rashin kunya, to babu shakka zai sa kafar wando guda dasu.
Washe garin ranar da ciwon ciki ya tashi, yaransa suka kewayeshi suna masa sannu, yana kwance idanuwansa a lumshe yake amsawa, daya daga cikin rayan nashi, yace.” Allah ya taimaki Mai dawa! ga magani na had’a maka.” A hankali ya bude idonshi ya dora kan ‘kwaryar maganin dake hannunsa, ya mutse fuska yayi ya mayar da idonsa ya rufe da fadin.” Alba ka ajiye wannan maganin ka matsa min lemon tsami guda shida.”
Da sauri yace.” An gama ranka ya dade.
Ya dan sauke numfashi tare da sake rintse idonsa shi kadai yasan irin ciwon da marar shi ke masa.
Alba ya k’araso gurin cike da bin umarni yace.” Allah yaja zamaninka ga abinda ka bukata.
Ba tare da ya bude ido ba yace.” Nagode Alba kuna iya tafiya Allah ya bada sa’a.” Suka amsa da ameen kafin su bar gurin sai da sukayi yi masa kirari kamar yanda suka saba.
Kimanin minti biyar da tafiyarsu ya tashi da kyar, ya jima yana yamutse-yamutse kafin ya dauki matsatstsan lemon tsamin ya shanye tas, ya ajiye ya koma ya kwanta, yana danne saman cikinsa.
Tayi mamaki da gari ya waye be zo ya dubata kamar koda yaushe ba, kawai tashi tayi a bacci ta samu ruwa cikin kwarya da asuwaki sai manya manya ayaba da mangwaro a gabanta.
Ta wanke bakinta da fuskarta, dama can ibadah bata dameta ba domin data dameta da duk yanda za tayi sai tayi ta gabatar da sallolin da suke kanta.
Yunwar da takeji bata tsammanin Ayaba da mangwaro zasu kawar da ita, taja tsaki tana harare-harare a gurin da babu motsin kowa sai ikon Allah.
Jikinta ta duba tayi fututu! fatar jikinta duk ta bushe tayi datti! ta dubi qunar da duk ta bushe tana mata kaikayi, ruwan hawaye ta goge tana tunanin jin dadi da irin rayuwar da take ciki amma lokaci kankanki rayuwa ta juya mata baya.
Kullum idan za ta kirashi da ‘Barawo zai kalubanceta kan cewa shi ba ‘Barawo! bane to idan ba haka ba waye silar zuwanta wannan kasurgumin dajin.”?
Ta girgiza kai cikin qunar zuciya ta kudiri aniyar irin rashin mutuncin da za tayi mata huce takaicinta.
Ayaban kadai ta iya ci ta dauki kwaryar ruwan ta shiga tsakanin bishiyu kayanta jikinta ta cire tas ta wanke jikinta, gurin wankan ta jike rigar data zame mata garkuwa, bata damu ba kawai tasa breziyya ta mayar da wandonta ta fito a haka, taja ta tsaya tana dube-dube a gurin.
Babu motsin mutum sai kukan tsintsaye da alama yau ma sun fita sun barta a dajin ita kad’ai.
Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke taja tsumman zanin ta dan daure tsakain cinyoyinta kafin ta nemi saman wani kuttuturun icce ta zauna tana tunanin halin da iyayenta ke ciki na rashinta, ta san mahaifinta sai yafi kowa shiga tashin hankali rashinta a kusa dashi.
Ya kai minti arba’in cikin halin ni ‘yasu kafin Allah ya sassauta masa, ya mike zaune da kyar! duk da halin da yake ciki hankalinsa na kanta burinshi ya tashi yaje ya duba halin da take ciki.
Ya mike babu kuzari a jikinsa, kai tsaye gurin da take ya nufa……………….Rintse idonsa yayi da karfi yana Auziya a fili sakamakon ganin da yayi mata ita ba tsirara ba ita mai tufafi domin breziyar dake jikinta bata hanashi ganin kamai ba……..”Subahanallah !
Ya jima a tsaye a gurun yana kiran sunan Allah! kafin yayi namijin kokarin bude idonsa yayi ya’ki da shaid’an da kuma zuciyarsa ya durfafeta babu alamun wasa a tare dashi…………