GOJE

GOJE 25 and 26

FREE PEGE
25&26
“Kada ku yarda ku bari ya kubce daga hannunku, mugu! ne macuci! ya jima yana ta’addanci a k’asa! kuyi masa hukunci mai tsauri! domun da bakinsa yake fadin cewa yafi karfin hukuma! yau tsayin kwana shida kenan daya raba ni da iyayena yayi kidnapping dina domin samun makudan kudi daga gurin mahaifina, ” Sunana ZINATU ni ‘yar asalin jahar kano ce mahaifina kuma shine sarki dake kan kujerar mulki a jahar.” Bilhaki da gaskiya take maganar.

Gabad’aya hankalinsu ya koma kanta a lokacin da take wannan maganar, da yawa daga cikinsu ba su lura da ita ba, maganarta ce ta janyo hankalinsu kanta. ganinta a firgice babu sutturar arziki yasa suka gazgata maganarta, babban cikinsu ya kwantar mata da hankali da cewa komai yazo karshe kuma sunyi alkawarin kaita gaban iyayenta idan sun gama gudanar da binkice.

Beyi mamaki da jin furucinta akansa ba, ita kad’ai ce zata bada cikakkiyar sheda a kansa, amma ba tayi hakan ba, to ba zai tsananta ba, ba kuma zaiyi jayayya da hukuma ba, zai bi doka da odar amma ya san ita gaskiya d’aya ce kuma a kanta yake babu gudu babu ja da baya babu shakka! Allah za bayyana mai gaskiya.

Da kansa ya haura ya shiga motar ya zauna, sojoji uku suka zauna hagu da damanshi, ya kalli na hannun damansa cikin nutsuwa yace.” Akwai sauran yarana da suke n…….. ya katseshi ta hanyar buga masa tsawa da fadin.

“Rufe mana baki ko kai zaka nuna mana aikinmu.”? Kansa ya girgiza, yace.” To kabi umarnin mu domin shine samun zaman lafiyarka.”

Be sake cewa komai ba ya kauda kansa gefe yana hangensu suna ta binkice a gurin………..Can ya hango sun taso sauran yaransa a gaba! suna dukansu! bai dauke idonsa ba har sai da suka karaso gurin, gabadaya sun galabaita domin wasu harda rauni a jikinsu bayan wa’inda suka kone sakamakon bomb din daya tashi, ya tausaya musu sosai, domin ya san shine mujaza! domin da yawa daga cikinsu ba’a son ransu hakan ta faru ba.

Suka dinga turasu cikin motar suna dukansu da wata murtukekiyar bulala irin ta karfe!

To duk iya binkincensu a gurin Allah bai nuna musu dungulmin hannun Uban daba! da ‘kasa ta turbudeshi a gurin ba, Yana kallonsu suka ‘karaci dube-dubensu suka shishshiga mota da niyyar fita daga dajin.

‘Bude baki yayi da niyyar magana kawai ya hangota tare da wani soja yana kokarin bude mata gaban mota domun shiga……..Yaji wani irin ciwo a cikin ranshi! bakinsa ne yayi nauyi ya gaza furta maganar dake cikin cikinsa har suka fita daga cikin dajin bai dago kanshi ba! wani irin kuttun bakin ciki ya tsaya masa a wuya, tunda yake bai ta’ba ganin butulu irinta ba.

Da yayi motsi zasu saita shi da bindiga! da fadin.” Ya kiyaye idan kuma yayi wani yunk’uri na gudu to zasu harbe shi! murmushi kawai yake musu, wanda hakan ke ‘kara tunzura musu zuciya.

Labari kaf ya cika garin Katsina da kewayenta cewa A yau 11/3/2007 jami’an tsaro sunyi nasarar kama babban dan ta’addah nan wato Mashekin daji! wanda ya addabi k’asa da jama’ar dake cikinta.

Headquarter ‘yan sandan kuwa cike take da ‘yan jarida da jama’ar gari masu ganin kwal uwar daka.

Koda motocin jami’an tsaron suka shiga headquarter ‘yan sandan sai gurin ya hargitse da hayaniya kowa burinsa yayi ido hudu dashi, Mussaman ‘yan jarida masu daukar rahoto.

Sai da suka rufe masa fuska sannan suka fito dashi a dadd’aure! Suka rirrikeshi da kyar yake cire k’afa sakamakon sark’ar da tayi masa dabaibayi!

Duk da hakan sai da yan jaridan suka dinga daukar hotonsa tun daga sama har kasan Kafafunsa, da yawa daga cikin ‘yan jaridar da jama’ar dake gurin sunyi mamakin ganinsa ingarmar namiji a labari dai sun san cewa ba haka kammaninsa yake ba gajere ne mara fasali ya akayi kuma a zahiri basu ga haka ba.

Har sai da aka shiga dashi ofis din Asp sannan kowa ya watse, jama’ar gari suka tafi da zancan a bakunansu, su kuma ‘yan jarida suka fara gudanar da ayyukansu.


Cikin tsananin tashin hankali Saude matar Alba ta shiga gidan tana kuka hannunta rike da jarida.

Uwale ta tare ta tana tambayarta abinda ke faruwa.

Jaridar ta nuna mata da fadin.” Uwale kin san abinda yake faruwa kuwa.”? ta kar’bi jaridar tana dubawa tace.” Saude kin san ban iya karatu ba me yake faruwa.”

Tace.”Ki duba hoton jiki mana Mijina Alba ake tuhumarsu da ta’addanci.”

Gabanta ya fadi! tace.” Ta’addanci kuma Saude! su da suka tafi farauta mai ya hadasu da ta’addanci inace gobe zasu dawo.”

Saude na kuka tace.” Uwale kisa kunne da kyau ki saurari jawabin da zanyi miki.”

Jiki a sanyaye tace.” Ina sauraranki.”

“Jami’an tsaro ne suka kama UMARU wato jikanki dashi da yaransa saboda zargin da ake musu na ta’addanci, a yanda na karanta rahoton cewa wai ana tunanin shi UMARU shine wannan d’an ta’addan da ya addabi kasa! yanzu haka dai gabad’ayansu suna hannun hukuma! jama’a da yawa sunyi imani da cewa hukuncin kisa za’ayi musu.”

Hankalinta ya tashi sosai sai ta fashe! da kuka ta tsirawa hotonsa ido duk da fuskarsa a rufe take hakan be hana ta ganeshi ba, ta tsirawa kafafunsa ido tana wani irin kuka tace.” UMARU wannan ranar nake gudu a gareka, itace rana mafi muni da ba zan ta’ba mantawa da ita ba, ashe tsautsayi ne ya sanya ka tsunduma kanka wannan harkar, ni na san halinka UMARU kuma zan bada sheda a kanka, ka taka sawun ‘barawo insha Allah sai Allah ya wanke ka daga zargin da ake maka.” Kuka sosai takeyi hawayenta duk ya jika takardar dake hannunta.

Hamra’u ta shigo gidan cikin kuka na fitar hayyaci! tana zuwa ta rugumeta da fadin.”Uwale ya za muyi da wannan kaddara hukuma ta kama Yayana da laifin ta’addanci! bayan bashi da laifi Yayana bashi da mugunta baya cin hakkin wani burinsa kullum ya za’ayi k’asa ta samu cigaba, amma ya taka sawun barawo jami’an tsaro sun kamashi dumu-dumu a cikin sansanin da Uban daba! yake zaune da jama’arsa, Uwale ya za muyi bamu da kudi bamu da ikon da zamu tunkari hukuma! domin kalubantar zargin da sukeyi akan wanda bai ji bai gani ba.”

Tace.”Hamrau bamu da komai wanda zamu tunkari hukuma dashi, amma muna da Allah shi kadai zai ne zai mana jagoranci Allah ba azzalimin sarki bane yana tare da masu gaskiya insha Allah cikin hikimarsa zai bayyana mai gaskiya.”

Asp Musa Baharu shine shugaban ‘yan sandan jahar, kuma duk wani jami’in tsaro a karkashinsa yake, mutumin yana da hankali da nutsuwa gami da sanin makamar aiki, koda aka shigar masa dashi ofis din kallo daya yayi masa ya tabbatar da cewa bashi suke da bukata ba, amma be nuna hakan a zahiri ba, sai kawai ya bawa wa’inda suka shigo dashi umarnin fita, ya rage su biyu kacal a ofis din.

Shi baya ganin komai saboda har yanzu fuskarsa a daure take, amma shi Asp din yana kallon duk wani motsinsa.

K’ira ne ya shigo wayarsa, daga gidan gwamnati , cikin cikin girmawa ya daga da fadin.” Ranka ya dade barka da wannan lokaci.”

Mai girma governor yace.” Barka dai Asp barkanmu da samun nasara! wannan ranar ba zamu ta’ba mancewa da ita ba, yana kuma da kyau ayi rubutu na mussaman domin ajiyewa a kudin tarihi.”

Asp ya d’anyi murmushi da fadin.” Hakane ranka ya dade, labarin samun nasara ya cika gari da sauran garuruwa jama’a da yawa sun kirayi waya suna yi mana murna! amma ban san me yasa ni nake shakku! akan hakan ba.”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button