GOJE 25 and 26

Mai girma governor yace.” Asp wannan wace irin magana ce? da farko kafin isowar rudunar da muka tura kaine ka kirayi wayata kake sheda min cewa an samu nasara ya za’ayi kuma yanzu kace na shakku akan hakan.”
Gilashin dake idonsa ya cire ya ajiye saman tevur din dake gabansa, ido! ya tsira masa yana sake nazartarsa, yace.” Ranka ya dad’e ni da kai da sauran jama’ar gari bamu ta’ba ganin Uban daba! a zahiri ba, sai dai muna hasashe akansa cewa shi din wani irin mutum ne mara fasali sanin hakan ma ya samo asali ne daga bakin d’aya daga cikin yaransa da Allah ya bamu ikon kamawa a shekarun baya, shine yake sheda mana kammaninsa, a lokacin da al’amarin ya faru, banyi ‘kasa a gwiwa ba na samu yaron daya haddace zane ya zana min kammaninsa domin samun sauki gurin binkice a kansa, amma abin mamaki! a yanzu wanda yake gabana a yanzu kuma muke hasashen cewa shine wanda muke nema ruwa a jallo kammaninsa yasha bambam! da wannan hoton zanen da nasa aka zana min a shekarun baya.”
Mai girma governor yace.” Asp ya akayi hakan ta faru? kana so ka sheda min cewa bashi bane.”?
Ya mi’ke tsaye da wayar a kunnasa, kujerar ya janye ya fito daga tsakankanin kai tsaye inda yake zaune ya nufa!…….Yana wayar yana kokarin kwance masa fuska dake d’aure.
Tsaf ya warware d”aurin fuskar, idanuwansu suka hadu guri guda, kujera yaja ya zauna suna fecing din juna.
Ya cigaba da cewa.” Gani gashi a halin yanzu kuma yanzu zan dauki hotonsa na turo maka dashi domin ka sheda maganata, amma duk wani binkice zanyi a kansa domin samun tartibiyar magana.”
Mai girma governor ya sauke ajiyar zuciya da fadin.” Okey to babu damuwa ina tsumayinka.” sallama sukayi kafin ya kashe wayar, ya tsira masa ido! shima nasa idon ya tsira masa suka dinga kallon kallo suna nazarta juna, shi Asp din shine ya fara janye idonsa daga kanshi, ya jima kanshi a kasa kafin ya dago ya sake mai da idonsa gareshi yace.” Inaso naji cikakken sunanka gami da jin asalin tarihin rayuwarka.”?