GOJE 29 and 30

Kusan a tare suka sauke zuciya da jin furucinsa suka shiga godewa Allah da abinda yayi musu.
Har yamma suna tare ya saki jikinsa sosai yana basu labarin irin gwagwarmar suka sha a dajin! tace.”Kaga Umaru shiyasa kwata-kwata hankalina bai kwanta da wannan harkar ba mahaifinka har ya mutu da abun a cikin ransa saboda haka idan Allah yasa ka kubta to dole ka ajiye wannan sana’ar ka nemi wata domin hakan shine samun nutsuwarmu baki daya.
Domin ya kwantar mata da hankali sai ya amsa mata akan abinda take so, taji dadin hakan kuwa tay tai masa addua da fatan samun nasara akan dukkan abinda ya sanya a gaba.
Ta jima a toilet din tana durje jikinta da sabulai iri-iri kafin ta dauro towel ta fito. idonta ya sauka kan tufafi wanda aka ajiye mata su kan gado komai sabo underwears sai riga da siket na wani material mai taushi, goge jikinta tayi kafin ta zauna gaban mudubi tana kokarin duba man da zata shafa a jikinta, tsaki taja tana hararar tarin kayan kwalliyan dake dressing mirror din duk ciki babu kalar man da yayi mata ballantana ta shafa a jikinta……..wani lotoin ta dauka tana jujjuyashi a hannunta sai ya mutse fuska.
Ta turo kofar dakin ta shigo da sallama a bakinta kallo guda kayi mata zaka fahimci cewa tana daga cikin jerin mutane masu sauki kai da daukar rayuwa a sannu, tana da fara’a sosai domin da wuya kaga bacin ranta sai in tura ta kai bango.
Fuskarta yalwace da fara’a ta ‘karasa shiga dakin da fadin.” Yawwa kin fito ko ga kaya nan na ajiye miki na san za suyi miki dadin sawa.”
Shuru tayi bata tanka ba. Ta kalleta da fadin.” Ko dai na sauya miki wasu wannan ba suyi miki ba.”?
Tsaki taja da fadin.” Don Allah kin cikani da surutu haka na duba na gani okey nagode.”
Ranta ya ‘baci da abinda tayi mata amma sai ta danne ko alama bata nuna a fuska ba tace.” Okey to shikkenan idan kin shirya sai ki fito muci abinci .”
Ta’be bakinta tayi ba tace komai ba ta cigaba da jujjuya abinda ke hannunta.
Juyawa tayi da niyyar fita daga dakin. sai ta dakatar da ita, ta tsaya tana sauraranta.
A yatsine tace.” Wannan tarkacen mayukan shafawar taki ba zan iya shafawa ko daya a jikina ba domin ni ba irinsu nake shafawa ba.
Cike da mamaki take kallonta tana mamakin furucinta, tarkace!!! duk man da take shafawa babu na kasa da dubu biyar sai sama amma shine har take magana cewa ita tafi karfin ta shafa a jikinta.
Jinjina al’amarin tayi kafin tayi ‘yar dariya da fadin.” Lallai ‘kawata kina ji da gayu amma idan ba haka ba meye laifin mayuka na ko wannan na hannunki kika shafa ya isheki.” Cike da wasa ta karashe maganar……….Sai ta fusata! ta mike tsaye tare da buga mata tsawa! da fadin.” Ke kin san wacece ni kuwa? da har kike min wannan banzar maganar.”? Ta’be bakinta tayi tace.” Ina zan sani hajiya ni dai Daddy ya kira ni a waya ya sheda min cewa zanyi b’akuwa shiyasa nake karramaki bahaushe yace.” bakon ka Annabin ka.”
Dogon tsaki! taja kafin ta koma ta zauna……….Ita kuma da sauri ta bude kofar dakin ta fita tana mamakin al’amarin.
Zama tayi tare da sauke ajiyar zuciya, ta kalleta da fadin.” Ya akayi ne? bata gama shiryawa bane.”?
Baki ta dan ta’be kafin tayi ‘yar dariya da fadin.” Na isketa ta fito daga wanka tana nazari man da zata shafa.”
Cike da mamaki tace.” Kamar yaya nazari duk cikin mayukan shafawar taki babu wanda yayi mata.”?
Tace.”Hakan take nufi.”
Tana kokarin magana motsin fitowarta ya katseta duk sai suka juya suna kallonta tayi kyau sosai a cikin material din sai dai siket din ya matseta dalili tana da kwankwaso mai fadi da cika sakamakon mai kayan da nata bai kai hakan ba.
Da murmushi a fuskar matar gidan tace.” Kin fito.”? “Umm.” tace kawai ta nemi kujera ta zauna sai wani basarwa take.
Ta kalleta da fadin.” Nabila mai yasa ki ka bata wannan kayan kamar sun matseta ki tashi ki dauko mata wasu.”
Tace.”Mommy kin san duk kayana riga da siket ne kuma bai zama dole suyi mata yanda takeso ba tunda ta fini kiba.”
Ta kalleta da fadin.” Zinatu baki takura ba dai ko.”?
Girgiza kai tayi da fadin.” Kada ki damu hakan yayi min daidai domin yawancin kayana haka suke.” Tace.” To masha Allah ku tashi muje muci abinci.” kusan a tare suka mike kai tsaye gurin cin abincin suka nufa.
To duk wasu bayanai da ya kamata ace gwamnati ta san dasu Asp ya harhad’a komai ya turawa maigirma governor domin ya saurara dashi da wa’inda da ke da alhakin hakan, sai dai ya sheda masa cewa ranar asabar shi da wanda ake zargi da aikata ta’addancin zasu shiga sansanin domin binkice akan sassan sannun da zai tabbatar da gaskiyar magana. maigirma governor yayi na’am da maganar ya kuma bada goyon baya akan tafiyar.
*’Yan jarida mane ma labarai suka samu abun yayatawa a gari! gidajen redio da television gami da jaridu labarin abinda suke nunawa kenan cewa ashe wanda ake zargi da *UBAN DABA!* bashi da ala’ka da zargin da ake masa asali ma shine mutum na farko wanda ya fara karya alkadarin d’an ta’addan da ya addabi kasa da al’ummar dake cikinta, domin tabbatar da gaskiyar magana kakakin rundunar ‘yan sanda wato Asp Musa Baharu zai jagoranci shi wanda ake zargi domin gudanar da binkicen sassan hannun wanda ake nema ruwa a jallo………..Sannan kakakin rundunar ‘yan sandan ya shedawa mane ma labarai cewa yanzu haka akwai d’iyar Sarkin Kano mai suna Zinatu wanda ake zargin cewa wasu ‘bata gari sunyi kidnapping d’inta domin samun kudi daga gurin mahaifinta, amma ha’kan su bai cimma ruwa ba sakamakon zuwan shi wanda ake zargi da ta’addanci mai suna UMARU wanda jama’a suka fi sanin sa da GOJE! shine wanda ya zama garkuwa a gareta har yayi nasarar tallafar rayuwarta bayan ya samu nasara akan wa’inda sukayi garkuwa da ita…………Wannan shine cikakken rahoton da ya cika garin Katsina dama kewayanta.
Duk wanda ya danganci masarautar yana cikin farin ciki sakamakon samun cikkaken labarin bayyanuwar ta…………Fada ta cika da jama’a masu zuwa taya murna da fatan alkairi maimarta da ‘yan uwansa fuskokinsu tamkar gonar auduga saboda tsantsar farin cikin da suke ciki a ranar yini cir masarautar babu masaka tsinke mata da maza wannan ya fita wannan ya shiga.
Gimbiya Aysha da ‘yar uwata tare da ‘ya’yansu su ka kasance cikin farin ciki mara misaltuwa, Maijidda ma tayi nata murnar daidai gwargwado amma ta ciki na ciki domin kasa zama tayi cikin ‘yan uwanta ta nufi b’angaranta jikinta duk a sanyaye yanzu babbar damuwarta kada asiri ya tonu sunanta ya fito shine abinda yafi tsaya mata a rai….
Hello my fans A hanzarta biyan kudi domin yanzu zamu shiga cikin labarin akwai kuraa!! 馃槃 kada ki sake ayi bbu ke ‘yar uwata kada ganin k’yashi ya hanaki biya ki zauna jiran na sata wallahi tallahi! hakkin wani masifa ne!! mai girman gaske!! yi kokarin gudun haram! komai kankantarta!!!