GOJE 5 and 6

Uwale, kayan dillacinta ta dauko ta nada gammo ta dora aka, tana gyara yafan mayafi take fadin.”Hamra’u ni zan fita dama a irin wannan lokacin nake samu na nemi halalina idan kin gama gyara min gidan ga kwado ( dan mukulli) akan taga ki kulle gidan ki bawa Tasallah ta ajiye min.”
Tace.”Uwale inace Yayana ya hanaki yawon dillaci nan kuma kin san Babana ma baya so me kike bukata ne a duniyar nan.”
Tsaki taja da fadin.” Sai kiyi kuma kinga tafiya ni babu wanda zai hanani neman kudi.” tana gama maganarta tasa kai ta fita daga gidan.
Hamra’u girgiza kanta kawai tayi idan da sabo ta saba da hakan , a nutse ta mike ta fara ayyukan dake gabanta….
WAIWAYE
K’allo d’aya nayi masa na fahimci wanene a gabana, ko da yake koda zanyi shekara d’ari ba tare da na sanyashi a idona ba to ba zan mance kammaninsa ba, Sadauki Omar kenan Sarkin dake kan karagar mulki a jahar Kano Adalin sarki wanda al’ummarsa ke jin dadin mulkinsa.
Yana nan a yanda kuka san shi tsayayye! kuma jarumin namiji! kamanninsa suna nan sai dai alamun girma da ya baibayeshi amma a tsaye yake da jarumta babu abunda ya samu nakasu a cikin halayensa da d’abi’unsa.
Yana tsaye a tsakiyar babban falonshi hannuwansa goye a banyanshi yana kai kawo a gurin, kallo daya kayi masa zaka fahimci yana cikin damuwa.
Cikin nutsuwa da kamala tayi sallama be juyo ba ballantana ya amsa sallamarta,
kai tsaye inda yake ta nufa, sai na bita da kallo, ina hasashen a inda na san fuskarta, Gimbiya Aysha ce fa zuciya tayi saurin tuna min ita
Cike da dumbun mamaki nake kallonta tana sanye cikin laffaya milk color da adon zaiba kafarta sanye da takalmi rufaffe irin na sarauta, ban hango wata tawaya a tare da ita ba domin kuwa jikinta ya nuna alamun hutu da jin dadi sai dai alamun shekaru sun tura hakan ma sai ka ‘kura ido a kanta sannan zaka fahimci cewa ta kwana biyu a duniya.
Hannunta ta d’ora kan kafadarsa, a nutse ta kira sunanshi “Jarumi.” be juyo ba ballantana ya kalleta, sai ta dora kanta kan kafad’arsa, hawayen da take boyewa suka kufce, wai shin ya za suyi da wannan ibtila’in da yake kokarin ruguza musu farin cikin da suke ciki na tsayin shekaru masu yawa…………….
Ga wanda bai samu damar karanta Sadauki Omar ba, zai tura 1k domin samun damar karanta littafi biyu tare da Goje! Sadauki Omar return