NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 1) 11&12

????????11
     ………Ba manager kawaiba, hatta da sauran jama’ar dake gidan jaridar saida suka tsorata da tsawar Galadima, su Muftahu ma tsorone ya kamasu, sunsan irin wannan matsanancin fushin

gareshi babbar matsala ce ga lafiyarsa.

     Aikam sai gashi ya dafe kansa, saboda yay wani mugun sara masa, da sauri Harun yajawo kujera ya kamashi ya zaunar, har yanzu dafe yake da kan nasa.
    Muftahu ya furzar da hucin, matsalar da suke gudun ta d’akko hanyar faruwa kenan. kallon manaja dake durk’ushe har yanzun yayi,
   yace “tashi ka zauna”.
     Mik’ewa manaja yayi jiki Na rawa yakoma saman kujera, Muftahu da Harun ma suka zazzauna.
      Cikin tsare gida Harun yace, “manager ka nutsu, kabamu had’inkai wajan fad’ar gaskiya, inba hakaba wlhy zakayi nadama ne, ba kaiba hatta da ahalinka saisunyi nadamar kasancewarka acikinsu”.
       Manaja yashare guntun kwallar dasuka taru masa a idanu, a nutse yafara fad’in “ai tunkan jaridar jiya tafita nake acikin nadama, nayi dana Sanin kasancewata ma’aikacin jaridar da aka ci zarafin d’an Wanda yay tushen kasan cewata a wannan matsayin danake, da ace remote d’in rayuwata a hannuna yake, dana tariyo bayana jiya bata shigo rayuwata ba, amma Na…..”
          Muftahu ya katseshi cikin d’aga masa hannu “kaga manager, ba rayuwarka mukazo saniba, munason ka fad’a mana waye yasaka wannan aikin? nawa suka biyaka kamusu shi?”.
         “wlhy tallahi yalla6ai basu biyani komaiba, kaga wacan jakar sune suka ajiye min ita, amma ko bud’eta banyiba. kuma babu wani ma’aikaci daya buga labarinan  agidan jaridar nan da hannunsa. sune da Kansu adaren jiya sukayi komai, bayan sun had’emu waje guda da bindugu, kuma sunzo nannane dukansu fuska arufe, wlhy ko fuskar mutum d’aya bamu ganiba, yanzu haka sun kwashe muhimman documents dake ma’aikatar nan sun tafi dasu. kuma sunsan da zuwan yalla6ai gurinnan yau, Dan komai sunyishine a tsare kamar yanda mukaji suna hira a tsakaninsu” manaja ya fashe da kuka, sannan yacigaba da fad’in “saboda sunsan zakuzo nan yau, sunje gidana tun adaren jiya, sun kwashemin iyali da mahaifiyata, yanzu haka suna wajensu, sun tabbatar min inhar wani magana yafito abakina abakin ran matata da yarana hud’u da mahaifiyata sai k’anwata. wlhy ina cikin masifa, yau anan Na kwana, nakasa fita waje saboda banason jin 6atancin da jama’a suka gani a wannan safiyar akan yalla6ai. Wlhy Na rantse muku bansan komaiba”.
          Tunda manaja yafara magana kowa yay tsit, Galadima bai d’agoba saida yaji manaja ya ambaci iyalansa Na wajen wad’anda suka aikata aika-aikar. Idonsa yakad’a yayi jazur, sosai manaja ya tsorata da idanun Galadima, haryana tunani a zuciyarsa anya Galadima shi kad’aine, bashida aljanu kuwa?.
            Komai Galadima bai ceba, ya tashi dafe dakai yafice daga office d’in, ma’aikatan wajen sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa, amma kallon kowa baiyiba yafice.
     Dogaransa suna ganinsa suka mik’e da Sauri, Mota suka bud’e masa yashiga, suma su Muftahu suka fito da hanzari.
...........
        Tun daga fitar innaro sai gidan yay tsit, kowa ya kama gabansa zuwa d’akinsa, a can suka cigaba da gulmace-gulmacensu suda bak’insu.
     Niko da Munubiya muka shiga raira sabon kuka, munubiya ta kamo hannuna ta rik’e anata.
     “Munaya dan girman ALLAH kibarni Na kar6i hukuncin laifina, nice Na aikata bakeba, miyasa zaki cema iyayenmu kece? kibari nafad’a musu gaskiya please ”.
       “A’a Munubiya, wannan laifin nawane, karki manta ta sanadina abinnan yafaru, da ace Fu’aad bai kaimu plaza d’innanba da hakan bata faruba wlhy, munubiya farincikina fansane agareki, har abada bazan iya juriyar ganinki cikin k’unciba, Dan Girman ALLAH koda da wasa kar wani agidannan yaji banice Na aikata abunnanba koda kuwa innarmu Ce, namiki alk’awarin zan jure duk wata fitina dazata taso, zankira Fu’aad yafito muyi aure, duk da naso ace rana d’aya aurenmu zai kasance, amma haka ALLAH ya k’addara mana”.
        rungume juna mukayi muka kuma fashewa da kuka, cikin shashshekar kuka Munubiya ke fad’in “mi mukaima Wanda ya k’ulla mana wannan sharrin? mi muka tare masa agidan duniyarnan Munaya?”.
       “ban saniba Munubiya, bansan waneneba? Amma nafi zargin gidan wannan jaridar, aganinsu sun sami babban labari, bara su buga suyi suna, Sun zaluncemu Munubiya, sun yad’a labarin abinda ba haka faruwarsa ta kasanceba, Galadima ko ta6aki baiyiba amma suka saka har yana kissing d’inki, wane irin zaluncine wannan? wlhy nima bai ta6a niba da mukayi karo a filin idi, amma ki duba hannunsa rik’e da nawa ajaridar, Munubiya banga laifin iyayenmu ba, kowanne mahaifa bazasu so ganin wannan mummunan abinba, kuma ko zamu kwana rantsuwa bakowa zai amince damu ba, INA tausayama innarmu, ada Yaya muka k’are ma a gidannan bare yanzu?, munubiya innarmu innarmu, banason innarmu tashiga mummunan hali akanmu, yazamuyi innarmu ta fahimcemu, koda ace kowa bai yarda damu ba inason innarmu fahimcemu munubiya…..”
       
       “Na fahimceku ‘ya’yana, tabbas nashiga tashin hankali da ganin hotonku a jarida,  kuma a yanayin da kowace uwa ba zataso ganin  ‘ya’yanta a wanna halinba, kuma ace bazata shiga fiyeda yanayin Dana fad’aba, sai dai ni ba abinda naganine yasakani cikin rud’ani irin haka ba harna yanke jiki na fad’i, cin zarafin innaro ne.
     ‘ya’yana nasan bazaku aikata koda makamancin hakanba, dan naji ajikina sharri akai muku…..”
      Da gudu suka sakko a gadon sukazo suka fad’a jikin innarsu suka cigaba da raira kuka harda ita kanta innar, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru.
     Duk suka nutsu suka mata bayanin komai, har Munaya ta d’akko wayar da Galadima ya barta da ita a filin idi ta nuna musu.
    Nanna INA ta kuma fahimtar akwai 6oyayyen al’amarin abinda basu saniba akan lamarin, kuma tafi zargin k’ullin Anma Galadima ne kawai, ‘ya’yanta k’addara Ce ta sakasu cikin sark’ak’iyar, itadai Addu’arta ALLAH ya fiddashi da ‘ya’yanta baki d’aya, saitaji yabata matuk’ar tausayima.
        Suna cikin haka saiga mama Rabi’a dasu Ayusher, nanma aka kuma zaman warware zance, mama Rabi’a da inna suka kuma fahimtar komai yanda yake.
    Nasiha suka Shiga yima ‘ya’yan Nasu mai ratsa jiki, sannan suka nuna musu illar biyema samari batareda wani dogon tunaniba, duk sai jikin su Munaya yayi sanyi, sun fahimci bin Fu’aad dasukayi plaza shine yazama babban kuskurensu.
     Sun nemi gafarar iyayen nasu akan hakan dasuka aikata, daganan suka Shiga tattauna maganar Auren munaya da Abba yakafe akan nanda sati biyu.
    Sun Yanke shawara akan akira Fu’aad, inhar da gaske yakeyi to saiya fito kawai.
     Akan wannan shawarrar suka zauna gaba d’aya.
★★.★★.★★.★★.★★
      Har suka Isa cikin masarautar Galadima baiko motsaba, yana tangad’i da layi yashige 6angarensa, daga Muftahu har Harun babu Wanda yayi yunk’urin binsa.
     Tunda yaje yazube saman 3seater bai sake sanin inda kansa yakeba saboda matsanancin ciwon kai dake damunsa, da k’yar ya iya gabatar da sallar magrib da isha’i a lokaci d’aya, a saman abin sallar ya kwanta rigingine dafe da goshi, yana kwance shiba mai barciba shiba ido biyuba.
    8:30pm dukkan mai ruwa da tsaki a meeting d’in ya hallara, hatta da sarki gaba d’aya, sai dai kuma babu Galadima babu dalilinsa har mama Fulani tafito.
        (Babbar magana ????) na fad’a a raina, saboda ganin tsantsar mulki da isa ajikin hamshak’iyar tsohuwa dazata iya kaiwa shekaru 77 a duniya, sai dai tsantsar hutu da gayu ya 6oye ziryan d’in tsufan nata, gata da k’aramin jiki kuma, daka ganta haka bafulatanar asali.
      Tunda ta fito kowa a falon yamik’e tsaye saboda girmamawa a gareta, amma banda sarki, ya risinar da kansane kawai alamun girmamawa ga mahaifiyar tasa.
     Saman kujera 2seater ta zauna cikeda izzar mulki, (saikace itace sarkin????????)  sai da ta gamaima kowa dake falon kallon tsaf sannan takuma kamewa, cikeda k’asaita tace, “Shi yana ina? Ko raini. Hankalin nasane ya hanashi zuwa?”.
     Kowa dake wajen yasan galadima take nufi, babu wanda ya iya cewa komai sai wani matashin saurayi dazasu iya zama sa’annin juna da galadima, ya gyara zamansa yana wani 6ata rai shima, “Granny kinsan halinsa aii, ba ganin kowa da gashi yakeba a masarautar nan mtsoww”.
       Mama Fulani ta turo hanci ga bada, cikeda fushi ta bada umarnin a kira mata  jakadiya.
      babu dad’ewa saiga jakadiya tashigo, k’asa ta zube tamkar zatayi mata sujuda tafara fad’in “ALLAH yaja zamaninki ranki ya dad’e, kinga taki kinga tawasu, fatanmu kiga tawasun wasuma, Sarautar gagara badau a hannunki take, domin kaida kaya ai duk mallakar wuyane, duk mai shirin ganin barcinki ya tabbata shima bazaiyi nasaba, kece k’i gudu samaza gudu, jaruma mai dad’and’en tarihi, kin ajiye tarihin da babu wanda yake dashi a masarautar nan, koda kuwa mai martaba gagara badaune, ALLAH ya tsare gabanki ya tsare bayanki, mace mai kamar maza, mazanma a tafin k’afafunki suke ya uwar gijiyata”.
         Sosai kirarin jakadiya yayima mama Fulani dad’i, takuma kishingid’a a kujerar, cikeda izza tace, “inason ganin Galadima yanzunan”.
      Angama damusa k’i sabo, cika umarninki wajabtaccene a gareni ‘Yar sarki, matar sairi kuma mamar sarki, wata ran kakar sarki, ki huta lafiya babbar giwa”.
      Fita jakadiya tayi.
     Ta isa 6angaren galadima, inda sarkin k’ofa yashiga domin yimata iso, halin daya isake shugaban nasa ya razanashi, amma haka yadake ya isar da sak’on jakadiya.
     Da k’yar galadima yay masa nuni akan yabarta tashigo.
    Babu dad’ewa saiga jakadiya, ta rusina cikin girmamawa ta gaisheshi, bata damu da rashin amsawar tashiba ta isar da sak’on mama Fulani. hannu kawai ya iya d’aga mata.
   Kusan mintuna 7 da fitar jakadiya yamik’e dafe da kansa dayakejin tamkar zai fad’o k’asa, jiyay falon na juya masa, ya dafe bango da gyar kusan 2munute sannan yad’an lafa, haka yafito yana d’an tangad’i,  wajen mota yanufa, dan bazai iya zuwa sashen mama Fulani da k’afaba, saboda akwai tazara sosai a tsakaninsu.
     Da sauri sarkin mota yataso ya bud’e masa, shima shiga yayi mazaunin driver, sauran dogaranma suka shishshiga mota.
    Da k’yar galadima yafurta “sashen mama Fulani zamuje, sauran su zauna”.
       cikin girmamawa sarkin mota ya amsa, sannan ya sanarma sauran dogaran.
   dukkan jama’ar dake falon idanu suka zuboma Galadima daya shigo dafe da kansa, baima kowa magana ba yasamu can gefe ya zauna, har yanzu hanunsa na saman kansa, muryarsa a shak’e yace, “barkanku da dare”.
        Hakan yayi masifar k’ona ran mama Fulani, saboda ma ya rainata tare zai gaidata da kowa? kuma bazaizo gaban taba ma yabata girmanta?.
      A falonma wasu sun amsa wasu basu amsa mishiba, shi baima San sunayiba, ta kansa kawai yakeyi.
       Cikeda izza mama Fulani tace, “to isashe, gaisuwar ma saina rok’a ko yaya”.
        Dukda halin dayake ciki bai hanashi sakin guntun murmushiba, ya janye hannunsa daga goshinsa, idanunsa dasuke matuk’ar jajur yad’ago ya kalleta, ba mama Fulani niba kowama a falon ya firgita daganin idanunsa, hakan ya tabbatar musu da bashida lfy kenan.
     Ahankali Yakuma furta  “bagykanki da hutawa”.
       “ALLAH yarabamu da bak’in hali” . ‘mama Fulani tafad’a batareda ta amsa gaisuwar ba’.
    Baice uffanba ya maida kansa ya duk’ar, tareda kuma tallafe goshin yana ta6e baki.
    Idanun Ummu Hasheem yacika da kwalla saboda tausayin Galadima, ko kad’an batasan bashida lafiya ba, dukda d’azun ta aika bayinta su duba matashi suka tarar yafita.
      Mama Fulani kam baki ta k’ya6e tareda kuma hard’ewa a kujera, takai dubanta ga wani dake gefenta, Matawalle! ahad’amin video call da Zeenah yanzunan”.
        “angama ranki ya dad’e” Dan danan yahad’a video call bayan yakira wata number, wata kamilalliyar matace ta bayyana ajikin System d’in, tana sanye cikin shigar kamala, kallo d’aya namata Na hango kamannin Galadima tartare da ita, dukda kamar tafisa haske, hakkane ya tabbatar min da Momma ce.
     Cikin girmamawa ta gaida mama Fulani, ita kuma ta amsa cikeda k’asaita sannan tafara magana kamar haka.
       “nasan kowa yasan miya taramu anan wajen?, bana buk’atar maimaita wannan shed’ancin a harshena, wanda kuma ya aikata yasan kansa, Dan haka hukunci biyune, yanada za6i aciki. Na farko tozarcin da yayama masarautarnan da zubar mana mutunci mun haramta masa auren kowacce yarinya data fito daga kowacce masarauta, na biyu ya gaggauta fidda matar aure acikin shekararnan kafin yaje yayma wata ciki a waje akawo mana d’an tsakar gida a masarauta,  kokuma mu muza6a masa acikin bayin gidannan, hukunci na farko babu sasauci acikinsa kuma babu canji, Na biyu yanada za6i nemowa komu nema masa. Wannan shine tabbataccen hukuncin kotun fulani. Idan akwai mai abun fad’a sainaji?”.
     Kowa ya girgiza kai alamun a’a, wasu hukuncin bai musu dad’iba, wasuko yamusu fiye da zaton mai karatu.
     A hankali Galadima ya yunk’ura yatashi batareda yacema kowa uffanba yanufi hanyar fita.
        “to fand’ararre, daka tafi ba’a gama magana ba ai uwarka zataji, mara mutunci mai bak’in hali”.
     Juyowa Galadima yayi ya kalli mama Fulani, wani k’asaitaccen murmushi ya sakar mata sannan yay salute nata yafice abinsa”.
      Mafi yawansu saida suka zaro idanun mamakinsa, dama Kowa yasan galadima baya tsoron mama Fulani a masarautar, duk masifarta saima yagadama yake amsata, gaisheta kam saiya zo k’asar yatafi ma bata ganshiba. Iya kacinta tayi masifarta da sababi ta hak’ura, babu yanda ta iya dashi.
    Murmushi kawai shima sarki yayi baice komaiba.
      Mama Fulani kam kasa koda motsi tayi a kujerar saboda abin kunyar da galadima yayi mata gaban kowa, ta tsani shed’anin yaronnan mai ido a tsaitsaye dabaya shakkar kowa. Kwafa tayi sannan tatashi tabar falon tana tafiya cikeda mulki da izza.
      Gaba d’aya suke fad’in ALLAH ya huci zuciyar sarauniyar sarakuna.
        Duk abinda ke faruwa Momma naji kuma tana gani, amma dayake Galadima yana bayan laptop d’in bataga miyayiba, hasalima bataji ko sau d’aya yayi magana ba, hakanne ya tada hankalinta, mama Fulani Na barin wajen ta katse call d’in, waya ta d’auka takira number Galadima, amma harta tainke bai d’agaba.
     Kira Na biyu ta sakeyi, hakan yay dai-dai da shigowar Galadima falon dafe da kansa.
     Da k’yar ya iya d’aga wayar, muryarsa a shak’e yace, “Momma zan kigyaki anjima” bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
      Hankalin Momma yakuma tashi, tasan ransa yakai k’ololuwar 6aci, da sauri ta danna kiran Harun, yana d’agawa ko gaisuwar dayake mata bata amsaba tace, “Harun maza jeka duba min Moh’d yanzunan”.
      Yanda yaji Momma Na magana shima kansa saiya kid’ime…..
.........
Ayusher tafita tasiyo min credit domin kiran Fu’aad.
      Jikina a sanyaye nagama loda katin, tunani nakeyi shin Fu’aad zai kar6eni bayan yaji abinda yafaru a jiya zuwa yau? tunda komai akan idonsa yafaru. Na dad’e ina juya wayar a hannu kafin Nayi dialing d’in Number d’insa d’in, harta tsinke bai d’agaba, ban damuba Na sake kiransa da tunanin ko baya kusa da wayarne.
    Bugun farko kuwa ya d’aga wayar………..????
Humm masu karatu, mi kuke tunanin zai faru tsakanin Munaya da Fu’aad a waya, zai kar6eta kokuwa sa6anin haka?.
   Yaya zata kasance ga Galadima kuma?.
    Wannan amsar tana a page 12 da zaizo muku ranar Monday????????????.
Barkanku da juma’a.
Musha weekend lafiya????????????????.
Team *_INNARO & MAMA FULANI_*????????????♀⛹????♀⛹????.
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*????????????
*_Typing????_*
  *_HASKE WRITERS ASSO…????_*
       _(Home of expert and perfect writer’s)_
       *_RAINA KAMA……!!_*
               _{Kaga gayya}_
         *_Bilyn Abdull ce????????_*
????12
     …….Murya a sanyaye Munaya tace, “Assalamu alaika”.
    “wa’alaikissalam”. ‘wata murya ta amsa sa6anin Fu’aad’.
         “Uhhm ‘yar uwa please, ko ina mai wayar dan ALLAH?”.
       “Mai wayar kuma? ai nice mai wayar”.
       Wani iri munaya taji a zuciyarta, suka kalli juna itada Munubiya dan a Hans free tasaka wayar. alama munubiya tamata akan tayi magana. kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace, “ayya ‘yar uwa sorry dan ALLAH, wlhy wanine yabani number d’innan mai suna Fu’aad”.
        “Fu’aad!”. ‘yarinyar ta maimaita daga can’, saikuma tace “to gaskiya ‘yar uwa yabaki wrong Number, ni sunana Afnan, ina Katsina state ne”.
        Wasu hawaye masu zafi suka zubo a kumatun Munaya, “shikenan ngd sis…, kiyi hak’uri”.
       “no babu damuwa”.
     Bayan Munaya ta katse wayar ta dafe kai tana hawaye, daga Ayusher har Munubiya basa Neman k’arin bayani, tunda sunji komai, Munubiya ta share hawayenta tana murmushin takaici, “kibarshi karki sake kiranshi, nasan shine yabama yarinyar nan wayar akan tace wrong number ne, ya ALLAH ka kawo mana sauk’i a wannan lamari dai”.
           Tsaki Ayusher taja, ta kamo hannun Munaya “sweet sis…, please wannan karya zama abinda zai ta6a zuciyarki, ki d’auki hakan matsayin ba komaiba, kuma hakan da Fu’aad yayi yasani kuma tabbatar da zargin danake a kansa, ku duba yanda yazage saimunje birnin gayu plaza aranar”.
        Gaba d’ayansu zuba mata ido sukayi cikin wani yanayi.
     Feena dake kwance tatashi zaune, “humm aini wlhy tunda zancen jaridar nan yafito zargina yana kan Fu’aad ne, Na barine akirashi dama danna sake tabbatarwa”.
        Munubiya tace, “sisters nifa duk Na kasan fahimtar zancennan naku fa, zargi babu k’yau ai, miye ribarsa idan ya aikata hakan? dukama yaushe muka San juna dazai yi hakan a garemu? yarasa kuma dawa zai mana hakan sai galadima?”.
       Zama Ayusher ta gyara, tafara musu bayani dalla-dalla. “tad’ora da fad’in kinsani ko saboda galadiman yayi?”.
       “to amma Dan zaima Galadima mu miye Na had’awa damu kuma?”.
    “wannan amasar tana wajen Fu’aad sister ”.
     Hankalin Munaya yatashi ainun, itafa ko kad’an bata ta6a kawo  Fu’aad acikin wad’anda take zargiba, amma maganar Ayusher tasata dogon nazari yanzu, duk da dai bawai tama yarda baneba kwata-kwata..
★★★★★★★★★★
Lokacin da harun ya iso sashen Galadima bai wani jira isoba yashiga, kwance ya iskeshi bisa 3seaters sam6al, hannunsa d’aya dafe da k’irji, d’aya dafe da kansa.
     Da sassarfa ya k’arasa gabansa “Sameer lafiya kuwa?”.
         Da hannu Galadima yamasa nuni da k’irjinsa da Kansa.
      “ya salam, Sameer! Shiyyasa naketa cemaka kacire abunnan a ranka, kafasan matsalarka batason yawan takura da tunani”. Wayarsa dake ringing ya Ciro a aljihu, Momma Ce ke kiransa.
    Cikeda girmamawa ya amsa sallamar data masa, sannan naji yace, “wlhy Momma bashida lfy, kuma k’irjinsa yake complain akai”.
        “ok Momma ”.
 Yana yanke wayar sai yayi kiran Dr Jalal.
      “Jaalal please kana gida kuwa?”.
    Bansan wace amsa ya bashi ba daga can, naji dai yace, “please kazo kaduba Galadima”.
    Babu dad’ewa saiga Dr Jaalal, damuwa sosai Nagano a fuskarshi saboda ganin halin da Galadima yake ciki.
        Harun ya taimaka masa suka kaishi bedroom, sannan yamasa allurar barci.
    Babu dad’ewa kuwa barcin ya kwasheshi.
      Su duka ajiyar zuciya suka sauke, Dr jaalal yama harun sallama yatafi.
      Yana fita Muftahu Na shigowa, gaisawa sukayi da Harun, sannan ya tambayi jikin Galadima d’in.
      Harun ya amsa masa Cesar da sauk’i.
     Anan sashen Galadima suka kwana, sai dai kowanne acikinsu da dalilin kwannan nasa.
        *_Washe gari_*
Alhmdllh Galadima yatashi jikinsa da d’an sauk’i, yakuma ji dad’in ganin Harun da Muftahu a tare dashi. bai iya zuwa masallaciba sai a d’aki yayi salla.
          Yana zaune akan sallayar yana azkar su Muftahu suka shigo, zama sukayi bisa Sofa suna jiran yak’arasa azkar d’in nasa.
       Bayan ya k’arasa ya juyo garesu, hannu ya mik’a musu sukayi musabaha, suka tamyashi jikinsa.
    Yace da sauk’i Alhmddlh, sannan yace, “Muftahu inason ticket, dan yau zan wuce India, ina buk’atar ganin doctor d’ina”.
       “ok babu damuwa, bara na bincika idan akwai jirgi mai zuwa India daret”.
       Harun yamik’e yana fad’in “bara ahad’a maka ruwan wanka to”.
      Kai ya d’agama harun, ya maida idonsa ya lumshe tareda jingina da Waldrop.
       Muftahu dake latsa waya yad’ago ya kallesa, “babu jirgin dazai tashi a yau, sai gobe 1:30pm”.
       Batareda ya bud’e idonsa ba yace, “bincika min ta Abuja ko legos. dan bazan iya kuma kwana a k’asar nanba yau, ina buk’atar ganin lilita”.
     Kai Muftahu ya jinjina ya cigaba da latse-latsensa a wayar, kusan mintuna 4 sannan yad’ago, “an samu, amma zai biya Abu-Dhabi  ya sauke Passenger’s, daga nan zasuyi hutun kamar na 1hour”.
       Idomsa a lumshen yace “yaushe zai tashi daga Nan?”.
        “12pm, yanzu na saya maka ticket d’in zuwa Abuja, jirgin zai tashi 8am ne”.
     “Ok bara na shirya to”.
     Harun dake tsaye yana saurarensu yace “bara naje Na watsa ruwa nima”.
     Shima Muftahu mik’ewa yayi suka fita tare.
     Galadima yashiga bathroom, kusan mintunansa 40 sannan ya fito, dauriya kawai yakeyi, amma shi kad’ai yasan irin suyar da zuciyarsa ke masa. tsaf ya shirya cikin Suit blue, rigarshi ta ciki Orange, yayi k’yau sosai, yana zaune bakin gado yana saka takalminsa Muftahu yashigo da sallama.
    d’ago idanunsa yayi akan Muftahu, sannan yatashi tsaye yana gyara belt nashi, “ya maganar binciko yarinyar nan?”.
     “Nagama komai, inason kasami nutsuwane sai muyi maganar daman”.
       Galadima dake gyara ‘yar sumarsa da bawani yatarata da uban yawa bane yace “ok, katura min komai zan duba, sannan inason kaje kuyi magana da commisshiner of police akan iyalan Manager d’innan”.
      “ok yalla6ai angama insha ALLAH”.
     Sallamar Harun suka amsa gaba d’aya, ya zauna kan sofa sannan yace “amma yakamata ma’aikatan plaza su koma aikinsu, naga jama’a kamar suna fassara abin dawani Abu daban kuma”.
      Murmushin gefen baki galadima yayi, ya ajiye Cumb d’in hannunsa yajiyo yana kallonsa “aini yanzun kuma babu kuma ta sigar dabaza’a fassara ni ba, inaga akan mace kawai yarage jaridu su buga duniya ta ganni, so sukoma aikin su kawai”.
     Daga Harun har Muftahu kallonsa suke cike da tausayawa. Muftahu yace wannan d’inma kansu sukai mawa, kuma ALLAH bazai barsuba”.
      “insha ALLAHU”. ‘cewar Harun’.
     Galadima baice komaiba, sai d’an kimtse kimtsen da ba’a rasabane ya k’arasa, su Harun kam suka fice suka bashi waje.
      Baifi mintuna 10 ba yafito suka fice, bayan yatsaya da bayinsa na mintuna biyar, bansan miya fad’a musuba, naga dai sunata faman godiya damasa addu’a.
        Aka bud’e masa mota yashiga, duk wanda yake k’ark’ashimsa saikaga fuskarsa ta canja alamun baya son tafiyar tasa.
 
    Kai tsaye fada suka nufa, bayan motocin sun tsaya aka bud’e masa yafito.
    Shi kad’ai yashiga fadan, cike take da dukkan masu ruwa da tsaki anata fadanci.
     Saida ya gaida sarki, sannan ya zauna mazauninsa kusada sarkin, sauran fadawan suka gaidashi cikin girmamawa, shima ya amsa cikeda mutuntawa.
        “ya adalin sarkinmu yau zan koma inda na fito, saboda inason ganin likitana”.
     Murmushi sarki yayi, sannan ya gyad’a kai bare da yayi maganaba.
      Da sauri Dogarawa suka d’auka da fad’in Sarki yajika Galadima, Yakuma amsa, yana maka addu’ar sauka lfy kuma.
      “ina godiya da wannan alfarma”. ‘galadima yafad’a cikin rissinar da kai alamun girmamawa”.
      Sarki yad’an gyara zamansa, ahankali ya furta “ka gaidamin da d’an uwana da gimbiya Zeenah, insha ALLAH nima nextweek ina nan zuwa”.
      “ina godiya ranka shi dad’e, insha ALLAH d’an uwanka zaiji”.
      “gyad’a kai kawai sarki yayi”.
     “An gaisheka galasima, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ALLAH ya kaika lafiya yabama adalin tsohon sarki lafiya, Alkairin ALLAH da ni’ima sukai a garesa, gaba dai gaba dai Galadima mai jiran gado, d’an sarki jikan sarakuna k…..”.
     Hannu ya d’aga musu alamar ya Isa.
      Ya risinar da Kansa domin girmamawa ga fada sannan yamik’e suna jera masa addu’oi, yayinda shikuma yake amsawa asaman la66ansa.
       Bai shiga sashen kowaba yay tafiyarsa, suna isa filin jirgi ko 20 minutes basuyiba jirgin su yatashi zuwa Abuja.
    Muftahu da Harun da dogaransa suka dawo cikeda kewarsa.
    Koda ya isa Abuja hotel yanufa kai tsaye, yakama d’aki danya huta, akwai kusan 3hours nan gaba kafin jirginsu ya tashi. Rigar suit d’insa yacire tareda tie d’in, sannan ya zame wandon da rigar cikin ya kwanta dagashi sai boxer da vest.
    Juyi kawai yakeyi agadon, Dan barci yakasa d’aukarsa, abinda yafaru a kwanaki biyunnan yakasa barin zuciyarsa, yarasa wane irin hasashe zaiyi ga masu aikata masa hakan… Ringing d’in da phone nasa tayine yasakashi bud’e idanunsa, wayar yajawo yana kallon mai kiran. *_Sweet papi_* yagani ajikin wayar, yay saurin d’agawa kafin ta tsike.
      Cikeda girmamawa tamkar yana a gabansa ya rissinar da kansa bayan yatashi zaune, “Barka da hantsi ranka ya dad’e”.
        Daga can aka amsa “da yauwa Muhammad, ina fata kana lfy?”.
       “Alhmdllh ranka ya dad’e”.
     “To masha ALLAH, dama mamanka Ce takirani takemin wasu bayani, duk da kafin kiran nata dama naga zantukan dake yawo a jaridu da yanar gizo, zuciyata bata yarda zaka aikata hakanba Muhammad, amma inason sanin gaskiyar zancen?”.
          “wlhy ranka ya dad’e sunyi hakanne kawai domin 6atamin suna, amma ainahin abunda yafaru shine………….”
      Nan Galadima ya zayyane masa komai.
      Murmushi mai sauti tsohon yayi, har Galadima Na jiyosa, sannan yace, “hummm! to yanzu kai kana wace nahiya ne?”.
       “Ina Abuja zan koma India, saboda jikina yana Neman motsawa”.
       “to to, hakanma dakayi dai-daine, amma a kwantar da hankali, komai mai wucewane, komai kaga yafaru da d’an Adam rubutaccene a littafinsa, dama ita rayuwa tana tafiyane da k’addara, yanzu zan isa fada, bayan kasamu nutsuwa idan kaje zamuyi magana, duk da watak’ilma nashigo ganin mahaifin naka k’arshen watannan”.
         “to shikenan, ngd sosai, ALLAH yak’ara tsahon rai da lafiya mai amfani”.
        “amin ya rabbi Muhammad” cikin tsokana tsohon yace “kaga d’annema, duk kabi ka susuce akan k’aramin Abu, kazo Na sanmaka jarumtata mana”.
        Dariya Galadima yayai (karon farko danaga yayi dariya????????) cikin tausasa harshe yace “haba dai, ai sai dai Na sammaka tawa,  nifa sabon jinine, ta ina mai shekaru 80+ zai fi mai 29 jarumta?”.
          Daga canma Sarki dariya yayi, cikeda k’aunar jikan nasa, “uhmyim tunda kace haka idan kazo saimu gwada kwanji ai”.
        “hhh tom kafad’ama inno ta tsumaka sosai, inba hakaba zatayi takaba”.
         “ja’irin gora zan kamakane ai, ALLAH ya tsare hanya, ka gaida iyayen naka”.
        “zasuji ranka ya dad’e, a gaidamin inno, tayi hak’uri wannan karon ban shigo naci tuwon taba, nazo k’asarne da uzurori dayawa, gashima banyi ko d’ayaba”.
        “zataji insha ALLAHU, babu komai, adage dai da addu’a watarana sai labari, *zakaran da ALLAH ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai yayi jikana kaji*.
        Murmushi Galadima yayi dan jin maganar kakan nasa, sukayi sallama cikeda k’aunar juna”.
     
     Ajiye wayar yayi yakoma ya kwanta fuskarsa d’auke da murmushi, yana k’aunar kakansa (mahaifin Momma) saboda shima yana nuna masa k’auna da kulawa, akan la66ansa ya furata “ALLAH ya k’aramaka tsawon rai my sweet papi”.
    Amin Galadima.
????bara nalek’o su munaya.
★★★★*★★★*★★★★
         Bansan yanda zan musalta muku irin bak’in cikin danakeba a yau, tundaga kiran Fu’aad zuwa yanzu zuciyata sai suya takemin, banida wata walwala, sai dai ina dannewa kodan kwanciyar hankalin innarmu da ‘Yar uwata Munubiya, dama tun randa abunnan ya faru bamu sake fita koda tsakar gidaba dagani har ‘yar uwata, abinci sai dai innarmu kosu Aryaan su kar6o mana.
      Habaici dai da gugar zana muna shanshi acikin gidanmu, innarmu bata cemusu uffan, nikuma mai maida murtanin damuwa ta hanani iya cewa komai, ‘yan biki dai zuwa yau kowa yakama gabansa, yanzu dagamu sai mune agidan.
     Sauk’inmu d’aya tun ranar innaro bata sake shigowa gidanba, inaga baba mai kanwa yahanata.
        Babu Wanda yay mana maganar komawa makaranta, muma kuma bamuyi yunk’urin zuwanba, kullum dai innarmu NATA k’ok’arin ganin munkwantar da hankalinmu, a koda yaushe cikin mana nasiha take dayimana kwatance da rayuwarta itada mama Rabi’a, takan Nuna mana muhimmancin hak’uri da amfanin yinsa, koda baka ci ribarsa anan gidan duniyaba zakaci ribarsa a lahira inda kowa ke rububin tara ayyukan alkairi.
      Alhmdllh muma mun fara rage damuwar kodan ganin farin cikinta, Abu d’ayane kecin zukatanmu shine maganar fidda miji da Abbamu yace nayi acikin sati biyu kacal, gashi kuma babu wani tsayayye a hannu.
     Duk mun rame mun zuge nida munubiya, dama gamunan bawani aukin kirkiba, ahaka muka cinye satin da abin yafaru.
     Yau ta kasance lahadi, wasu a yaran gidanmu sunata shirin ziyartar gidajen amare, kaf sa’aninmu ‘yan matan gidan sunyi shirinsu, Fauziyya, Fiddausi, Safara’u, Haleematu, amma ban da mu, Dan kogaya mana mu shirya ba’ayiba, saima Fauziyya Ce data tashigo da safe gaida innarmu take sanar damu wai mushirya zamuje gidajen amare.
     Dagani har Munubiya bamuce da ita komaiba, sai ‘yar dariya damukayi.
       Koda suka gama shirinsu basu nememu ba, sai Fauziyya Ce tashigo danta mana magana akan mufito.
     Turus tayi Dan ganinmu babu wani shiri, hasalima muna falo zaunene, Munubiya ta kwantar da kanta bisa cinyata ina kwance mata kai, innarmu kuma Na zaune gefe  suna waya da mama Rabi’a, sai Aiyaan da Aryaan daketa faman buga game.
       Hira mukeyi da Munubiya akan wasu write-ups datake dubawa a Instagram da akayi akan maganarmu da galadima, cikin damuwa take karanta writeup d’in, shiyyasa bamuga shigiwar Fauziyya ba saida tayi magana…
       “wai sisters kuna nufin ma ko shiryawa bakuyiba?”.
     Gaba d’aya muka kalleta, nayi murmushi ina fad’i “kiyi hak’uri Fauziyya, kutafi kawai, har yanzu fita bata kamacemu ba, dan abubuwa basu gama daidaitaba tukunna”.
        Cikeda damuwa ta gyad’a kai, jiki a sanyaye tace “shikenan saimun dawo”.
       “ok to Ku gaida mana amare”.
      Kanta ta jinjina nanama tana ficewa.
       
     Munubiya tace, “ALLAH Sarki Fauziyya, itadai tana sonmu”.
        Nad’an murmusa ina taje mata Wanda Na tsefe, “Munu…. nima ina k’aunar Fauziyya wlhy itada mamansu, sune kad’ai suke sonmu agidannan, Na tabbata wannan fitar dama ba’a sota damuba, itace kawai taketa k’ok’arin taga munje d’in”.
        “wlhy hakane sweetheart ”. ‘cewar Munubiya’.
    Innarmu dai tanata waya, Dan haka batace mana komaiba…..
★★★★★★★★★
      Lokaci na gabatowa yay shiri yabar hotel d’in, zuwansa airport babu dad’ewa jirginsu yad’aga, sun tsaya a Dubai Abu-dhabi sukayi hutun 1hour sannan suka nufi India.
      Tunkan jirginsu ya sauka Sauban da Samha sukazo d’aukarsa.
     Dan haka yana fara taka matakalar jirgin suka hangosa, cikeda jin dad’i suka nufo gareshi.
        Duk da fuskarsa babu walwala hakan bai hanasu nuna farincikin ganinsa ba, shima dai yayi farin cikin ganinsu, duk da kwanaki 4 kacal kenan da barinsa k’asar.
       Sauban ya kar6i bag d’in hannunsa yana fad’in yaya  welcome”.
        Kansa ya shafa yana lumshe ido alamun amsawa.
    Samha ma tace “Wellcom back Uncle Sam”.
          Ahankali ya furta Thanks you dear, ya school?”.
        “Alhmdllh Uncle, ya kabaro Nigeria? ”.
         Murmushi kawai yayi batareda ya amsa mata ba, yasan surutun Samha bamai k’arewa bane, yana amsa wannan wata zata jeho masa.
     Sauban ya bud’e masa back seat ya zauna, sannan yarufe shi yakoma mazaunin driver, Samha Na gefensa.
      Idonsa ya lumshe ya maida Kansa ya jingina da kujera.
       Wani madaidaici Gida suka isa, Wanda baza’a kirashi k’aramiba, sannan ba k’ato baneba, sai dai muce tsaka tsaki.
        Samha ce tafita da kanta tabud’e gate d’in, Wanda ana ganin komai dake farfajiyar gidan ta jikinsa daga waje. Sauban ya ida shiga da motar, kusada wasu motoci uku yay parking, Samha data k’araso tabud’ema Galadima yafita.
         Kusan atare suka shiga falon gidan, yana gaba suna baya.
     Masha ALLAH nafad’a saboda ganin tsaruwar falon, sai dai shiru gidan alamun babu kowa a ciki.
        Ya zube bisa rukunin kujerun farko dasuka kasance golden color and white. Isaka yad’an turo daga bakinsa sannan ya kalli Sauban dake shirin zama shima.
      “yanaji gidan shiru? inasu Momma ne?”.
          “duk suna hospital, har jakadiya ma, zamu tafi d’akko kanema Aunty Mimi tatafi itama, dama ita kad’aice agidan saboda mu muna school ”.
          “Ok, ya jikin Abie?”.
       “hummm da sauk’i yaya”.
        “mik’ewa yayi yana guntun murmushi, tunda yafara girma yafahimci mahaifinsa Na kwance yakejin idan antanbaya Momma jikin Abie tana cewa da sauk’i, amma shi shekaru kusan 25 Abie Na kwance amma shifa baiga wannan sauk’inba, kawai suna dai fad’ane, sauk’i d’ayane zai iya cewa yagani shine magana da idanu da Abie keyi kawai.
      Da wannan tunanin ya haye steps d’in benen, yana tafiya yana sasaauta tied d’in wuyansa. ahaka harya k’arasa d’akinsa.
           Komai needs kamar yanda ya barsa, (kullum ne babu fashi sai Samha ta gyara d’akin) Komai a d’akin fari ne, sai golden dasuka kasance d’ai-d’ai. d’akin yayi k’yau sosai, sai tashin k’amshin turarensa daya manne yakeyi, gakuma na air fresheners, saiya had’u yana bada wani ni’im taccen k’amshi. kayansa yashiga cirewa d’ai-d’ai yana sagewa jikin hanger. wanka yashiga sannan ya gabatar da sallan data riskeshi a hanya ………
★★*★★*★★*★★*★★
       Da daddare muna zaune munacin tuwo saiga kiran Abba yashigo wayar innarmu, tana d’agawa yace ta turo masa mu.
     To kawai tace ya yanke wayar.
       Kallonmu tayi ad’an sanyaye, tace “idan kun gama cin abincin kuje abbanku Na kira”.
      Daga ni har Munubiya sai da gabanmu yafad’i, jiki a sanyaye muka amsa da “to innamu”.
         Kasa cigaba Dacin abincin mukayi, dole muka ajiye kawai mukaje muka wanko hannu………………????
????ko wane kira kuma Abba yakema su Munaya?????.
Barkanmu da dawowa????, ina fata duk kuna cikin k’oshin lafiya?????????????.
To gashinan Na k’ara yawan page Masu k’orafi????⛹????♀⛹????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button