Labarai

BIDIYO: Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce Aljanu biliyan uku ne su ka karbi Darikar Tijjaniya

Darikar Tijjaniya ta na da Almajirai 3,000,000,000 cikin Aljanu – Dahiru Bauchi

– Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce Aljanu biliyan uku ne su ka karbi Darikar Tijjaniya

– Babban Malamin ya ce daga cikin wadannan Aljanu, akwai mukaddamai miliyan 200.

Akwai yiwuwar a rika amfani da Aljanun domin maganin masu garkuwa da mutane

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi wata magana wanda ta ba dinbin mabiyansa da sauran al’umma mamaki.

Shehin malamin ya bayyana cewa akwai wasu kebantattun mutane da su ke iya sadu wa da aljanu. Ya ce ya na daga cikin masu mu’amala da su.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce wasu suna ganinsu, har su yi magana da su, kamar yadda shaidanun mutane su ke hulda da shaidanun Aljanu.

A cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi akwai Aljanu muminai, daga cikin su har mabiya Darikar Tijjaniya wanda yanzu adadinsu ya zarce biliyan uku.

Shehin darikar ya ke cewa daga cikinsu akwai mukaddamai miliyan 200 wadanda su ka yi nisa a Tijjaniya.

Duk da tulin wadannan dakarun Aljanu da suka karbi darikar Tijjaniya, shehin malamin ya ce ba za a rasa wasu dinbin mabiyan da ba a san da zamansu ba.

Dattijon malamin yake cewa suna kokarin ganin an zakulo manyan malamai daga cikin Aljannun da aka ba Darikar Tijjaniya, da nufin yada addini.

“Mu na zama da su, amma babu wani alkawari da aka yi da su na yin abin da bai kamata ba.” “Mu ne mukaddamai a cikinsu” inji Shehi Dahiru Usman Bauchi.

Dahiru Usman Bauchi ya ke cewa an kawo shawarar ayi amfani da wadannan rundunar Aljanu domin ceto ‘Yan Tijjaniya daga hannun miyagu a Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button