GURBIN IDO

GURBIN IDO 10

“Bai fito ba har yanzu anni,duk da munyi magana,amma ina da tabbacin nan da dan wani lokaci koda baiyi kiran kowa ba zaiyi kiranki” ya fada with full confidence,saboda yasan tsakaninsa da annin

“Shikenan,ka sake kula don Allah jabir”

“In sha Allah anni” ya fada shima zuciyarsa na karyewa,bayason wannan ja’afar din na yanzu,yafi qaunar ja’afar dinsa na asali,duk da dama tun asali azama da ja’afar din sai shi,duk da yadda mutane suke daukansa suke kuma kallonsa….amma zai iya cewa bai taba rayuwa da wani mutum me dadin zama irin ja’afar din ba,wasu abubuwa ne game tattare dashi da idan ka fahimcesu shikenan.

Wunin ranar gaba daya anni ta qarar dashi kan tunanin maganganun yuuma,ita kanta yuuma ta fuskanci yau din annin akwai damuwa fal tattare da zuciyarta,don ko abincin rana data kawo mata bata cishi ba sai kusan gefin la’asar,ta jima sosai tana waya da daya daga cikin yayanta.

Sanda rana ta kammala faduwa,wanda ya zamana lokaci ne na sallar magariba,annin na daya daga cikin mutanen da basa wasa da ibada,wannan ya sanya ubangiji ya bata kyakkyawan tsufa da kuna qwarin jiki,banda ciwon qafa babu abinda yake damunta,zaka zaci shekarunta basu kai yadda take fada ba.

Tana saman abun sallah tana lazumi,hannunta riqe da carbinta,ta tsakankanin labulen dakin tana hangen wulgawar mutanen gidan kowa na sabgar gabansa.

Waiwayawa tayi ga laila dake kwance tana latse latsen waya abinta sakamakon bata sallah ta watsa mata harara,ta shafa addu’arta tana shirin mata magana akayi sallama daga tsakar gidan.

Tsam anni tayi da ranta,saboda sautin muryar kamar tasan me ita,hakanan sai taji kamar ta saba jin muryar dama. Yuuma dake alwala tana wanke qafafuwanta ta waiwayo,sosai mamaki ya cikata,karon farko bayan wasu shekaru da suka shude rabon da taga maimunatu cikin gidan,don haka ta miqe cikin kulawa

“Lafiya maimunatu?” Tafukan hannuwanta dake a dunqule ta budewa yuuma,kyakkyawar sarqar wuya ta ainihin dutsen wuri da kuma murjani na asali ta bayyana

“Kun yada wannan ne a gidanmu dazu” zubawa sarqar idanu yuuma tayi,don tasan bata da ita,dutsene maj tsada wanda su kansu fulani sunsan dajarsa

“Anya kuwa?…..amma….qarasa rumfata ko anni ce,don nasan da laila ba zata saka wannan ba” kai ta gyada tana sakin siririn murmushi,sannan ta fara takawa zuwa rumfar yuuman,gabanta yana dukan uku uku,batason ta hadu daada mahaifiyar ibrahim,bare shi ibrahim din kansa,ita daya tasan irin jan kunne da kums gargadi da tasha daga wajen inna furera,ba shakka banda akwai qudurin da innar keson cimmawa ma,babu abinda zai sanyata ta kawo musu sarqar.

“Wa’alaikumussalam,shigo mana” anni ta fada tana zubawa maimunatun idanu sanda take sanyo kai cikin dakin,idanunta ya sauka ga gefe wuya da kuma kunne zuwa kuncin maimunatu karo na barkatai a yau din,ita din bata jiya bace ba kuma ta yau bace,wannan tabon tun dazu data kalleshi ta tabbatar da cewa na duka ne,to amma me yarinya kamar maimunatu tayi da za’ayi mata irin wannan dukan?,me aka saka akayi mata wannan dukan dashi?,sai taji ranta yana baci abinda.bai faru ba a yanzu.

Ita din wata irin macace da bata qaunar zalunci ko kadan,ko kai waye,ko yaya kake da ita,matuqar ta fuskanci kana da dabi’a ta zalunci yanzu zaku raba hanya.

Gaban annin ga durqusa,tasa hannu biyu tana miqa mata sarqar,anni ta miqa hannu ta karba

“Hukumullahi…ni nayar da ita,tabbas,to kinga basan ma ta fadin ba banda Allah ya tsananta rabo yanzun kin ganta kin kawomin,da haka zan yita bulayin nemanta” anni ta fada tana sakarwa maimunatu murmushi,zuciyarta da ruhinta cike da soyayya da kuma kaunar maimunatun,halayenta mabanbanta ne da halayen sauran al’umma,abar yabo ce ta gaske kuma a zahiri,godiya ta yiwa maimunatun sosai,tans juya abun a ranta ta tayar da sallah.

     "Anni.....gaba daya yau tunani ya sanyamin ke agaba,komai yayi zafi maganinsa Allah anni,aci gaba dai da addu'a,wataran komai zai warware in sha Allahu" yuuma dake ajewa anni kwanon tuwo ta fada,don idan annin tazo har ta koma babu ruwanta,irin tasu cimar takeci,takan ce ko a gida rashin samun me tsaya mata da irin cimar ne yadda takeso,amma ita bata da kamar irin abincinsu.

     Ajiyar zuciya annin ta sake tana miqe daya qafar tata data jima a lanqwashe ta fara yi mata tsami

“Ramatu,inajin wani abu a jikina tattare da yarinyar nan”

“Wa fa?” Yuuma ta tambayi anni tana tattara hankalinta gareta

“Maimunatu”

“Ohhh…..maimunatu?”

“Ita…..tun dazu da mukayi magana dake ramatu nake juya zancan cikin raina,da magaribar nan bayan yarinyar tazo ta kawomin sarqa ta,sai gaba daya tunani ya damfaru a kanta,na lura da irin dabi’un da nake buqata tattare da yarinyar,ta hada juriya haquri da kuma amanar da zata iya zama da ja’afar,dabi’u da kuma halayen da tabbas zata iya dawo da ja’afar yadda yake ja’afar dinsa”

“What!” Laila dane kwance ta fada cikin rata,har maganar tata taso ta fito fili

“Me anni ke fada ne?,ta manta waye ya ja’afar?,ta manta waye yaa J?,the classic and unique guy?,ya ja’afar fa ake magana da wata bafulatanar ruga?,saura kadan ta miqe ta zauna,amma sai taci gaba da kwanciya,tanason jin yadda maganar zata kaya.

   Dukka idanunta yuuma ta fidda tana duban anni

“Anya kuwa anni?,bakiyi ragon tunani ba?ja’afar fa?”

“Me yasa kika ce haka ramatu?,ko hasashe na bai hasaso dai dai kan dukka nagartarta ba?” Kai yuuma ta girgiza a hankali tana juya abun a ranta,bai kamata tayi shuru ba wani abu ya kasance daga baya kuma ta zama abar zargi ba daga kowanne bangare,abu me muhimmanci ta fara gayawa anni wace ainihin maimunatu tukunna

“Dukkan abinda kika hasaso akan halayen maimunatu haka suke,yarinyar har tafi haka ma,dukka rugar nan sunsan da wannan,saidai wani baqar al’ada da jahlici gami son rai sun rufe musu idanu basa ganin wannan,bari na gaya miki wace maimunatu tun daga tushe,wanda ba kowane cikin rugar nan ya sani ba,domin kuwa,ni din,nice qawa qwaya daya tilo da mahaifiyarta keda ita a rugar nan,wadda bata da kamata,wani rikici da ya faru tsakanin gidan da gidan nan yasa bappa ya yanke huldata dasu saboda wanzar da zaman lafiya,abinda ya rabamu kenan da shatu,har zuwa sanda ta koma ga mahaliccinta” kai anni ta gyada tana bada hankalinta zuwa ga yuuma,yayin da itama yuuma ta nutsu sosai ta fara yima anni magana

“Furera mahaifiyar gaje,waddda kukayi ciniki a hannunta,mata ce ga jauro,wadda keda yara biyu dashi,macace mara mutunci ta gasken gaske,wadda ba kasafai ake tabota ta qyale ba,me son abun duniya ce da kuma masifar son ‘ya’ya,asalinta bafulatanae gembu ce,jauro ne dan wannan rugar,muna zaune tare da ita tsahon shekaru,kwatsam tayi baquwa,wadda ta shigo rugar nan tare da furera da taje ganin gida,matar itace shatu,wadda tazo da diyarta maimunatu……sun shigo tare da tarin dabbobi wadda dukka dabbobin nan mallakin shatu da diyarta maimunatu ne,amma kuma a idanun kowa dabbobi na furera ne,don a haka ta gayawa kowa wannan labarin,ta shaidawa mutane cewa gadonsu dama taje gida karbowa ta taho dasu,ta kuma hado da wadda zafa dinga mata kiwo tana biyanta wato shatu,abinda zai baki mamaki,shatu ba kowace bace a wajen furera face ‘yar uwarta da suke uba daya,bata da ikon musawa ko qi,saboda a sannan shatun na cikin wani yanayi na tashin hankalin rayuwa,tana neman mafaka,mahaifin maimunatu baqo ne,irin baqin dake shigowa garin na gembu saboda huldar kasuwanci da kuma yawon buda idanu,a nan yaga shatu ya kuma tsaya kai da fata sai daya aureta,a nan garin ya barta saboda ta nuna tafison zama cikin danginta,yana zuwa yana ganinta yayi mata kwanaki ya koma,mutum ne mai arziqi,don haka gida na alfarma ya ginawa shatu,ya zuba mata dukka kayan alatu da more rayuwa,ta yadda gidan shatu shi ya zama abu kwatance da kuma burin kowa cikin garin nasu,wannan ya haifar da hassada daga zuciyar ‘yan uwanta da suke ‘yan uba,saboda ita shatu su biyu mahaifiyarsu ta haifa a gidan,ita da ‘yar uwarta sa’ade,kusan jinin dakinsu ne haka,sannan kuma da baiwar zallar kyau da Allah yayi musu fiye da sauran ‘yan uwansu,itama sa’ade nata mijin me hali ne sosai,hakan ya sake haifar da zallar ‘yan ubanci a tsakaninsu,saidai sunata dannewa saboda suna rabarta suna kuma samun akhairai da abun duniya daga wajenta,kasancewarta ba mai rowa ba,a haka ta haifa maimunatu,dukka alhaji na zuwa wajenta ne yayi mata satittika ya tafi,bayan ta.haifi maimunatu yake maganar zai kaita taga danginsa,saidai kuma wata tafiyace ta taso masa,wanda ya dauki tsahon watanni kafin ya dawo,koda ya dawo din kuma shima yana da niyyar kaita,har sun shirya sun saka rana,yace zai taho takanas daga kano ya dauketa. Shiri sosai shatu tayi domin zuwa ganin surukanta,ta shirya maimunatu da kyau wadda ke samun gata kamar babu gobe,itama haka,saidai haka ta yita jiran alhaji amma shuru babu shi babu dalilinsa,nata da wayar hannu bare ta nemeshi,haka tayita zaman jiransa har dare yayi ta fidda tsammani,ta sanyawa ranta qila wani abune ya tareshi,ta barwa gobe. To washegarin ma dai haka ta yita jiransa shuru babu shi babu labarinsa,haka wata washegarin,wasa wasa sai ga kwanaki nata tafiya shatu bata sake ganin gilmawar alhaji ba,abun ya daga hankalinta qwarai da gaske,tafi tafi watanni suka fara shudawa shuru babu shi babu dalilinsa,ga ciki da ya bayyana a jikinta,ita dai ta yarda da alhaj dari bisa dari,saboda iya tsahon zamata dashi tsakaninsu ita dashi babu komai sai son barka,mutum ne mai son addini da kuma kiyaye dokokin Allah,kusan a wajensa shatu tayi karatun addini mai dan dama wanda ta dinga koyawa maimunatu,duk da a sannan ta sanyata makarantar islamiyya da boko,amma kamar tasan yadda rayuwa zata juya musu,sai take zama duk bayan sallar magariba take mata nata karatun,ganin cewa yarinyar tana da budaddiyar kwanya dake saurin kwashe karatu,don tun bata isa sakawa a makaranta ba ta sanyata,tace tayi wayon acan,hakan yasa adan lokacin ta samu karatu me yawa,tana cika shekara tara zata shiga ta goma ta gama primary,mahaifinta nada niyyar yi mata shirin shiga makarantar gaba wannan abun ya faru”

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button