GURBIN IDO

GURBIN IDO 11

11

“Yau da gobe bata bar komai ba,hakanan zara bata qyale dami ba,dukka kayan abincin da shatu ke dasu wanda alhj ke jibge mata suka faru suka qare,ta fara kame kame,a sannan yan uwanta suka fahimta,sukayi mata caa,yar uwarta saade tace kada ta kulasu,ita ta dinga taimaka mata har zuwa wani lokaci,wanda kishiyar mahaifiyarsu wadda wajenta suka rayu sanadiyyar rasuwar mahaifiyarsu tun suna qananu ta tayar da borin qarya,ta tara manyan gari,ta fada musu qabli da ba’adi kan rashin dacewar zaman shatu ita daya cikin gidan,tace saidai lallai ta dawo gabanta da zama,saade yayar shatun bata qalubalanci hakan ba,hakan yayi,duk da tasan badon Allah inne tayi hakan baAmma kuma bayan giya akwai wata caca,maza maza tayi ta sanya aka saida gidan da shatu ke ciki,tunda mallakin alhj ne,ya ginawa shatun,ta tattara kudin ta siyawa shatun dabbobi ta damqa mata,saboda gudun abinda kaje yazo,babu jimawa shatu ta tattara ta koma gida ita da maimunatu,gidan da suka fara sabuwar rayuwa me cike da qunci da kuma takura,wahalhalu iri daban daban,zuciyar shatu na cike da qauna da kuma begen mijinta,jiki da zuciyarta sinqi yarda da zancan daketa yawo a garin kan cewa,mijinta guduwa yayi ya barta,tafi kowa sanin halinsa,tayi imani bazai aikata mata haka ba. Zama ya sake tsanani a wajenta sanda inne ta fahimci cikine da ita,tayi tsalle ta dire kan ba za’a haifa mata dan da bashi da uba ba,maganar data tsayewa shatu da saade a rai,ta kuma kusan haifar mata da ciwo,a lokacin saade bata kusa da ita,kasuwanci ya shillata ita da mijinta zuwa benin republic,wanda tayi matuqar baqincikin hakan,saboda sanin halin da ‘yar uwarta take ciki,amma babu yadda zatayi dole tabi mijinta. Ana tsaka da wannan fa shine inna furera taje garin,ita tunda ta qyalla idanu taga dabbobin da shatu ke dasu tayi mata romon bakin ta biyota rugarsu tayi xamanta,ta kula da dabbobinta ta haihu a can babu takura. A zaton shatu ta samu mafaka a wajen yayartata,saidai tun basu kai ga shigowa rugar ba ta fara yanka mata sharuda tare da shaida mata dokokin da rugar ke dasu,suka kuma yi yarjejeniyar dabbobinta zasu shiga a mazaunin na ita fureran,idan ba haka ba zaayita kawo musu farmaki ana kashesu tunda ita baquwa ce. Ko a sannan shatu shekarunta basu fi ashirin da hudu ba,saboda auren wuri akayi mata kamar yadda aka saba.

   Shatu ta shigo baquwa a rugar nan,wadda hatta da kyanta ya banbanta da irin namu,babu tausayi ko tsoron Allah furera ta maida shatu da maimunatu tamkar bayi da basu da 'yanci,shatu bauta maimunatu bauta,Allah ya zubawa shatun wani irin haquri juriya da kuma kau da kai wanda cikin irin nata ta sanwa maimunatu,don babu lallai tayi yakai irin nata,a haka dai suke rayuwar. Abinda ya faru ya kuma janyo shatu da maimunatu suka zama abun qyama shine......a al'darmu ta fulani,baka ganin nagge ko sauran dabbobi ka nuna su tankasu,komai kyau da burgewar da suka baka,cikin irin haka,cikin rashin sani shatu taga wasu nagge na bappa labaran,yana gab da fita dasu kudu,ranar an fiddasu kiwo ta nuna wata babbar nagge a cikinsu tace a haka kamar lafiyayya me kyau da ita,amma kuma bata da lpy,suka yita fada dame kiwon,aka mata ca,ta bada haquri,saboda mantawa da tayi ta aikata hakan,kuma tace tana musu tsoron asara ne,magani ya koma a maidata gida a bata,koda suka dawo gida baice bata da lafiya ba yadda shatu ta fada,ba'a wayi gari da naggen ba ta rasu,rigima sosai daada taso a tayar,amma bapp ya hana,abinda basu sani ba ni da kaina bayan asuba na fita zan dora sanwar safe,na lura da naggen bata da kuxari yadda ya kamata,ni da kaina nasan tabbas bata da lpy,to amma dana fada qaryatani daada tayi,tace kawai dai don tana zuwa wajena ne yasa nakeson kareta,anyi wannan rigimar ta mutu,shatu da tsohon cikinta taje diban ruwa matan gidan barau daya daga cikinsu ta takaleta da fada yadda suka saba mata,tunda muke da shatu bata taba gayamin ko kawomin qarar kowa ba,amma inajin labarin yadda wasu cikin rugar suka matsanta mata,a ranar taso dauke kai amma yau da gobe,ga yanayin tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe,talatu bata duba wannan ba ta dinga ja mata riga shatu na gocewa,daga qarshe dai da talatu taga ba zata kulata ba sai ta tureta,wanda sauran kadan ta afka cikin rafin,Allah ne kawai yayi ruwan ba shine ajalinta ba,sosai ran shatu ya baci bayan tasha da qyar,cikin bacin rai idanuwanta cike da hawaye ta kalleta

“Na dauka ko banci darajar komai a wajenki ba zanci darajar cikin dake jikina,tunda kema macace,idan kinyi hakane don ki tozarta ni kije,Allah yana gani,kuma ina fatan kiga sakayya da gaggawa anan kusa” daga haka shatu bata qara ba bata rage ba,ta dauki ruwanta ta wuce,suka taru suka yita maida magana,tare da maido maganar nagge,a nan suka fara qulla wataqil mayya ce ita din,kwana biyu tsakani kuwa talatu taje diban ruwa ruwan yayi ciki da ita,ya kuma zama ajalinta,aka fara lugwigwita magana tare da fara yada jita jitar shatun mayyace,kafin kace me?,magana ta fantsama a gari,dangin talatu da sauran mutane ‘yan bani na iya suka dauki sanduna sukayi gidan furera kan sai an fiddo shatu sun kasheta,ya tabbata mayyace ita,da qyar da sudin goshi qurar ta lafa,baiwar Allah shatu,ashe sanadin wannan tashin hankalin naquda ta tasammata,furera haushin abinda ya faru tayi banza da ita,daga ita sai maimunatu ne suka yita fama,daga qarshe tace maimunatun ta lallaba ta kirawo mata ni,har maimunatu takai bakin qofa ta qwala mata kira,saita tsaya,ta yafitota da hannu ta koma gaban shatun ta duqa

“Daada,akwai wani abun da kike so ne?” Murmushi ta sakar mata,ta daga hannayenta ta cirw dukka duwatsun jiki da maimunatu ta dade tana qulafucin tabar mata ta zura mata su,saidai yarinyar a sannan sam bataji farincikin da take ayyanawa zataji ba duk sanda daadar tata tabar mata dutsunan

“Daada kin barmin ne wai?” Kai ta gyada

“Na bar miki maimunatu……kiyi haquri kiyi haquri…..kiyi haquri kinji,ki fuskanci rayuwa duk yadda tazo miki,ki zama mai gaskiya da amana,karki yadda a kamaki kinci amanar wani,idan kinga saade,kice ina mata fatan alkhairi” sanda yarinyar ke gayan abinda uwar tace nayi mamakin yadda ta iya riqewa,hankalin maimunatu a sannan ya tashi sosai duk da qarancin shekarunta,ba kowa zai gane hakan ba sai wanda irin haka ya sameshi,cikin rudewa tace

“Daada” hannu ta daga mata

“Barci nake ji,yi sauri ki kiramin yuuma” maganar data sanya maimunatu tashi ta fita a dakin da gudu,fitar da ta zama silar rabuwarta da mahaifiyarta kenan rabuwa ta har abada,don koni sanda na shiga wajen shatu rai yayi halinsa,haka akayi mata sutura bata ko haife abinda yake cikinta ba,sanda na koma gida da daddare randa shatu ya rasu,tunda na tsaya na taya maimunatu da bata dame rarrashinta zama,mahaifiyarta ta rasu ta barta babu ko mutum daya da zata jingina dashi tayi kuka taji sauqi cikin ranta,Bappa da kansa ha sameni,ya shaida min ya yanke hulda da wata alaqata da duk abinda ya shafi shatu matuqar shike aure na,duk randa na kuskurewa hakan kuwa,zai dauki tsatstsauran mataki a kaina,bansan me aka gayawa bappan ba bayan fitata wajen shatu,amma dai na sani cewa akwai qullin daadar himu da kuma furera a ciki da suka sake tunzura komai,don kuwa bappan mutum ne mai sanin ya kamata,sannan ta yaya zaa rabani da maimunatu kuma abar mu’amalar dake tsakanin furera da daadar himu?,bayan duka gida daya ne,abu daya ne?,duk da furera ta cikasu da labaran qarya na cewa babu abinda ya hadata da shatun illa aikin bauta data dauketa,mutuwar shatu sai furera ta sake sakankancewa,ta mallake dukka dabbobin shatu da maimunatu suka zama nata,maimunatu bata tashi a komai ba illa me aikin bauta,ta riqeta wani irin riqo na qunci da kuma wahala,dole inaji ina gani na dauke idanuna daga kan maimunatun,nayi kamar bansan tana raye ba,saidai ban fasa mata addu’a ba da nema mata sasauci”

“Yanzu ‘yan wadan nan abubuwan sune suka zama hujja da kuma dalilin da ake qyamatar yarinyar bayan cikin abun babu wani abu guda daya data aikata?”

“Sune anni” kada kai kawai anni keyi,wani abu ya tsaye mata a zuciyarta me taba rai,tana kwatanta yuuma da maimunatu,inda an samu sakaci ko wani abu makamancin hakan haka zai iya faruwa da yuuma kenan sanda tana qarama,duk da ita tana gaban mahaifinta ne cikin soyayya da kulawa a sannan?.

“Wannan duka ba hujja bace,zallar jahilci ne da kuma son zuciya,kuma tabbas sai Allah ya yiwa yarinyar sakayya,zan dauke maimunatu daga wannan garin don bata cancanci zama a nan ba,maraya?,maraya wasa ne?,daka taba maraya hawayensa guda daya tak ya diga a qasa saboda kai,gwara ka rasa dukkan abinda ka mallaka ciki harda lafiyarka,kukan maraya masifa ne bare a sakashi a damuwa” yalwataccen murmushi ne ya bayyana fuskar yuuma

“Da nafi kowa jin dadin hakan anni,tabbas zanfi kowa murna”

“Kafin na wuce zan karba maimunatu zan wuce da ita,in sha Allah qarshen kukanta yazo,lallai mahaifiyarta macace mai nagarta,nagartar da nake jin yaqini da tabbcin akwaita tattare da maimunatu,tunda dukkan alamu sun bayyana”

“Amma anni wani hanzari ba gudu ba…..anya kinyi duba da tarin banbanci da tazarar dake tsakanin ja’afar da maimunatu kuwa?,shirinki me yuwuwa ne?” Tambayar dake rai da zuciyar laila kenan,labarin ya dauki hankalinta cike da mamaki da kuma al’ajabi,zuciyarta kuma ta narke matuqa da tausayin maimunatu

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button