GURBIN IDO

GURBIN IDO 13

Dan gayu ne na gasken gaske,gayu wanda ake kira gayu bawai muna gayu ba,mai tsananin tsafta ne daya tsani qazanta dama qazami,yana da tsari da kuma dokoki da ya sanya ba kowa ke iya mu’amala dashi ba,kamar yadda shima bada kowa yake iya mu’amala ba.

Miskili ne ajin farko,irin miskilancin da zakayi tunani bebe ne ko kuma kurma,magana ko hira bata daga cikin abubuwan dake burgeshi,abu ne mai wuya ka zauna dashi kaji wata doguwar magana a bakinsa,sau tari yafi ganewa amfani da body language,kamar wani me ciwon baki ko kuma mara lafiya,yana da tsananin kamewa da kuma tsare gida,akwai jinin sarauta sosai cikin jikinsa,hakan ya sanya yake da izza da kuma rashin daukan raini,bai yarda da qasqanci ba,yana da neman na kansa sosai,mahaifiyarsa diya ce ga turakin akko,yana da matuqar girmama na gaba dashi,komai qanqantar shekarun daka bashi,duk da mutane da yawa sun masa shaidar wulaqanci da kuma girman kai.

Mutum ne mai tsanani ta fannin so ko qi,bai iya so ba,hakanan bai iya qiyayya ba,idan jininku bai hadu ba ka fita a hanyarsa kawai shi yafi maka alkhairi,yana tsananin son mahaifiyarsa fiye da kowacce halitta a duniya,mahaifinsa da kuma anninsa suke da gurbi na biyu,don yakan kasa tantance cikinsu wa yafi so?,sannan gwaggwo sadiya qanwa ga anni,akwai mutanen da yake ganin kima sosai cikin rayuwarsa da zamantakewarsa.

Jabir shine qawa kuma amini ga ja’afar,d’a ne ga qanin mahaifin ja’afar,mahaifiyarsa ta rasu ta barshi sanda ta haifeshi ko juyawa taga abinda ta haifa bata yi ba,akwai aminci sosai tsakaninta da mahaifiyar jaafar,kuma rana daya aka haifesu,don haka ta dauka jabir ta hada jaafar ta riqesu gaba daya,duk da taso qwarai ta shayar dashi kamar yadda ta shayar da jaafar amma anni ta hana,tace tayi haquri,yasha madara,saboda gudun samun matsala anan gaba,idan hakan ta faru zata haramta masa duk wata ‘ya da ita din zata haifa jaafar yace yanaso,ko kuma wata daga cikin ‘ya’yan ‘yan uwanta,ba’asan kuma me Allah zaiyi ba,dukkansu sun gamsu sun kuma fahimta,taci gaba da bashi madarar,madarar kuma ta amsheshi sosai,ya tashi tubarkall,dashi da jaafar me shan nono babu bambamci,sun tashi tamkar ‘yan biyu,don haka ma ake ce musu,akwai matuqar shaquwa da fahimtar juna a tsakaninsu,kowannensu bashi da kamar dan uwansa,dashi yake shawara,shi yake gayawa sirrinsa.

Farinjinin ja’afar ya sanya yake da tarin ‘yammata dake hauka a kanshi,saidai ko sau daya bai taba sha’awar bata lokacinsa akan kowacce yarinya ba,a haka kwarjininsa ya sanya mata da yawa sun hadiye kwadayinsu,don basa iya tunkararsa da zancan soyayya kansu tsaye,masu tsaurin idanu ke biyo ta hannun jabir,to shima jabir din yasan waye ja’afar,kuma dabi’un nasu suna dan kamanceceniya,duk da jabir bashi da miskilanci,saidai yana ararsa a duk sanda yaso,hakan yasa sau tari wasunsu baya ko gayawa ja’afar ma yake barin batun yabi iska.

A sannan babban burin ja’afar a duniya shine ya zama pilot,dukka hankali nutsuwa da kuma rayuwarsa ya tattarata ne kan karatunsa gaba daya,sanda yake gab da zama pilot,a lokacin da suke komawa gida hutu daga qasar da yake karatu,a filin jirgin sama shaheeda ta fara ganinsa,d’iya ga shugaban malamai na qasa gaba daya,kuma babban limamin masallacin shugaban qasa dake abuja,yarinyar data bala’in mato masa,saidai tasirin tarbiyya data samu ya hanata bayyana masa,tana da kunya da kuma tsananin kamun kai,amma duk da haka ta kasa kanta sakat,sai data gano waye ja’afar din.

Ta shiga tsananin tashin hankali sanda aka gama karanto mata waye ja’afar?,ta yaya zata shawo kansa?,da wannan tunanin ta dinga rayuwa,haka ta dinga ramewa.

Kwanaki qalilan da ya rage musu su koma gida daga hutunsu suka giwa dr marwan rakiya abuja shi da jabir zuwa taron musabaqa na kasa da ake gudanarwa acan,a ture yaje bawai don yana so ba,don bai shirya zuwan ba.

Cikin hall din kansa yana qasa yanata danne danne a wayarsa,yana jin jabir sunata hira da wasu matasa biyu da suka hadu a can,har zuwa sanda aka fara gabatar da musabaqar,bai daga kansa ko sau daya ba,saidai duk wanda yahau zaiyi karatu har ya sauka yana bibiyarsa a zuciyarsa,yana taya alqalan cin gyaransu,don shima Allah ya bashi haddar qur’ani izifi arba’in cif,sauran kuma biye ne da qur’ani.

Kiran sunan wata daliba da akayi yaji daya daga cikin abokan hirar jabir din yace

“Alhamdlh……ga sister dita din” baiyi niyyar dago da kansa ba,amma jin ana sake maimaita kiran sunanta ganin bata fito ba,sabanin sauran dalibai da kowa ake kiransa sau daya…..shi ya sanyashi daga kansa sanda yaji me kiran sunan ya ajjiye abun maganar alamun ta taso.

Daga rukunin kujerin dake opposite dinsu ta taso,sanye cikin yalwataccen dogon hijabi har qasa,qafarta da hannunta duka safar hannu ne,baka ganin komai nata sai kyakkyawar fuskarta wanda nutsuwa ke kwance samanta.

Kansa ya dauke ya maida ga wayarsa,amma sai ya samu kansa da dakon jin nata karatun,ta daidaita zamanta aka tambayeta wacce qira’a take amfani da ita,ta fada,mai jan karatun ya janyo mata sannan aka bata damar ci gaba.

Gaba daya hall din sai daya dauki shuru sanda tayi bismillah,zazzaqar muryarta ta karade hall din cikin kyakkyawan sauti da qira’a,wanda tunda aka fara ba’ayi mata gyara har ta dire,kabarbarin mutane da yawa data burge suka dinga fitowa daga bakunan jama’a

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button