BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 52

Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

52

……….Sake maido da ita yayi da riƙo fuskarta cikin hanunsa da ɗage gira sama. “Faɗi abinda ke ranki mana yarinya. Koba angon bane?”.
      “Kaima kasan bashi ɗin bane ba, dan auren wata uku ne, kamar yau ne zai ƙare”.
   “Oh really?”.
Cike da confidence ta bashi amsa. “Ka rubuta ka ajiye”.
        Wani ƙayataccen murmushi daya nema sumar da ita ya saki, yaja hancinta da kashe mata ido ɗaya har sannan murmushin bai bar fuskarsa ba. “Kin tabbatar zaki iya?”.
     Da ƙyar ta iya jawo yawu mai kauri ta jiƙa bushashshen maƙoshinta tana ƙyaƙyƙyafta ido. “Babu tantama a alwashina Yaya MM”.
          Juyata yay suka koma tsakkiyar gadon, ta koma ƙasa shi kuma ya dawo samanta. ƙara ta saki da ƙoƙarin son turesa sai dai ko gezau, ta fara jan numfashi da fesarwa da ƙyar dan gaba ɗaya ya sakar mata nauyinsa dan mugunta. Ɗan ɗagata yay sai dai ba duka ba, ya kalla cikin tsakkiyar idanunta da har sun canja launin farinsu zuwa ja harda tara ƴan ƙwalla. Murmushi ya kuma saki da shafa lips ɗinta kaɗan da yatsun hanunsa. Ya ɗan kashe mata ido ɗaya da kai bakinsa saitin kunenta ya fara magana kamar mai raɗan. “Wannan bakin naki ne zai kaiki ya baroki yarinya. Idan kikace zaki buga game ɗin nan dani zubar hawaye bata shirya barin idaniyarkiba kenan….”
    Janye fuskarta tayi saboda wani zirrr da takeji a cikin jikinta. Cike da tsiwa da son hana ganin lagonta ta sake maido fuskar “Never for ever, ka rubuta ka ajiye Yaya nanda wata uku zamu koma gaban Baba Ibrahim da kai ka bani sakina, dan ni da kai bazamu taɓa son juna ba, kaima kasan da haka ai”. Itama ta ƙare maganar da salon kashe masa idanu daya nema ɗauke masa numfashi.
     Jin zata zille yay azamar tareta da hannunsa, gaba ɗaya annurin fuskarsa ya gushe, cikin ɗan kausasa harshe da zuba mata idanunsa da launinsu ya canja tsakkiyar nata ya fara magana. “Kuma dole ki zauna da ni yarinya, zan kuma tabbatar miki da hakan ki rubuta ki ajiye”.
            Alwashin nasa ya matuƙar tsaya mata a rai, amma sai ta basar cike da rainin wayo ta saki siririyar dariyar data saka tsigar jikinsa tashi. “Yaya MM kana wasa da wannan Anaam ɗin, amma dai muje zuwa, hausawa kance ba’a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare, nanda cikar wata uku zan tuna maka wannan”.
      “Ni kuma kafin cikar wata ukun zan maimaita miki”. Ya faɗa yana janye jikinsa a nata ya sauka a gadon baki ɗaya. Harara ta dallama bayansa zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, harda sakin ɓoyayyar ajiyar zuciya. Ita kanta ta yabama kanta da kanta, dan tasan ba ƙaramin dauriya taiba na riƙe tsoronta. Sai da taga ya fice a ɗakin gaba ɗaya ta dafe ƙirji da rumtse ido. Sai kuma ta buɗe da ɗan mangarin kanta. “Stupid girl! Anaam kina da hankali kuwa?. Wayyo ni ALLAH miya kaini yin waɗan nan cika bakin yanzu idan yaƙi sakin fa?” (Sai ki kaisa kotu) zuciyarya ta bata amsa kai tsaye. (Ya zakiyi da su Abie kuma?) wani gefen ya tambayeta. “Shike nan na mutu” ta faɗa a fili tana sake dafe kanta. Ganin zata zarar da kanta sai ta miƙe cikin murguɗa baki da faɗin, “Koma miye bazan yarda yaci galaba a kaina ba. Kafinma wata uku nayi gaba abina”.

    ????To bara muga yaya wasan zai kaya ƴar mitsila????.

        ★★★

   Duk yanda taso danne zuciyarta yau ta musu breakfast kasawa tai, koda maman Abu kuma tace zatayi saita hanata. Kallo ɗaya zakai mata ka fahimci taci kuka sosai dan idanunta har sun nuna. Tun tana kallon agogo da tsumayen shigowar Shareff harta daina zuciyarta na cigaba da mata zafi da raɗaɗi. Da alama ya fita ko sallama bai mataba kenan dan yanzu dai lokacin zuwa office ya gota matuƙa, ta kuma tabbatar bazai zauna har zuwa yanzun bai fitaba dan bai haɗa aikinsa da komai ba. Zuwa yanzu ta yarda kuka rahama ne, dan jiya tayi kuma taji sauƙi da sassaucin zuciyarta. Amma yanzu ya gagara fita ko kaɗanne balle taji sauƙi. Wani irin tsanarsa da haushinsa takeji mara misaltuwa, zuciyarta kuma ta kasa tsayawa waje guda da tunanin abu biyu. Shin maganin su Aunty Malika ne baiyi aiki a kansa ba? Kokuwa dai asirin dasu Gwaggo suka jima suna faɗa iyayen yarinyar nan nayine yafi nasu ƙarfi. Kanta ya kulle, ta rasa ina zata kama. Zafafan hawayen da taketa son fitarsu suka sami damar silalowa saman kumatunta masu matuƙar zafi, daga haka kuka mai cin rai ya kufce mata har ya shigo bata sani ba.. Ƙamshin turarensa dake ƙara yawaita a ɗakin da hancintane ya sakata ɗagowa kaɗan ta dubi ƙofar. Tsaye yake cikin ƙananun kaya masu taushi da sukai matuƙar fidda ƙuruciyarsa ta matashin namiji alamar yau bai fita ko’ina ba kamar yanda tai hasashe. Wani irin damm zuciyarta ta bada sauti a cikin ƙirjinta, abinda zai hana Shareff fita office kam lallai ba ƙarami bane, hawaye ne suka sake ziraro mata, ta sake ɗago ido ta kallesa har yanzu yana a ƙofar tsaye hannayensa duka a cikin aljihun wandonsa idanunsa a kanta tamkar ya samu television. Sakkowa tai a gadon da gudu taje ta rungumesa. Murmushi ya saki mai faɗi, tare da zare hannayensa daga cikin aljihu shima ya rungumeta. Ta saki ajiyar zuciya da sake kanƙamesa. Kusan mintuna uku suna a haka tsaye kafin ya ɗagota, fuskarta ya rike a tafukan hannayensa yana raba idanu akan hawayenta, ya girgiza mata kansa yana binta da wani kallon ƙasa-ƙasa.
      “Kukan bai isaba?”.
   Ya faɗa idanunsa cikin nata.
Kasa jure kallon nasa tai dan tamkar yana zuba mata wasu maganaɗisune masu wahalar ja’inja. Tai ƙoƙarin maida idanun nata ƙasa amma ya hana hakan ta hanyar ɗora lips nashi kan nata. A tare suka lumshe ido. light kiss ya sakar mata. Taja numfashi da ƙyar da ajiyar zuciya mai ƙarfi.
      Murmushi ya saki da kai goshinsa saman nata ya haɗe, “Kin huce ko?”.
Baki ta tura masa zata kautar da kan nata ya hana hakan. Dole ta haƙura ta tsaya tanata sauke ajiyar zuciya a jere. Sai da ya tabbatar ta nutsu sannan ya saketa suka koma bakin gado. tissue ya miƙa mata, babu musu ta amsa ta share hawayenta.
    “Kin tashi lafiya?”.
“Alhmdllh”.
Ta faɗa a taƙaice. Shiru ɗakin ya ɗauka kamar wasu baƙin juna. Taso ta danne komai kamar yanda taga ya basar, sai dai bazata iyaba. Ta ɗan dubesa muryarta na rawa. “Yau bazakaje office ba ne?”.
      Bai iya ɓoye magana ba ko kwana-kwana, dan haka kai tsaye ya bata amsa da “Haba dai Madam, ango a office ai a koro ni. Ko ke ɗin nan ai baƙya so ganina a can ba ko. Ina hutu ne sai monday insha ALLAH”.
           Ido ta tsura masa ko ƙyaftawa babu, “Sati ɗaya fa kenan?”.
    “Kinga sun ragemin mudu ba kamar lokacin naki amarcinba ko? Nima dai inajin kamar zanyi bore na ƙara wani satin akan wannan na more angwancina da kyau, amma bani shawara kar ace na cika son bati”.
         Da yasan yanda zancensa ke ƙona zuciyarta da bai cigaba da yinsa ba. Ta janye idanunta dake cikowa da ƙwalla a kansa tana jan numfashi da haɗiye abinda ya tokare maƙoshinta da ƙyar.
      “Babie kinyi shiru?”.
Kanta ta girgiza masa hawaye na sakkowa a kumatunta. Ta miƙe batare data bari ya gani ba, toilet ta nufa tana faɗin, “Wannan ai maganar amarya ce ba tawaba ita ya kamata ka samu kaga ko wata guda saiku je a ƙara muku”.
     Ƙofar toilet ɗin data bugo da ɗan ƙarfi ya tsurama ido, zuciyarsa na jujjuya maganar tata da son bata fassara. Ganin zai takura kansa akan son fahinta sai kawai ya ɗage kafaɗu da ɗan taɓe bakinsa. Shiru-shiru taƙi fitowa har kusan mintuna biyar, ya kalla agogon dake ɗaure a hanunsa tare da kai dubansa ga ƙofar toilet ɗin da mamaki. “Wai nikam mi kike a toilet ɗin nan haka kizo ki bamu breakfast”.
     Shiru babu alamar zata amsa masa balle fitowar tata. Ya sake maimaita maganar sai dai anan ɗin ma babu alamar motsinta. Miƙewa yay zuwa ga ƙofar cikin ɗan tunzura ya bubbuga. “Wai kina jina inata magana kikai min banza?”.
         Nan ma yitai kamar zata sharesa sai kuma ta buɗe, ganinta ɗaure da toilet ya sashi faɗin, “Wai dan walaƙanci dama wanka kika shiga kika barni anan?”.
     “Toni ai ban san zaka tsaya jirana bane kayi haƙuri”.
Ta faɗa cikin son yanƙwala shi tana nufar mirror. Da kallo ya bita kawai. Sai kuma ta ɗan juyo ta kallesa. “Kana buƙatar wani abu ne?”.
     Bai tanka mata ba, bai kuma janye idanunsa akanta ba, sai dai haka kawai zuciyarsa ta sosu da yanda take masan. Idanunsa ya ɗauke kawai da nufar ƙofa ya fice abinsa… Ta raka bayansa da harara cikin taɓe baki.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button