FARHATAL-QALB

FARHATAL-QALB 15

PG:15

××××
 
“Okay Maaa…!” Ya amsa ta cikin nutsuwa da tantsar biyayya.

Har dinning area din ta raka shi. Yana gaba tana biye da shi a baya suka zauna akan kujeru.

“Tea or coffee…?”

“Coffee literally…”

“Tam…. ” Wajen coffee maker ta isa dake jone ajin bango. Dake dinning area din kawatacce ne daya ji kaya ya koshi.

Nan da nan cikin kankanin cokali ta hada ta miqa masa. Ta bubbude warmers din da abincin ke cike. Niimataccen kamshin abincin ya gauraye ko’ina.

“Plantain, chips. Doya. Ko yamballs? Ga shredded beef sauce kuma nan da kunu. Nan kuma kosai ne sai wainar kwai.”

Dan tsayawa yai yana duban abincin data bubbude murafen su kafin ya girgiza kai kawai.

“Ai kawai Maa bari na sha kununnan ya isa.”

“Bangane ba. Kasan sarai kuma dan kai akayi wadannan abubuwan tunda ba cin abincin masu aiki kake ba tun safe nake aikin soye soye .”

“Afuwan Maa ” Ya fada ahankali kawai yana sauke numfashi

“Meya faru ne? Naga kaman akwai abunda yake damun ka.”

“Bakomai Maa.”

“Ai kai taurin kan ka ne yake kara maka ciwo. Kaji da shi “

“Zanci. Aban plantain da soyayyan kwan kawai “

Zuba masa tayi ta tura masa da plate din gaban sa.

“Kullum tamkar wani karamun yaro sai an tsaya akan ka kake cin abinci.”

Murmushi kawai yayi. Ya dauki fork yana ci ahankali.

“Nagode Maa. Komai yayi dadi “

“Madalla. …”

Bai sake cewa komai ba. Ya shiga ci ahankali har ya karasa cinyewa.

“Alhamdulillah…Wai ina su Nassem ne?”

“Suna bacci mana, Anjima kadan zaka gan su. Nadra kuma tana wajen su Jannat. “

“Oh okay. Ni dai ince duk yau banji motsin su ba. “

“Uhm..”

“Bari na tashi zan dan biya site ne.”

“Okay Madallah, Allah ya temaka.”

“Aamin Yaa Rabbi Maa. “

Tashi yayi ya maida kujerar cikin dinning table din, Sannan ya fice daga cikin sashen bayan ya saci kallon Umma Hadiza da ke shanya dusters ajikin abun shanya.

“Sannu da aiki Hadiza “

“Yauwa sannu Hajia. Na kammala wadan nan akwai wasu aiyukan da zaa tayaki dashi?”

“A’ah sai zuwa anjima. Har yanzu dai ba zaki karba abincin kici ba ko?”

“Allah Hajia a koshe nake. Sai da muka ci yar tsala tukun sannan na taho.”

“Ai shikenan, Kyaci anjima. Dawo parlor ki zauna. “

A tare suka fita daga cikin kitchen din zuwa parlor. Hajia ta zauna akan kujera Umma Hadiza kuma ta nemi gefe ta zauna.

“Wannan da ya fita shine babban ‘da na fa.”

“Ah haba dai? Allah sarki “

“Wallahi shine , Muna kiran sa da Zayn. Sai Nadra  wadda suka kare makaranta a kasar waje inda mukaje.Ita da su  yayyanta yayan wajen kishiyata. “

“Masha Allah. Allah ya raya su. Ya biya bukatu na alkhairi “

“Aamin Hadiza. Bayan Nassem sai Moha, Muhammad kenan, Ita Kuma Nadra ita kadai ce ‘yata mace ce. Su kumaa mazan su 3. Ai Ina tunanin tamkar ma ma gaya miki zuwan da kukayi ko?”

“Tabbas kin fadi haka Hajia. Allah ya raya su ya musu albarka Amin…”

“Aamin Yaa rabbi.”

“Jira nake 11 ta cika na je asibiti inada wata tiyata 12:30,”

“Allah ya kai mu yasa ayi lapia Hajia . Amin”

“Amin Hadiza “

Suna zaune Nadra ta dawo daga sashen su Jannat . Malami ne yake zuwa ya koya musu karatu .

“Maaa “

“Naam Nadra “

“Ah ina kwana?” Ta dan rissina ta gayda Umma Hadiza.

“Mun kwan kalau? “

“Alhamdulillah.”

“Itace ‘yata macen da nake gaya miki Nadra … Dake kafin zuwan ki tatafi can sashen shiyasa baku hadu ba. “

“Allah sarki. Ai kuwa dai ga kamar nan masha Allah. “

“Okay itace wadda kike fada mana ko Maa?”

“Yes ita ce.”

“Yunwa…”

“Kije kitchen an kai tun dazu. Amma sai kinyi reheating . Idan kuma na Zayn kike so yana dinning “

“Ah bari naci namun. Abincin akhi sai shi.”

Dariya suka sanya baki daya. Nadra ta dubi Umma Hadiza ta shiga cewa.

“Allah shi abincin sa ba yaji kwata kwata, Kuma yana son spices over. Shi fa kullum abinci sai Maa ta masa da kanta yake ci. Idan aka dafa bayacin girkin wani. Sannan ko eateries ba zeje ya saya yaci ba. Ko anyi ordering bayaso. Kullum home cook. Abincin ma wanda Maa tayi. “

Umma Hadiza tayi daria .

“Allah sarki bawan Allah, ..”

“Ke Nadra. Je ki kwankwasawa Nassem baccin ya isa haka nan.”

“Harda Moha?”

“A’a shi kyale shi “

“Autan ne Moha ko?”

“Eh shine. Ai kinji tace a kyale shi. Dangware shalele ne ai.”

Suka sake sakin dariya. Kafin daga bisani Nadra ta miqe ta nufi wani daki dake kasan kafar bene. Ta shiga knocking kofar.

“Nassem.!!! Nasseem!! Nassem!!”

“Naam…” Ya amsa ta cikin muryar bacci

“Ka tashi inji Maa.”

“Tohhh. ” Ya sake kundundunewa da bargo zai koma baccin kawai ta murda kofar ta shiga kanta tsaye bayan ta saki katuwar sallama

“Oh please ….”

“Ba wani please. Dalla ka tashi inji Maa.” Ta kunna wutar dakin.

Ya yamitsa fuska yana mai jujjuya kansa.

“Na ji…”

Ta tsaya kyam a kànsa har sai daya gaji ya miqe ya shige bandaki bayan yayi sallama. Sai da taga ya tashin dagaske tukun tatafi kitchen. Nan da nan ta zuba abincin ta ta koma kan dinning bayan ta hada shayi mai kauri.

Ba jimawa sosai Nassem ya fito daga dakin sa. Sanye cikin jallabiya fara. Gashin kansa a kanannade. Kamar su daya da Zayn.

“Ina kwana?” Ya gayda Umma Hadiza yana rufe bakinsa da tafun hannu. Sakamakon hammar data taho masa,

“Alhamdulillah….”

“Shine Nassem din.”

“Allah sarki…” Cewar Umma Hadiza. Tana dan kare masa kallo tamkar shine na wajen nan da suka ci karo da Waheedah .

“Ai kamar shine suka yi gware da yarinyata a waje ko dazu da sassafe.”

“Nasseem? Anya kuwa shine. Saboda tun sallar asubah da suka dawo daga masallaci cikin gidah kawai yayo. Dan masallacin ma anan gidan yake. Ina ga dai cikin yan uwansa ne. “

“Maybe Akhi ne… Ya Zayn.”

“Oh eh… Yayan su kika gani tabbas, Wanda yazo yaci abinci dazu. Kamar su daya da Nassem din.”

“Allah sarki. Sai da kika fada na gano.”

“Yarinyar ki makaranta take zuwa anan unguwar……….????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button