GURBIN IDO 41-45

“To in sha Allahu” tabawa ta fada tana yunqurawa ta wuce dakinta ta shirya,driver ya dauketa,kafin ta wuce sai data biya wajen amma ta gaya mata abinda ke faruwan,irin tunanin da ya darsu a ranta shine ya darsu a ran amman,farinciki sosai taji ya.mamayeta,tana qaunar ja’afar can qasan ranta,tana kuma qaunar duk wani abu daya danganceshi,tana boyewa ne saboda ‘yan uwansa da kuma idanun mutane,tana da kara da alkunya irin wanda asalin bafulatanin mutum ke dashi.
Sanda ta isa asibitin suna gaisawa ya fice a dakin,sai daya dan kalleta ta gefan idanu kafin fitar tashi,bacci take lakadan,sai ya taka a hankali yabar dakin,yana kiran waya yaji an kawo masa motar da yace a kawo masan.
Sai da baba tabawa ta fidda mata hijabin jikin nata ta sake gyara mata kwanciya yadda zataji dadi kana ta zauna dab da ita kamar me gadinta,itama tana cikin masoya maimunatu,wadda Allah ya dora mata qaunar yarinyar har cikin ranta.
Bayan la'asar kadan ya shiga gidan,main parlor din babu kowa,hakanan shuru yake sai na'urori daketa aikinsu,sama ya wuce kai tsaye,ya sanya key ya bude qofar dakin nasa kana ya tura yana furzar da iska daga bakinsa,da daya da daya yake duban dakin,yau dakin ya masa shirgi da yawa,baa kintse yake yadda yakeso ba,duk sai yaji ransa ya jagule,mutum ne shi da baya qaunar datti ko qanqani,don haka ya zare tie dinsa ya kuma soma fidda suit din jikinsa,ya zamana daga shi sai farar qal din singlet dinsa ta zallar auduga dake fidda wani sihirtaccen qamshi,a hankali ya fara picking duk abubuwan dake zube a qasa, yana kintsa dakin.
Sam wannan ba rayuwarsa bace,dole ya koyeta,baya son kowa ya shigar masa daki,sai daya dauki good five thirty minutes sannan ya samu dakin ya masa yadda yakeso,bawai don ya gama qalqaleshi yadda ya kamata ba,yadda jikinsa yayi masa week yasa ya zame a gefan gadonsa ya kwanta,yana runtse idanunsa yana miqewa sambal,wanda tsahonsa gaba daya ya kusa cinye tsahon gadon,abinda zai tabbatar maka da baiwar tsahon da yake da ita kenan.
Yadda shuru ya ratsa dakin haka yaji kwanyarsa ta dauki shurun,a hankali abinda ya faru dazun ya gifta cikin idanunsa,yadda ta tsorata sosai sanda hon dinsa yakai kunnuwanta,idanunta suka fidda wani kalar tsoro da ya sanyata durqushewa a wajen
“Astagfirullah” ya fada yana maida folding hannayensa a qirjinsa,yana jin ba dadi har cikin ransa,tausayinta ya ratsashi,a sannan baisan zazzabi ne a tare da ita ba,da bai matsa mata hon din ba.
Tun asalinsa mutum ne mai tausayi da kuma son kyautatawa kowa,duk da zallar miskilancinsa ya boye hakan,mutane da dama suna masa kallon bahagon mutum mai zallar rashin son jama'a da mugun hali,musamman wadanda basu mu'amalanceshi na tsahon lokaci ba.
Haka yayiya kokawa da kwanyarsa da kuma tarin tunane tunanen da take saqa masa,tsahon wasu mintuna kafin a sannu a hankali bacci yazo yayi awon gaba dashi.
A hankali take takowa zuwa uwar dakin nasa,gabanta yana dukan uku uku,tana kuma warning daya yanka mata sati guda baya daya wuce,saidai zuciyarta ta kasa jurewa,bata samu komai daga gareshi ba sannan kuma ace ganinsa yana gagararta alhalin suna zaune a gida daya,amma idan batayi da gaske ba sai ta shafe sati bata sanyashi a idanunta ba.
Da wata nutsuwa data aro ta murza handle din sannan ta tura qofar dakin,idanunta ya sauka a kanshi sanda yake baccinsa very calmly kamar babu wani abu da yake damunsa cikin duniya,idanunta a kansa ba tare data iya daukewa ba taci gaba da takawa,duk takun da zatayi zuwa inda yake bugun zuciyarta ne yake daduwa,yayin da fuskarsan nan dake dauke da wani sassanyan kyau da kuma kwarjini na musamman wanda bai gushe ba koda ckin bacci ne take sake kusantowa gareta.
Dab dashi ta isa,sannan ta zauna gefan qafarsa a hankali idanunta na sauka kan sambala sambalan qafafunsa,kai kace baya taka qasa dash,fari qal sai lallausan gashin da ya yiwa yatsunsa ado,ya kuma kwanta luf a singalalin qafarsa,hannu takai kamar zata shafo sai kuma ta janye hannunta da sauri,ta maida dubanta ga fuskarsa,zaman da tayi yadan kare mata fuskar tasa,don haka sai ta sake miqewa tayi tsaye a kansa tana morewa kallonsa,kallon data tabbatar inda idanunsa biyu bata isa ta yishi ba,wani irin sonsa ke kwarara a ranta,takai hannuna hankali zata shafi kwantaccen sajen dake gefe da gefan fuskarsa
“Don’t touch me” ya furta cikin kaushi cikin muryar mutumin dake bacci,sosai ta tsorata,ta janye hannunta da sauri tana fiddo idanu waje,dai dai lokacin da shima ya fara bude idanun nasa da kadan da kadan har ya zubesu fes kan fuskar unaisa.
Kafeta yayi da idanu wani zallar bacin rai yana saukar masa,wannan shine karo na kusan biyar da take masa hakan,kamar bazai motsa ba sai daga bisani ya miqe daga kwanciyar a hankali,cikin zuciyarsa yana karanto addu'a,saman gadon ya zauna sosai bayan ya zubo da qafafunsa qasan gadon
“Me kikemin a daki?” Ya tambayeta kai tsaye,sosai tayi qoqarin sanyawa kanta dakiya,duk da yadda jiki da kuma muryarta suke dan shaking kadan
“Zuwa nayi na duba dawowarka,ga abinci can a gama” shuru yayi na second uku
“How many times nake gaya miki ba kowanne jagwalgwalon masu aiki da sunan abinci nake ci ba?,take note please,kada ki sake shigomin daki ba tare da izini na ba” ranta ya sosu kamar kullum,ta kuma kasa hadiyewa
“Amma dai kasan ni matarka ce ko?,sannan kuma ko yaya ne ina da hakki a kanka” qas yayi da kansa,murmushi nason kubce masa amma kuma ya hana kansa faruwar hakan,don baya son raini,daga bisani ya kuma daga kan nasa ya dubeta kai tsaye
“I know,i already know, that’s why na baki zabi ai tuntuni,a mutunce zan baki takardarki ki qara wuta,i assure you zaki samu dai dai dake” wani qullutun baqinciki ne ya tokare mata wuya,wanda ta kasa riqeshi,sai ta saki kuka kawai ta juya gudu gudu sauri sauri tabar dakin,yayin da shi kuma ya bi bayanta da wani kallo da tsarabar tsaki,kana ya miqe a hankali yana sanya hannunsa cikin sumarsa yana maidata baya saboda yadda ta cakude,bawai bashi da feelings ba,ko kuma feelings dinsa ya mutu ba,aah…..yana nan a yadda yake,lafiyayyen namiji,wanda wannan dalilin ya sanya ko a baya ya riga jabir aure,amma dai for now bayajin komai akan kowacce diya mace,musamman unaisar da sai a yanzu yake gano fuskarta ranar da qaddara ta fara hadasu da ita a wani club sanda yake aviation school,zuwansa club na farko kenan a rayuwarsa,shima baisan can zasuje ba,daga wajen cin abinci suke shida abokinsa kuma abokin karatunsa muslim,yace yazo ya rakashi wajen wani abokinsa,as’ad zubair,dan gida wani babbban qusan gwamnati a nijeria,acan ya gansu tare da ita,wanda shikam kallo daya ya yiwa fuskarta ya dauke kai,abinda yasa ya kasa shaida fuskarta kenan da wurwuri sai daga baya,duk da ba shigar banza ko wani abu yaga tana sha ba amma abun ya tsaye masa a rai,don yana da tabbacin cikakkiyar mace mai cikakkiyar kunya ilimin addini da tarbiyya ba zaa sameta a wannan wajen ba.
Ruwa mai dumi sosai ya sakarwa kansa,bayan ya gama yayi brush ya feshe bakinsa da turaren mouth mint mai qamshin strawberry,ya dauki babban towel yana tsane jikinsa daya jiqe da lema sosai saboda yawaj gargasar da yake da ita saman lafiyayyar fatarsa.
Cikin wasu lafiyayyun kaftan ya shirya kansa farare qal,duk motsin da zaiyi jikinsa na fidda wani irin qamshi mai taushi,ba kasafai ya fiya sanya hula ba,don haka ya riqeta a hannu bayan ya laluba key din motar da yake son fita da ita,ya kalli agogo yana duba lokaci,sai ya sanya wayoyinsa a aljihu bayan yayi kiran daya daga cikin drivers dinsa yaji yana kusa don qyuyar tuqi yakeji,har yanzu kasalar bata sakeshi ba,yayo waje cikin takunsan nan dake dauke da wani salo na dabam da zaka tsammaci tsabar jin kai ne ko izza.
Sai da suka tsaya sukayi sallar magariba da isha'i a hanya sannan suka qarasa a asibitin,a sannan har yayi waya an musu take away na abinci awa daya kafin ya isa,qarfe takwas da wasu motsi,driver yayi parking motar tasu,ya balle murfin motar ya ficw cikin nutsuwa,iskar asibitin tana kadashi,tana kuma tuna masa wasu abubuwa sa suka shude cikin rayuwarsa.
Babu yawan jama'a sosai a asibitin,hakan ya bashi damar isa qofar dakin kai tsaye,tun bai shiga ba ya tabbatar akwai mutane a ciki,sai ya tura qofan a nutse da sallama.
su hudu ne 'yammatan gidan nasu,sai baba tabawa ta biyar dinsu,sallamarsa ta sanya su duka yin dif,yayin da wuta ta daukewa maimunatu dake zaune ta jingine bayanta da filo tana sauraren hirar tasu,sanye take da doguwar rigar atamfa wadda ta zauna mata sosai a madaidaicin jikinta,ta kuma fidda mata shape dinta saboda yadda breast curve din aka yishi cif da cif,ya kuma zauna mata sosai,dogon hannu aka yiwa dinkin saidai an yayyanka shi ya koma kamar spaghetti sleeve,tayi tayi sanda ta sanya kayan a bata baby hijab dinta data saba sakawa amma fa'iza tace a'ah,su da su waye a dakin da sai ta sanya hijab,baba tabawa ma tace
“Ki barshi kawai maimunatu,kada kije ya dameki ma ya gotar miki da canola din” kasancewar sun cire mata ruwan da ake qara matan don ta huta.
A ladabce suka gaidashi bayan baba tabawa ta miqe ta bashi kujerar da take kai ta matsar da ita gaban gadon maimunatu,maimunatun da tunda ya shigo tayi qas da kanta,ko sau daya bata dago ba,idanunta nakan Canola din hannunta.
Takalmanta baba tabawa ta jawo tana sanyawa,dai dai sanda anni ke fitowa daga bandaki
“Yaushe ka shigo?” Da hannu ya nuna mata yanzu yanzu
“Zamu wuce,dama shirin tafiya muke”
“Akwai driver?” Ya tambaya a taqaice da muryarsan nan me cike da ginshira
“A’ah a’ah,salma ta tuqomu,gani nayi tafiyar babu yawa” cikin salma ya duri ruwa,ita anni me yasa ba’a sirri da ita?,kawai tace masa eh driver dinne,na meye saita bashi labari?.
Qarasa dibibicewa tayi sanda ya watsa mata wani kallo na gargadin kinyi na farko kinyi na qarshe,baa baau mota su tuqa a gidan,saidai idan kinyi aure mijinki ya baki,suk inda zasu driver ke kaisu
Da daya da daya suka fice a dakin suna yima maimunatu sallama tare da cewa zai gobe,murya can qasa take amsa musu,gabanta na wani irin faduwa,tana jin kamar tabi bayansu sanda suka fita,dakin ya rage daga ita saishi daya sanya waya a gaba yana dannawa
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 44
Ba wani qura sashen nata yayi sosai ba,saboda yanayin ginin gidan dama unguwar,amma duk da haka baba tabawa ta zage ta gyare mata sassan nata tas,ko ina ya dauki qamshi da qyalli,aikin da ada ita ke abunta duk sanda ta dawo hutu,abu nafarko data lura dashi,babu wani daki da maimunatun ta ware da sunan dakin maigidan,hakanan bataga wani abu ko guda daya daya danganceshi ba a sassan,koda agogo bare akai gasu hula,tsoronta daya kada dai ace fa yarinyar tana gefe suna rayuwarsu shida unaisa,kada suyi amfani da qanqantarta su cutar da ita,abinda bata sani ba duk kanwar ja ce,har gwara gwara maimunatun,yana tsayawa ya dubeta da idanunsa,yana mata kallon quruciya sometimes har yakanji abar tausayi ce a ransa (hmmmmm,ya manta duk qanqantar allura qarfe ce,mace babba da yarinya duk sunanta mace).
Baaba tabawan batace dai da ita komai ba,taci gaba da sanya ido a fakaice,har zuwa sanda ta gama kintsa ko ina,sanna ta dora musu abincin dare saboda yammaci sosai yayi,sun kuma yi 'yan ciye ciyensu kafin ta gama aikin,babu kuma mejin yunwa a cikinsu,duk da maimunatun taso ta barta tadan dafa musu koda jallop ce kafin baban ta gama aikin amma ta hanata.
Gab da magariban akayi knocking qofar falon,baba tabawa ta leqa,sai gata ta dawo tana gaya mata yaron gidanne da siyayyar kayan abinci,ta saba,kusan duk sanda ta dawo hutu zai aiko da cefane da kayan abinci a zuba mata a store,duk da ba rasa komai takeyi ba,hasalima kayan abincin kamar ba'a tabasu,saboda ita daya ce iya cikinta,ba kuma kasafai take wani girki ba,don idan tayi breakfast sai takai har rana bataji yunwa ba,bata sake dora girki sai na dare,ta riga data saba zama da yunwa,banda yanzun ma da cikinta yake komawa normal irin na mutane.
Baba tabawa ce ta bude masa can qofar baya ta kitchen din,ya shiga ya zuba komai ya fitar da wanda zai fidda kamar yadda aka saba,sai daya tafi ta kulle wajen sannan ta dawo
“Niko nace,kuna gaisawa kuwa da abokiyar zamankin nan?” Kanta maimunatu ta daga daga qoqarin jona chargy da take a wayarta
“Ina shiga duk sanda na dawo a makaranta mu gaisa na gaya mata na dawo”
“Amma duk xaman da kikayi asibiti ban ganta ba” ta tambaya cikin mamaki,don ko yanzun ma taji motsinta,sun kuma hadu da masu aikinta a kitchen din gidan,saidai babu wanda yace mata kanzail a cikinsu.
Shuru maimunatun tayi,don itama bata da amsar da zata ce,ta kuma fuskanci kusan ita kadai dince bata zo dubata ba,tasan kuma ta sani,koda mai gidan bai gaya mata ba sanda su laila sukazo daukar mata kayan sawa sun hadu,sun kuma gaya mata abinda ya kawosu,duk yadda taso kada taji babu dadi aka abun wannan karon sai dataji ranta ya sosu,ita din batasan ciwon kanta ba kenan da take shiga har sassanta duk randa ta dawo ta gaidata ta gaya mata ta dawo,badon komai ba sai don zaman lafiya dake da dadi,bawai rashin sanin ciwon kai bane,duk mutumin da zakayi ciwo ya kasa dubaka to lallai rashin qauna yakai iyaka,a take nan taji a cikin ranta itama tabar taka sassanta.
A nan waje ta watsar da batun,kamar yadda baba tabawa bata sake daga batun ba,ta wuce bedroom dinta tayi wanka,ta shirya cikin dinkin doguwar rigar atamfa A shape,ta dora baby hijab dinta saman kanta bayan tayi sallar magariba,tasha magungunanta sannan ta fito falon,tana ji a ranta zuwa yanzu wayarta ta cika da chargy.
Ta samu baba tabawa ta gama shirya musu abinci
“Na zuba sauran yana dumama don kada ya huce kafin yazo ci” baba tabawa tace da ita,sai ta amsa mata da to,ba tare data fuskanci ma’anar maganarta ba,tare suka zauna da ita sukaci abincin,suna ci suna hira,baba tabawa na bata labarai iri iri da suka shafi rayuwa,zamanta da kishiyoyinta da kuma mijinta,yadda mijin ke ji da ita saboda tafi duka sauran kula dashi,a fakaice take shigar mata da darasi.
Sosai take jin dadin labaran,tunda take tsahon watanni sai yau ne takejin gidan a matsayin gida,sai yau ta taba jin dadin zaman gidan,sun jima sosai suna hira,harta soma jin bacci yana fusgarta,don haka ta miqe ta bada faralin sallar isha'i,ta dubi baba idanuwanta na lumshewa
“Inajin akwai maganin dake sanya barci cikin magungunan da nasha”
“Bacci ko?” Kai ta gyada mata
“Eh wallahi,zan je na kwanta”
“To Allah ya tashemu lafiya” da kallo tabi maimunatu sanda take shigewa dakinta,tana jinjina kai tare da sake tabbatarwa kanta akwai matsala,bata ga ya shigo ba,bata ga taje nemansa ba,koda kuwa ba kwananta bane,tana kuma da tabbacin zuwa yanzu ai yana gida,don ba mai yawon dare bane shi tun asali,amna zatabi komai a sannu,koda yau da gobe ba kwananta bane,dole jibi ya zamanto kwananta,jinjina kai tayi tana ci gaba da kallonta,saidai kuma gefe guda na zuciyarta tana ayyana mata yadda zata tafi da komai.
******washegari ta kunna wayarta,ta kuma dauko number afra fatima da ayman ta sanya,tayi saving number kowa,sannan ta fara kiransu daya bayan daya,duk wadda ta kira sai ta yi mamaki,cike da murna da farincikin samun number aminiyar tasu,afrah ce a qarshe,don tasan dole sufi dadewa da juna akan kowa.
Da tsiya afra ta fara yi mata
“Kin yiwa kanki fada kenan?” Dariya maimunatu tayi
“Na gaji da kewarku ne” hira sosai suka sha da afrah din,har sai da katinta da hisham ya taba lodawa layin ya qare,afran ta biyota
“Ina fata kin fara shawo mana kai captain” dan shuru tayi tana son tuna waye captain,sai kuma tadan saki fuska
“Manta da wannan batun”
“Seriously you are doing wrong fa maimunatu,kina nufin a haka zaki yita zama,meye ma’anar auren kenan?”
“Karfa ki damu,ni dashi duka bamu damu ba”
“Amma kin sauke amanar anni da amma kamar yadda suka baki?” Tambayar da ta sanya maimunatun yin shuru kenan,har sai da afrah tace
“Qarshen term na ss 2 nima za’a karbi kudin aure na da farid,lalurar abba tasa uncle kamal yace a daga,amma abban da kansa yace a karba,babu wata damuwa,sannan hajja ma tace itama tafi nutsuwa nayi auren,naci gaba da karatun a dakina,tunda shima farid din yana da ra’ayin karatun”
“Allah sarki,Allah ya bashi lafiya kafin lokacin bikin,Allah yasa za’ayi damu,qawata kice na fara shiri tun yanzu” hararar gefanta afrah tayi,kamar maimunatun tana kusa da ita
“Nifa mun kusa raba gaari dake,muddin ba zaki tsaya kiyi abinda ya kamata ba” murmushi maimunatun tayi
“Nifa baki fahimta ba,wai ta yaya kukeso na mu’amalanci mutumin da babu soyayyata ko digo a ransa sai ta marigayiyar matarsa,sannan kuma nima din babu qaunarsa ko qanqani a rai na,hasalima ni wani kallo na daban nake masa,ko inuwa daya idan muka hada Allah Allah nake yabar wajen ko kuma ni nabar wajen,infact ma kallon mugu nake masa,tunda na ganshi yana smoking,bansan ta inda zan fara sonshi ko sakashi ya soni ba” wata qaramar dariya afrah ta saki
“Ban yarda dake ba,ban kuma yarda da dukka hujjojinki ba,kece number one a cikin mu hudu da kika fi kowa son kallon k-dramas na soyayya,har turkish drama kin koya kallo…..”
“Kin tunamin ma,akwai wani da naga talla,zanje na kalla” taka katse afran tana miqewa daga kwanciyar da tayi
“Ahaf,kyaji dashi,kici gaba da zama,zaki mamaki idan kk ga wata tayi muku wuf dashi” dariya maimunatun ta saki,idan hakan ta faru batajin tana da asara,saidai unaisa,don ta fuskanci tana da damuwa sosai a kanshi.
Agogo ta kalla sanda suka gama waya,sai taga lokaci yaja,abinda ya sanyata miqewa kawai ta shiga wanka,so take ta shirya ta fita su gaisa da baba tabawa.
Dai dai lokacin da yake shigowa sassan nasu,cikin shirin office kamar kullum,slim fit three pieces suits ne a jikinsa Dim gray color dake da ratsin butter color,kwantacciyar fatarsa dake nuna zallar hutu da gayu tayi kyau cikin shigar,jikinsa ba abinda yake sai fidda sassanyan qamshin turaren prive rose George armani dan qasan turkey,kwantacciyar sumarsa sai fidda qyalli take kamar qura baya tabata,komai nashi me kyau tsari da kuma tsafta ne.
A nutse baba tabawa dake gyara abinci saman dining hannunta kuma maqale da carbi tana ja ta waiwayo tana amsa sallamarsa
“Barka da fitowa” ta fada tana sakin murmushi,taji dadin ganinsa sosai,don ya soma wanke zato da zargin dake ranta,kadan ya motsa fuskarsa,abinda ke alamta yanayin nasa murmushi ko fara’ar kenan