GURBIN IDO

GURBIN IDO 41-45

“Barka da asuba”

“Barka kadai manya,mun tashi lafiya?”

“Alhmdlh,jiya na gaji sosai,kuma na dawo late,ban leqo ba” murmushi tayi

“Ai babu komai,ta warware ma” agogon daure a tsintsiyar hannunsa wanda yake mix da zallar ruwan gwal ya kalla

“Zan wuce office,akwai wani abu da kuke buqata?” Kai ta girgiza

“Babu komai,amma ga abinci ko zaka ci” wajen ya kalla,ya sani baba tabawa is the best cook a duk gidansu,tana cikin list din mutanen da yake iya zama hankali kwance yaci abincinsu,amma yanzun sai yakejin bazai iya zaman ba,baima saba cin abinci cikin gidan ba, infact ma bai taba ba

“Ina sauri ne,zan makara”

“Amma akwai kunun gyada irin wanda kakeso,ka daure ko cup daya kasha” ta fada tana hada masa da sauri,bayan ta saka madara da suger madaidaita,don tasan bai cika sonsu ba

“Na gode” ya fada yana karba,har cikin ransa yaji dadin hakan,yayin da baba tabawan ke karantarsa a fakaice,babu wadda ke girki a cikinsu ta bashi kenan?,abinda ya fara zuwa kanta kenan,lallai akwai aiki jazur a gidan,akwai kuma gyara.

“Tana ciki,ina tsammanin ta tashi,zan shiga ciki na watsa ruwa” tayi masa tayin shiga wajen maimunatun a fakaice,tanason haifar da kyakkyawar alaqa a tsakaninsu,tanason tayi wani aiki da anni zataji dadinsa,sannan kuma ba zata manta dashi ba. Bashi da wani sauran zabi face soma takawa a hankali zuwa dakin,tunda har ta fahimci bashi da nufin shiga,bayaso ta zargi wani abu a ranta game dashi,ya kuma tabbatar kome yayin kamar yayishi ne gaban idanun anni,tunda da ita da anni duka abu daya ne,hannunsa guda daya cikin aljihun wandon suit dinsa,daya hannun kuma cup din kunun ne yana sipping a hankali,ya masa dadi qwarai,ya kuma yi masa yadda yakeso.

Daure da babban towel ta fito daga bandakin,ta dora qarami saman kanta da yadan jiqe ya kuma bawa sumarta daman kwanciya a bayanta da gefan fuskarta,yau din sakayau take jinta,da alama lafiya tana sake samuwa a gareta,kai tsaye ta isa gaban mirror taja dressing chair ta zauna tana kallon fuskarta data yi wani irin haske ta kuma yi fresh har ita da kanta abun yana bata mamaki,kamar zaka taba ta jini ya fito,ta canza totally,irin canjin da ita da kanta yake bata mamaki.

Towel din saman kan nata ta cire ta fara goge fuskarta dashi tana maida sumartata dake son shige mata idanu baya,bayan ta miqa hannunta ta jona hand drayer amma bata kai ga kunnata ba,tana goge gashin nata tana dan rera karatun qur’ani,haddarta ta qarshe da bata baiwa ya shaik nasu ba,saboda zazzabin da ta dinga fama dashi kafin tafiyarsu hutu,ta miqe tsaye tana ture kujerar baya,ta kunna hand drayer din ta soma busar da kanta in a low heat.

Dai dai sanda ya murda qofar dakin ya kuma turo cikin cikakkiyar nutsuwa,tashin farko qamshin hair mist dinta dana hair oil da take amfani dashi wanda ya cika dakin saboda zafin hand drayer din dake kadoshi,ya kuma cakude da qamshin turarenta daya kama dakin suka buso saman fuskarsa.

Wata ajiyar zuciya ce ta qwace masa ba tare daya shirya hakan ba,bai kuma san dalilin faruwar hakan ba,ajiyar zuciyar data wuce da idanunsa suka lumshe na wasu gajerun sakanni sannan ya budesu tarwai,basu sauka ko ina ba sai santala santalan qafafunta da suma fito ta qasan towel din da take daure dashi,wanda ya tsaya mata iyaka gwiwarta,soma yawo yayi da idanunsa zuwa samanta,faffadan qugunta ya fito sosai ta cikin towel din,kallo daya zaka masa kasan daya daga cikin baiwar da Allah yayi mata ne,ci gaba yayi da kallonta zuwa sama,bayanta dake dauke da farar fata me sulbi da qyalli ya bayyana muraran,da wasu daga cikin gashin kanta da suka kwanta luf a kansa.

Cikin nauyin zuciya da kuma mutuwar jiki ya daga qafafunsa yaci gaba da shigowa dakin ba tare da maimunatu tasan an shigo ba,don zuwa sannan ta tattaro sumar tata zuwa fuskarta tana tajewa bayan ta kashe hand drayer din,tana kuma ci gaba da rera karatunta da qaramar muryarta mai zaqi da sanyi,karon farko ya sake sakin boyayyar ajiyar zuciya,qira’arta sak irin ta shaheeda,qira’ar malami guda suke bi,sai ya maida qofar ya rufe ya sake matsowa ciki sosai sannan yayi sallama idanunsa bisa kanta.

Previous page 1 2 3 4 5

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button